Sashe 143
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 "Ya kamata na koma haka, ance sun dora wani ma" "Ba fa inda zaka je sai an kama yaron nan, mutumen dake neman ranka zaka koma garinsa ka zauna da sunan aiki, daman can ni bana son aikin da kake a kuda mutanen nan ba su da kyau" "Abun da Allah ya rubutawa bawa baya wuce Ummi, kuma ai yanzu guduwa yake ba zai iya komai ba" "A nan din ma kasan ko yana nan yana haka maka rame? Ba zan barka ka koma ba, idan ma suna son aiki da kai su dawo da kai Abuja ko nan Kaduna" "Idan kuma suka ki fa" "Sai ka bar aikin dole? Ina za a kusa kai da kai a kasar nan baka samu aiki ba? Ga ka da cancanta kuma ga alfarma ta ko'ina, kasan ko bangaren President muna yan gaba gaba" Aliyu yayi murmushi mai sauti. "Ummi wato dai abun da ake fada na yan siyasa da gaske ne, daga kansu sai iyalansu?" Ummi ta yi dariya. "Gurin Surukinka muka koya, kasan ya fi kowa son kai" Aliyu yayi murmushi, shi da Ummi suka juya suka kalli kofar falon da aka turo. Ammy ce ta shigo da sallama fuska ba yabo ba fallasa, Ummi ta amsa mata ita ma tana dan sham kamshi domin abu daya ne Ummi bata yarda da shi ba, shi ne raini wayo ko wulakanci, bata daukar rashin girmamawa daga gurin kowa wannan dalilin ne ya saka suke kara samun rashin jituwa da mahaifiyar Kameela. "Ammy ce a gidan ba mu?" "Ai dole za ku gan ni tun da surukata tana nan, ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, fatan na same ku lafiya" "Lafiya alau sai Alheri da ke ta shigo mana" Ammy ta yi tsaye bayan Ummi ta amsa mata. "Bismillah Ammy ki zauna" "Aa ba zama ya kawo ni ba, Aisha tana ciki?" Ummi ta yi murmushi. "Tana nan waje, idan kika fita ki zagaya dama kadan gurin Garden tana can ita da jikarki" "Ammy ina wuni" Aliyu ya gaisheta yana sirina. "Lafiya" Ta amsa tare da juya bata ko kalleshi ba. Sai da Ammy ta fice sannan Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Ammy fushi take da ni, ban jidadin yadda abubuwa suka zo ba, ko kadan Kameela bata kyauta min ba, na so na tsara abun nan cikin hikima ba tare da kowa ya ga laifin kowa ba, Allah ya sani da zuciya daya na yi wannan abun ban yi nufin cutar da Turhan ba, na shiga tsakiya ne kamin na hankara tausayin Emily ya rinjaye ni, sai na fi fifita matsalarta saboda ina ganin ita ce tafi shiga matsala, har gobe idan na tuna abun nan sai na ji zafin abun da Kameela ta aikata" "Ai ni ba karamin taimaka min ta yi ba da ta yi haka, da yanzu ban san miye yake faruwa ba sai idan ka mutu ace ai ka ci guba, ko kuma ka ta daba maka wuka, ka ga masu shegen kishin nan tun wuri ana ganin abun da suke iya aikawa daga musu kafa ake ana ganin kamar ba komai ba ne, da yanzu bata yi wannan shirmen ba ba zaka fada min ta zuba maka guba ba, kuma ai ka kasa sakinta" "A lokacin ina kokarin bata hakkinta ne, hankalin namiji baya taba zama iri daya na mace, ina daga mata kafa da uzurine amman ko a lokacin na yi alkawarin ba zan sake cin abincinta ko kwanciya daki daya da ita ba, and zuwa nan da na yi saboda ita ne Mama Baraka ta kira ni, da na zo kuma mahaifinyarta ta wulakanta, sai kuma ta aikata min abun kawai sai na zabi sauwake mata domin samawa kaina salama" "Aiko gashi yanzu abun yana cinta, babu safiyar bata aiko min sako ban hak'uri, ni kuwa ko ba ni da rai Wallahi ba zaka zauna da Kameela ba, yarinya ta yi yunkurin kasheka kiri kiri sannan ga iyayenta ba son auren suke ba, tun farko ni damam na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, domin iyayenta ba masu dattako ba ne, kai kuma ka tsaya kai da fata ai ita tana sonka tana da tarbiya, ga abun da ta haifar maka ai, daman yaushe iyaye za su bada shawara aki bi kuma a ga daidai?" Aliyu yayi dariya. "Yanzu dai ba zan sake zabar mata ba, ke zaki zabar min" "Aa kai da kanka zaka zabo, ni nawa bincika ne da duba dacewa" Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya bude firjin ya dauko ruwa ya kafa gorar a baki ya sha, sannan ya fito rike da ita ya dawo falo ya zauna. "Ni yanzu ban san ya zan yi na shirya tsakaninsu ba" Ummi ta dauke kanta daga kan wayarta ta kalleshi. "Ina ruwanka da shirya tsakaninsu? Dan iya? Tun farko daman ai bata son Turhan din, kuma sai ga shi yayi mata abin da yayi ta ji ta tsane shi, kai kasan yadda mutum yake ji idan baya son wani kuma ya zo ya kara