Sashe 25
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ba, yana daga cikin motar yana kallonta har ta shige ciki sannan ya ciro wayarsa ya duba time, sai kuma yaja motar ya fice daga asibitin. ALIYU POV. Ya hade yawu a hankali yana mamakin yadda aka yi ta san hadisin da ta kafa masa hujja da shi, ta san addinin musulunci ne har haka? Ta yi nisa a ciki? Me yasa ma ta bar addinin tun farkon fari. Ya sake karanta sakon ta dayan bangaren yana nisa tunanin a wani bangare na labarin da ta gutsura masa, gashi kuma ta daure shi da kalamanta, be rabi Turhan a zamanin da suka yi rayuwa a Emily ne, dan haka ba zai iya shaidar kyautata ko kishiyarsa a tsakaninsu ba, amman a neman da Turhan yake mata a yanzu da kuma gudunsa da take zai iya fahimta daga rayuwarsu. Sama yayi kadan ya sake kallon hotunan da Fatima ta turo masa, Emily ta kai mace har ta wuce, and ya yaba da yadda hotunan duka basu bayyana tsiraicinta ba duk kuwa da kasancewar ba musulma ba. Ya fita daga chat dinsa da ita ya shiga na Turhan, ya sake karanta sakon da ya aiko masa a dazun. Na aureta ne a bisa cilastawar Ammy ba dan ina sonta ba, she's not my type at all, kuma adadin na ji ina sonta sai ma kiyayya ce ta ginu a tsakaninmu, har dai shedan yafi karfina na rabu da ita, amman ban cutar da ita ba Kana ta karanta dayan sakon dake biye da shi, a take jikinsa yayi sanyi zuciyarta ta karaya, ya san abokinsa yana neman Emily, and yes ya samu Emily da kuma tabbacin ita din ce, amman yana tsoron kar haifar mata da matsala, ka ya sakata a wani hali kamar yadda ta fada, ta dayan bangaren kuma yana tunanin ya zai yi da abokinsa, idan yayi shiru anya ya kyauta masa kuwa? Ya sani idan Turhan ko mahaifiyarsa suka san da Fatima ba za su bar mata ita ba. Lafiya kuwa? Aisha ta tambaya tana aje Bowl ta kunna tap ta wanke hannunta tana kallonsa irin kallon nan na jiransa. Tun da ka amsa wayar dazun na ga yanayinka gaba daya ya canja Ba komai Ko dai akan yarinyar da aka kora ne? Yayi murmushi ya dago daga jikin fridge. Ba ita ba ne Ya saka wayar aljihu ya nufeta ta rikata suka fice daga kitchen din tana masa zancen business din da take son ta fara. Watan cin kudin nawa ya tsaya kenan? Ta kyalkyale da dariya. Kasan ai kana cewa na rika sana'a Ke da baki san kowa a nan ba, taya zaki fara sana'a, kuma kin san ina binki kudi fa Namiji idan namiji ya rantawa matarsa kudi daman ai bata biya, amman shi idan ya ranta sai ya biya Saboda shi namiji be san zafin kudinsa ba ko? Ta saka dariya a tare suka zauna ta kwanta jikinsa tana taba jira kadan bachi yayi gaba da ita, a hankali ya zaro wayarsa wani abun na cizon zuciyarsa ya sake bude sakonta ya karanta a karo na biyar, abu ne da yake bayyana a gurin kowa, zuciyar kowace mace kyakkyawa ce, sai dai wanda ta bar shaidan ya rinjayeta, ko kuma wanda wasu gurbatatun mazan suka yi ma illa. Akwai tambayoyin da yake bukatar amsarsu a gurin Emily, yana son ya ji kadan daga dalilinta na hana yarta da ita kanwata zuwa ga abokinsa dake nemanta kamar zai salwantar da rayuwarsa wata kila hakan ya taimaka masa gurin karfafa rokon da ta yi masa. Sai dai kuma ba lallai ta saurare shi ba, ba lallai ta yarda ta maida shi duniyarta ta baya ba, yana bukatar ganinta face to face domin amsa masa tambayoyin da ita kadai take da amsarsu. Amman kuma? Anya zata yarda su hadu? Zata yarda ta fada masa a inda zai same ta ko ta same shi? Ya shiga contact list dinsa ya tabo William ya aika masa da sako. Please kana da wani information na gurin da Emily Aisha take zama William ya masa reply Immediately. Wace Aisha? Yarinyar da ka zo kana ta santi, wata half Cast haka mai jan gashi da blue eyes No wani abu ne ya faru? Yeah sun yi fada da Amal ne, har ta bar aikin ina bukatar ganinta face to face na bata hakuri kuma na mata bayanin yadda abubuwan suke Meyasa ka tambaye ni? Sau daya na ganta ban sake sakata a ido ba Saboda baka shigowa Office ne a yanzu, na dauka ko kuna gaisawa da juna ne, na ga ta sace maka zuciya ne Ta sace mana zuciya dai Nooo sam ba abun da kake tunani ba ne, idan ma kishi kake ka daina, ni ai musulmi ne, kuma ni bata cikin tsarin matan da nake so ma? Bata maka kyau ba Bana son macen da ta cika kyau sosai, kyaun idan yayi yawa yana zama illa, kuma ni bari da burin kara aure yanzu ko nan gaba Ya dauki William tsawon mintuna talatin kamin ya aiko masa da address din har da number gidan da take zaune. Thanks Aliyu ya rubuta masa a as reply. Me ya hada ta da Amal? Idan mun hadu zaka ji Ya amsa masa sannan ya saka wayar alijhu cikin jindadi, ya rika matarsa zuwa bedrooms dinsu bayan ya kashe komai na falon. #TeamTurhan #TeamVito A ina kuke? #KhadeejaCandy [4/20, 10:00 AM] : https://chat.whatsapp.com/Dfp3nf5JwbA22eFdvKklyG ABOKIN RAYUWA