← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 177

Sashe 22

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 EMILY POV. Tana shan ruwan tana shan ruwan tana ajiyar zuciya kai kace yar yarinya ce aka saka kuka, hannu ya kai yana shafa saman kanta har ta shanye ruwan, sai ya karbi kofin ya aje. Ba Fatima ce kawai ta saka ki a cikin damuwa ba, waya taba ki? Ita ce kawai Ya kalleta ba dan ya gamsu ba, ba zai cilasta mata ta fada masa abun da ya haifar mata da damuwa a yanzu ba, amman da sannu zai sani domin ya san yadda take sauyawa idan ta shiga damuwa. Mikewa yayi tsaye rike da cup sai ta rike hannunsa na hagu ta dago tana kallonsa da idanuwanta dake bayyana damuwa sosai. Komawa yayi ya zauna sai ta dora kanta a cinyarsa ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali, ta sani bata da sauran kima a idon kowa sai Vito a yanzu, ita din ba abar tausayin kowa bace sai mutumen da ya ganta a rana ya saka a inuwa kuma ya lullube ta da kulawa da kauna, yake gudun bacin ranta yake kaunarta fiye da kansa, tana jin kamar shi kadai ya rage mata a yanzu. Mommy ta fada min zata zo satin nan, idan ta sauka a nan na san zata rage miki kewa, ko ba komai zaki samu uwa zata kula dake kamin ta tafi, amman idan baki ra'ayi zata sauka gidana sai idan kin bukaci ganinta Ya fada yana shafa fuskarta a hankali kaunarta na kara zafafa a zuciyarsa. Bude idon ta yi ta tashi zaune tana kallon wani gafen, ta yi marmarin kasantuwa kusa da wasu iyalin, sai dai kudurin da take da shi ba zai barta ta sake kusantar iyalin Vito ba a yanzu. Ta mike tsaye ta cire ribbons din dake kanta jan gashinta ya sauko har bayanta, sai ta tsaya gaban madubi tana cire dankunenta, shi ma tsayen yayi ya matsa kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubi, baya bukatar ta bashi amsar tambayarsa, ya zauna da ita na tsawon shekara bakwai ya san me take so da wanda bata so, yana iya karantar yanayinta tun kamin ya san dalilin farinciki ko bakincikinta. Ya dafa kafadarta har lokacin kallon fuskarta yake ta madubin dake tsaye gabansu, ta dago ta kalleshi da blue eyes dinta. Zata zauna a gurina har sai kin bukaci ganinta Ba wai bana son zuwanta a nan ba ne kawai... Bata karasa ba ya juyo da ita ta fuskance sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskarta yana kallon zanen halintarta hancinta. Ina sonki Emily, ina sonki, so mai tsanani irin son da alkalin ba zai iya rubuta bawa, irin son da zan karar da kalamai gurin furtawa, ina sonki, irin son da zan iya kashe kowa a duniyar nan na rayu daga ni sai ke, zan iya rabuwa da kowa na rayu da ke, rashin zaman mahaifiyata a kusa da ke ba zai haifar da komai ba sai karin kaunarki, kar hakan ya dame ki, zata a gidana har sai idan ke da kanki kin bukaci ganinta Ya karasa yana kallon kanta, yana sonta wannan rubuce yake a cikin kaddararsa, shiyasa baya haufin nuna kaunarta a ko'ina haka kuma baya babu wanin abun da zata aikata a duniyar nan da zai saka ya nisance ta. Ya runtse ido yaja dogon numfashi ya sauke ya bude idon ya sauke su a kanta. Har yanzu baki san miye so ba, har yanzu baki fahimce waye ni ba, har yanzu baki san irin son da nake miki ba, amman ina fatan wata rana zaki san haka Hawaye ya sauko a idonta sai ya share mata da yatsanta. Zan tafi gurin London komai zai wuce Ya saketa ya matsa baya, kallonsa kawai take har ya fice sannan ta lumshe ido hawayen na cigaba da sauko mata, tana tsananin tausayin Vito fiye da yadda take tausayin kanta, ya mata fahimtar baibaine amman ta san son domin ta so mutumen da be dan darajar ta ba, son ne ya janta ga halaka har ta rasa makomarta ta butulcewar mutanen da suke rike a matsayin iya. Tana jin tsoron irin son da Vito yake mata, tana tsoron abun da zai haifar tana tsoron yadda makomarsa zata zama idan babu ita a kusa da shi. Tufafin jikinta ta cire ta daura tawul ta shiga bandaki ta kunna shower da nufin wanka sai kuma ta samu kanta da zama a cikin tube din tana nadamar shiga rayuwar Vito da ta yi... Ta dade a haka sannan ta yi wanka ta fito bata shafa komai ba ta saka short gown ta kwanta kwanta saman gadonta, korar da aka yi mata a yau ta dawo mata a rai, a take hawaye ya cika idonta, meyasa bata da sa'a a rayuwa? Meyasa farinciki yake mata nisa? A duk lokacin da ta daura damarar gina ramen farinciki sai bakinciki yayi mata kawanya, idan bata samu damar tsayawa da kafarta a yanzu ba sai yaushe