zalintarsa? Kai da ka gode Allah auren soyayya kuka yi da Kameela, haka din ma yanzu da ta yi maka ba daidai ba yanzu ya ka ji? Ka ce ta komawa mijinta ta ga kamar kana matsa mata? Yarinya ta sha wahala yanzu har bada son wari maza ai ta ma yi kokari da take kallonka, da ni ce ko hanya ba zan sake hadawa da namiji ba, idan ta ga wanda take so har zuciyarta ita zata yi magana, kuma ni yanzu ko mijina tace tana so ai sai na tattara ni da kai mu bar mata gidan ita ma ta samu jindadin rayuwa" Aliyu ya kyalkyale da dariya. "Ummi Allah ya bar min ke, duk matar da zata yi kishi da Ummi ai sai ta shirya, taya ma Emily zata ce ta so Daddy" Ummi ma ta yi dariya. "Aa wai a misali dan na nuna maka ta cancanci farinciki, kuma kishi da ni wata wahala ce? Ni fa ba zan cutar da kai ba, kuma ba zan zuba ido ka cuce ni ba, magana kuma a fada min daya na rama da goma" "Aa ni ba tsakaninta da Turhan zan shirya ba, tsakaninta da Ammy, tsakanin Emily da Turhan wannan wani abu ne da kowa be kamata ya saka kansa ba" "Yanzu na ji maganar hankali, Allah ya bata wanda zai riketa amana mai sonta tsakani da Allah kuma babu cutarwa" "In Shaa Allahu, daman ai bayan wuya sai dadi, kuma Allah da kansa yace dukkan tsanani yana tare da sauki" Ya sake kurba ruwan ya aje ya mike tsaye ya haura sama. EMILY POV. Tun bayan tafiyar Mama Baraka Emily bata fito ba sai da Ummi ta shiga ta lallasheta, da kalamai na karfafa guiwa ta fada mata yanzu ai komai ya wuce, be kamata ta rika tuna baya ba, kamata yayi ace ta fuskanci gaba. Da lallabawar Ummi Emily ta samu gwarin guiwar cin abinci ita da Fatima ta shiga ta yi wanka ta saka doguwar rigar Atamfa, sai Ummi tace ta fita ita da Fatima waje su bawa itatuwan gardens ruwa, daga bada ruwan ne ta fara jika Fatima tana dariya, sai Fatima ta yi mata gwalo ta boya a bayan itace ita kuma tana binta ta watsa mata ruwan, sai nishadi take kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba. Tana rike da tiyo ta ji kara bude karamin gate din da aka saka a gurin sai ta juya idanuwanta suka yi arba da Ammy. Emily ta dan rage murmushin da take tana kallon Ammy har ta karaso kusa da ita, Fatima ta fito daga inda ta boya da sauri ta rumgume Ammy tana mata oyoyo. "I miss you" Ammy bata damu da tufafin a jike ba ta daga ta sama ta hade da jikinta. "i miss you too, ya kike rabin rai na" "Lafiya lau, ina Dady" "Yana can bakin gate cikin mota gidan kin fita zaki gan shi" Ta sauke ta kasa Fatima ta zura da gudu tana murna ta fita gurin. Emily ta saki Tiyon hannunta. "Ina wuni Ammy?" Ammy ta yi murmushi. "Lafiya kalau yata, ya mai gudun uwarta, kin dawo lafiya?" Emily ta yi murmushi. "Lafiya alau" "Ina kika shiga kika boya? Kin daga mana hankali, kin dagawa Turhan babu inda be shiga nemanki ba har gurin da kika zauna kamin ki haifi Fatima, ita ma Fatima bata bar mu mun huta ba" "Yanzu ai na dawo, komai ya wuce Ammy" "Haka ne sai dai a fuskanci gaba, fatan dai babu wata matsala yanzu ko?" "Babu" "Tohm Alhamdulillah haka nake son ji, yanzu hankalin Turhan zai kwanta na yarki ma ya kwanta ni ma kuma sai na samu farinciki" Emily ta yi shiru bata ce komai ba. "Jiya Turhan be yi bachi ba, gaba daya ya bi ya damu saboda ba shi ya gano inda kika shiga ba, tare da shi muka zo na ce ya jira na fara shigowa na yi magana da ke, kin san saboda Aliyu baya son shigowa gidan nan" "Ammy akwai abun da nake son na fada miki" Emily ta fada, sai Ammy ta kara matsawa kusa da ita. "Ina jinki yata" "Mu zauna a can" Suka nufi gurin da kujerun zama suke suka zauna Ammy ta dora jakarta kan teburin. "Da farko da zan fara da miki godiya, na abun da kika min ni da ana a shekarun baya, na rike ni ba tare da kin sani ko kin san inda na fito ba, na gode Sosai, hakan ya saka ni auren Turhan da nufin na rama alheri da kika min, har abubuwan da suka faru suka faru, kowace jarabawa a rayuwa darasi ce ta kan koyar da kai wani darasi ne da baka sani ba, na kara jirmama abun da kika min ne da sanin muhimmanci a yanzu da Mahaifiyata ta bayyana" "Mahaifiyarki?" Ammy ta katse ta sai Emily ta daga mata kai Idonta na cika da hawaye. Ta tsakura mata abubuwan da suka faru. Emily ta rika hannunta. "kin yi kokari da kika rika ni, kika taimaki ana, a lokacin da mutunen da ya rabo ni da inda nake samun walwala ya wulakanta ni, danginsa suka ki