← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 177

Sashe 82

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

masa da kuka. "Aliyu dan Allah...." Be bari ta karasa ba ya tare numfashi ta. "No no no noooooo Emily ba abun da kike tunani ba ne, ina son na dandana mata dadin uba ne, tun da kin nuna mata na uwa, kuma kin wahala da yawa ya kamata ki huta, wani ya dauki responsibility, you're not alone we're Family" Kallonsa kawai take. "Kin min izini?" Ta daga mishi kai. "Thank You, ki yi hakuri da fadan da muka yi dazu ki yafe min" Ta yi murmushi, shi ma murmushin yayi tana tsaye yana kallonta har ta shige ciki, sannan ya koma motar ya koma gurin aikinsa. Yana shiga office abu na farko da ya fara yi shi ne kiran Ammy ya gaishe ta kuma yayi mata ya jiki domin tabbatarwa idan da gaske bata da lafiyar ko kuma fadar Turhan ne kawai. "Alhamdulillah" "Ammy me ke damunki?" "Sun ce hawan jini ne da ciwon suga, amman dai Alhamdulillah sauki yana samuwa" "Kina gida ne ko asibiti" "Ina asibiti" "Allah ya kara sauki, In Shaa Allahu zan shigo na dubaki" "Aa karka damu, ba sai ka wahalar da kanka ba ina tunanin da na kara samu sauki kadan za su sallame ni" "Allah ya kara sauki, amman dai zan shigo In Shaa Allahu" Daga haka yayi mata sallama, after like one hour, kira ya shigo wayarsa da bakuwar number sai da ya kai karshen typing din da yake sannan ya amsa wayar. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam, Aliyu kana lafiya?" "Lafiya kalau Alhamdulillah" "Baka gane mai magana ba ko? Mama Baraka ce" Ya dan yi shiru kamin ya amsa. "Maa Shaa Allahu Mama ya gida fatan kowa lafiya" "Alhamdulillah, Aliyu idan ka samu lokaci ina son mu yi magana ka kira ni, nasan yanzu kana kan aiki ne ko?" "Eh gaskiya ina gurin aiki" "Toh idan ka koma gida ko zuwa dare ne sai mu yi magana" "Lafiya dai ko?" "Lafiya amman ba kalau ba, akan matarka ne bata fada mana abun da ya hada ku ba, kai kuma baka biyo sawunta ba, ta zo mana nan duk ta rikice ta zama abar tausayi, sai dai ka samu lokaci za mu yi magana" "Okay Mama" Ya sauke wayar ya cigaba da aikinsa. Sai 4pm ya tashi aikin a hanya yayi sallah la'asar ya isa gida ya dafa ma kansa indomie ya ci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani voile lace na maza black color mai kyau, ya saka bakar hulla ya sha turare da bakaken talkama kamar wanda za shi zance, ya cika aljihunsw da sabbin kudi sannan ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanya sai gidan Emily, da ya isa unguwar be karasa gidan kai tsaye ba gudun kar ya janyo mata matsala, sai ya faka gida uku kamin nata, sannan ya kirata a waya. "Hello" "Assalamu Alaikum" Ta amsa, sai kuma ta yi shiru. "Gimbiyar tawa ta shirya ne?" "Oh oh oh Fatima?" "Yeah" "Eh ta shirya" "Toh a fito min da ita, ina waje nesa da ku sai kin saka ido sosai zaki iya ganina gida na uku kamin na ku, bana son na zo kusa ne ban san ko Vito yana ciki ba kar yace zai miki fada ko ya dake ki, kin san ni kuwa a yanzu ba zan saka ido ko yatsa wani ya nuna miki ba" Ta yi murmushi mai sauki tana jindadi tare da sauke numfashin da ya ji shi har cikin zuciyarsa. Ya zauna a motar na tsawon mintuna goma sannan ya hango ta ta fito sanye da bakar abaya ta rolling dankwalin abayar ta rufe kanta kai kace musulma ce, ta yi kwalliya sosai har da jan baki, tun daga nesa Aliyu yake kallon fuskarta tafiyarta da yadda bakar abayar ta yi mata shegen kyau ko kyaltawa baya yi gaba daya ta dauke hankalinsa ko Fatima da ya zo domin ita be gani ba sai Emily, da ta iso gurin motar sai ya sauke gilashin ya jingina da kujerar motar yana kallonta kamar wanda ya zauce. "Sannu" Ta fada ta muryar mai dadi idonta suna jan hankalinsa ga wani tsadadden murmushi a fuskarta. Yayi murmushi ya sauke kansa kasa. "Emily ashe kina da kyau, na gode da kika karramani, wannan shigar ta dace da kyau, kin yi ma abayar kyau sosai" Ta yi murmushi ita kanta ta san ta yi kyau. "Wata kila da zaki rika suturta jikinki haka da manyan kaya masu sauko miki su rufe tsiraicinki da zan yi ta kula ina fahimtar kyaunki ne, kuma zan fi sake jiki na jidadi, kin san ban taba kula da kina da kyau ba sai yanzu?" "Saboda na saka abaya?" Ya girgiza yana kallonta da murmushi. "Aa saboda kin rufe jiki, kin dace da sunan Aisha, daga yau ba zan sake kiranki da Emily ba, sai Aisha" A bakin gaskiyarsa yake fada mata tufafin yayi mata kyau domin yayi mata kyau babu karya, sai dai yana karfafa mata guiwa ne saboda ya dawo mata da sha'awar saka tufafin da musulunci ya yarda mace ta saka, so yake ta ji wannan alfarma yaja hankali da abun da yake gani da jin shi ya dace da ita. Fatima ta daga masa hannu tana masa waving domin ta lura be ganta ba, bayan kuma Emily ta fada mata ita ya zo dauka za su tafi yawo. Ku yi hakuri dan ni dan Allah Wallahi uzuri ne yake rike ni. [6/17, 9:33 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing ABOKIN RAYUWA
Chapter 82 · 0% Book details