zata yi? Ita kenan ba zata iya bawa kanta farinciki ba sai idan wani ne ya bata, wanin ma Vito mutunen da ya gama mata komai kuma bata da wata sakayya da zata masa, yanzu ko nan gaba. Motsin turo kofar dakin da Fatima ta yi da gudu ta shigo ya saka ta yanke tunanin da take ta tashi zaune, kamin ta yi wani yunkurin goge hawayen da suka bata mata fuska Fatima tace. Momy ki duba wannan number ki goge ta, amman karki kar duba abun da na tura gashi nan yana kira na san zai ce na goge ne kuma ban iya ba ban gane gurin ba, yace koya min amman na manta ban san ya ake gogewa ba... Kamar wanda aka ce amsa kiran mana, haka ta taba green botton din sai ga fuskar Aliyu ta bayyana. ALIYU POV. Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya gama sannan ya zauna gefen gado ya dauki wayarsa yana duba whatsapp dinsa, domin a yanzu ba shi da wani abu mai muhimmancin kamar jiran amsar Turhan, gashi kuma har yanzu Turhan be amsa masa ba bayan kuma ya karanta sakon nasa. Yaje wayar yayi ya mike tsaye ya fara shafa mai ya shirya tsab cikin shigar kanana kaya black T-shirt and White jean, yana tsaka da fesa turare Aisha ta shigo dakin, fuska ba yabo ba fallasa tana kallon bayansa har ta karasa kusa da shi. Ga abincinka can a falo fa, kai nake jira ka sauko mu ci Na ci abincin a waje Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, sakin baki ta yi tana mamakin furuncin, tasan waye mijinta cin abinci a waje ba dabi'arsa ba ce. Wai duk fushin ne haka? Fisabilillahi ganin chat kawai ya kai ace ka dauki fushi da ni har haka? Ya juyo ya kalleta. A gurinki abun da kika aikata ba laifi ba ne? Idan ma laifi ne ai ya kamata kayi min uzuri ko? Har sai idan na sake aikatawa Rashin daukarsa laifi shi yake kara bakanta min rai, taya zaki zauna da kawarki ki labarta mata yadda muke rayuwa a shimfidar da ko dan'uwanki ba a yarda ya sani ba, taya zaki ji idan kika kama ni ina fadawa abokina yadda nake da ke a gado? Dadi zan ji mana, ai kana fada masa yadda na iya gyara shimfida ne, Aliyu wannan abun fa is normal, yanzu rayuwa ta canja ba yadda muke a baya ba ne, wacan rayuwar da kake tunani ko iyayenmu ba su yi ta balle kuma mu, amman dai shikenan tun da baka so zan daina Ina fatan haka Ya furta yana kokarin danne fushinsa domin kara bata masa rai take da kalamansa na yanzu. Murmushi ya sakar mata ya matsa kusa da ita. Muje mu ci abincin Ba kace ka ci abinci a waje ba? Ta fada tana masa kallon da yafi kama da harara, ya fadada murmushinsa tare da shafa cikinta. Wasa nake kawai ina fushi ne amman yanzu na sauko Ya rike hannunta suka fice daga dakin, falo suka sauka ya ci tuwon shimkafa da favorite miyarsa miyar kuka, sai da ya ci yayi nas sannan ya soma bata labari, da hira ta yi dadi sai ya dauko mata zancen sabuwar ma'aikaciyarsu da kuma fadan da ta yi da Amal a yau. Har a ranta ta ji dadin korar da aka yi mata domin bata son kowace mace a kusa da mijinta, Amal din ma dan ta zama dole ne. Kasan wasu matan ba ba su da kai, musamman kabilun nan kara ana musu haka, ta nan za su fahimci matsayinsu, kuma wasu ma fa kawai neman maza ke kawo su Tana maganar tana yatsina fuska. Kallonta yayi yana girgiza kai. Madam ba fa ni kadai ba ne namiji a kamfanin nan, kawai ke da kin ji maganar mata sai kishi ya tashi Matan ne fa yanzu kamar za su auri namiji da karfi, idan mutum be yi taka tsantsan ba sai a aure masa miji Ke da kika san waye mijinki ai be kamata ki daga hankalinki akan ko'ina zan shiga ba, kuma karki manta ke kadai zaki rayu a gidan Aliyu daga ke sai yayanki, ko kin manta alkawarin da na yi miki? Ba ke ba kishiya Ban manta ba amman ku maza ai wani lokacin zaku iya ganin mace ku bi ku rude kanta duk wani alkawari da kuka yi ku watsar da shi, musamman idan ka ga wata fara kyakkyawa yar doguwa Yayi murmushi. Allah ya saukaka miki wannan kishin, ni bana da ra'ayin karin aure Dadi ya lullubeta ta kwanta jikinta. To yanzu zaka je ce ta dawo aikin ne ko kyaleta zata ka yi? Aa ai ta riga ta rasa kenan, ni ban san a ina take ba balle nace ta dawo, kuma an riga an yi replacing dinta da wata ai Sanin halin matarsa ya saka shi bata wannan amsar. Haka ma yafi, waya sani ma ko tana da kyau Wannan karon dariya yayi, domin ta canja daidai Emily tana da kyau kuma ya san da ta san haka ba zai zauna lafiya ba. Ai ni kowace mace na kalla ke nake gani a fuskarta Ta buge masa hanci tana dariya,
Chapter 22 · 0% Book details