Sashe 137
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
yace Momy bata nan, wani lokacin ta kan ce shi ya zo amman ba zai tafi ba, idan ta bukaci akaita gurinsa Turhan ba zai yarda ba. "Hello" "Bana fadi miki idan kin kira ki rika sallama ba?" Sai ta yi sallamar cikin kuka. "Waya taba ki?" "Momy ce, har yanzu bata zo ba? I miss her i want to see her" "Bari na kira ki FaceTime" Ya yanke wayar ya kirata FaceTime yana kallon fuskarta hawaye shabe shabe sai yayi murmushi ya rage volume din ya juya camera from font to back ya nuna mata Emily dake tsaye tana kallon gidan bata san wainar da ake toyawa ba. Wani irin tsalle Fatima ta yi ta fashe da kuka. "Hi Momy Hi Hi Hi Hi Momy Momy Momy I'm sorry" Aliyu ya juyo da front camera yana murmushi ya kara volume din. "Muna Abuja yanzu tare da Momynki, za mu dawo idan muka dawo zata zo ta ganki" "Okay..." Ta daga mishi kai tana dariya sosai tana daga mishi hannu alamar bye bye, sai duk ta ba shi tausayi, shi ma ya daga mata hannu ta kashe wayar ya kira sunan Emily. "Emily" Ta juyo sai ta kalli motar daya bude ta fara takawa ta nufi motar ta shiga tana ta kallon kofa wai ko Dr A-B zai fito ko Momy sai dai rashin jindadin tafiyarta ya hana Dr A-B fitowa because he don't want to say good bye to her, Momy kuma tana jin kanta ba kasafai take saukowa kasa ba, ba kuma dan wulakanci ba domin bata da wulakanci ko kadan sai dan isa ta naira. Ta shiga ta zauna Aliyu ya rufe motar Mama Barakat ta bude dayan gefen ta shiga ta zauna Aliyu ya shiga front seat sai da suka fice daga gidan sannan Aliyu ya tambaya ko dai su tsaya su kwana Abuja domin to him Abuja gida ce no need to rush, Ummi ma a nan take zauna ba dan abun da ya faru ba da yanzu bata je Kaduna ba. "Aa mu tafi kawai" Mama Barakat ta fada, a nan Emily ta kalleta. "Da gaske ke kika haife ni?" Mama Barakat ta kalleta jiki a sanyeye. "Ni ce?" "Taya? Meyasa kika jefar da ni? Me na yi?" "Baki yi komai ba, na haife kyakkyawa cikin koshin lafiya, na aje ki a inda na bar ki ne saboda na haife ki ba da aure ba, kuma baki yi kala da ni ba, ina jin tsoron irin kallon da duniya zata min a wacan lokaci ne" "Amman kin san ina gurin kuma a gurin na rayu? Kin taba tunanin nemana? Ko sanin halin da nake ciki?" Mama Barakat ta girgiza kai. "Ban taba ba, saboda ina tunanin kamar abun da na aikata shi ne mafita a gareki da ni, ban taba sha'awar na san wane kike ciki ko rayuwa kike yi ba, tun da na aje ki na rufe shafinki, ban sake ganinki ba sai wacan ranar da kika labarta min labarinki, dana kalleki kuma sai na ga siffarki da yanayinki be sauya ba daga na mahaifinki, kuma sai kika gudu saboda neman mafita, sai n aji tsoron nemanki saboda yarana da aurena da kuma ke taya zan fuskance ki?" Emily ta yi juyar da kanta ta jinginar jikin mota tana hawaye, hawayen da ba su tsaya mata ba har suka shiga jirgi. A guri daya suka zauna da Mama Barakat a first class, Aliyu kuma ya zauna wani guri dabam ba kusa da su ba. TURHAN POV "Momy zata dawo na ganta" Turhan yayi mata murmushin zahiri badini kuma wata wuce ta ce take cin ransa. "Wow zata dawo I'm happy, to yanzu sai kije ki ci abinci kar Momy ta ga kin rame ko?" Ammy ta fada, Fatima ta daga kai har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Idan ta dawo zata zauna a nan? Zamu zauna tare? Bana son wani ya sake tafiya kuma" Ammy ta daga mata kai, sai ta dawo da gudu ta rumgume Turhan. "Ina son haka" Ta fada da hausa domin zamanta gidan ta fara tsintar wasu kalamai na hausa, Ammy ta kan gwada mata magana da hausa ta koya mata wasu abubuwa, idan kuma ta ji ana hira aka fadi wani abu sai ta tambaya me aka ce ko me ake nufi har rubutawa take idan yan kwaran suna bisa kai, idan kuma rigimar neman Momy ya tashi bata kula kowa. Sai da ta fita dakin sannan Ammy ta kalli Turhan ta ce. "Abuja Ummi take zaune, amman a yanzu ance tana gidanta na Kaduna yanzu kuma Aliyu yace suna Abuja za su dawo Kaduna yau, jikina sai yake ba ni kamar aje yarinyar nan suka yi a can na tsawon lokacin nan" "Ni ma jikina ya ba ni haka, wata kila kuma daman ya san inda take ko da shi ya boye ta ba, ko kuma ya nemota ne, tun da ya fi ni sanin mutane a Kasar nan, yanzu kuma ita sai ta yu tunanin ko ban yi kokarin nemanta ba ne, Aliyu be kyauta min ba, na rasa gane me na yi masa, babu yadda za'ayi ta fahimce ni" Ya dafe kanta kansa idonsa na cika da kwalla damuwa ta matsa tsaye a rai. "Ban san dalilin Aliyu na yi min haka ba, amman ni ba zan iya yi ma Aliyu abun da yayi min ba, abota bata ce haka ba, aminci be cancani wannan sakamako ba" Ammy ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna ta dafa kafadarsa. "Haka butulci yake da ciwo, amman ka yi hakuri kuma ka yi addu'a idan kuma ta nuna bata son kasancewa da kai, dan Allah ka saka musu ido, mutum be taba cin amana ya ga daidai ba a rayuwarsa" "Ko ba zata dawo gareni ba, na aminta amman kar ta auri Aliyu, gayen nan ya gama da rayuwata, kuma idan ya sameta hakan ya nuna ya ci ribar abun da ya aikata kenan" "Idan bera da sata daddawa ma tana da wari ai, idan da can kamin ka bayyana a rayuwarta tana kula Aliyu a yanzu be kamata Aisha ta yi haka ba ko dan yarinyar nan, matukar tana da hankali da tunani yadda dai ka dawo mata ka nuna mata kau na be kamata ka saurari kowa ba sai kai, ita uwa koda yaushe tana son abun da danta yake so ne ko dan farincikinsa" "Ammy Aisha bata da laifi, Aliyun nan dai shi ne shege, ita ai daman fansa take son dauka shi ne be dace yayi min haka ba, Ammy ko dai naje na taro ta?" "Ai baka san yaushe zata sauka ba, kuma karamin aikin yarinyar nan ne ta disgaka a gaban mutane, kuma kasan har Aliyu yana gurin sai ya ji dadi ai" Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Turhan idan Aisha ta zabi Aliyu ko wani ba kai ba, ka yi hakuri dan Allah ka bi a hankali, kai fa namiji ne kuma kai ka fara wulakanta ta, na san ka yi nadama amman ka kara da hakuri idan ka yi hakuri ita kanta zata dawo maka, ko kuma ja ga Allah ya musanya maka da wanda ta fita alheri, ko kuma Allah ya baka zuri'a da matar da kake aure yanzu, tun da ba cewa aka yi ba zaka haihu ko kuma ita ba zata haihu ba" Ya mike tsaye cikin rashin jindadin maganar. Ammy ta bishi da kallon tausayi har ya fice, saukowa yayi kasa ya nufi dan karamin dinning din daya siyawa yarsa take zama ta ci abinci ya durkusa a gurin ya dauki spoon din da take cin abinci ya cigaba da bata abincin tana ci data gama ya bata ruwa ta sha sannan ya rumgumeta. "Fatima ina sonki, kuma ina son mahaifiyarki Allah shi ne shaidata, yanzu ku ne farincikina" Ta yi murmushi domin ta san ina sonki da hausa Ammy ta koya mata. "Daddy ina sonki" Ta yi kwance jikinsa tana jindadi ga babanta kusa kuma ga mamanta zata dawo. [8/1, 6:32 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t ABOKIN RAYUWA