Sashe 109
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutum ya kanki abu kuma ya zama shi ne alheri a gurinsa, ko kuma ya so abu ya zama abun sheri ne a gurinsa, a yanzu ya fahimci hakan domin gashi tsananin rabo ya saka ya samu haihuwa da matar da ya tsana yake ganin kamar bata dace da shi ba, ashe uwarsa ta iya zabe kuma ta hango masa abin da shi be hango ba be fahimta ba, kibar ma ashe da ta samu kulawa mai kyau jikinta zai canja ne yayi kyau ita ma ta yi kyau kamar yadda take yanzu, wato sai a yanzu ya fahimci ba karamin aika aika yayi ba, gaba daya ya rasa ta ina zai kama zaren lamarin ma balle ya dinke. Hango waya a kunnenta ya saka shi maida hankali sosai gurin kallonta na son fahimtar abun da yake faruwa, bata ji ma da sauke wayar ba ya hango Ummi ta iso gurin da take zaune sai Emily ta mike tsaye Ummi ta yi mata magana sannan ta rumgumeta, can kuma ta kama hannunta suka shiga cikin asibitin. A nan ne kansa ya kara daurewa zuciyarsa ta hararo masa ko danta din nan ne ba shi da lafiya Aliyu ya turo Ummi ta taimaka mata? Waya sani ko Aliyun ma yana ciki? Amman kuma Ummi ai ba anan take ba Abuja take zama. Motarsa ya koma yana ta tunanin me ya faru me zai faru, be san a inda zai samu labarin komai ba sai da Kameela ta fado masa a rai sai dai kuma ba shi da Number ta. Ya kira Ammy ya bukaci ta kira layin Kameela ta bincika masa abun da yake faruwa, sai Ammy ta fada mata da number Kameela kuma ta labarta masa Aliyu yana asibiti, ta gane hakan ne a lokacin data kunna wayarsa dake hannun Fatima saboda Fatima nata yi mata kuka sai aka yi ta kira ana tambayar abun da sauki. "Ina tunanin ko dai ya samu hatsari ko kuma wani abun ne ya faru da shi" Turhan ya sauke wayar a kunnensa yana wani kashe ido. "Kam uban nan, wato Aliyu take yi ma kukan nan? Lallai ko a cikin munafukai wutarka ta dabam ce Aliyu, har ya aka yi irin wannan shakuwar da ita? " Ta ji kamar ya tafi ya bi bayanta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ya yi ma motarsa key ya dauki hanyar gidan Ammynsa, sai da ya kusa isa ya ji kamar ba zai iya barin abun ya wuce ba yayi reverse ya juya sai kuma wata zuciyar ta tuna masa shi da yake neman mafita a yanzu ai be kamata yayi rigima ma be kamata yayi abun da zai saka Emily ta tsane shi ba, ya sake reverse ya juyo sai kuma zafin abun ya doki zuciyarsa taya wai zata zauna tana kuka hehehe akan wani katon banza munafiki? Alhalin tana matarsa? Da ama ace Aliyun yayi masa abun arziki da sauki ko shi ya bata aurensa ai kukan da take yayi yawa balle kuma yanzu a duk duniya ba shi da makiya kamar Aliyu. Ya juya ya sake daukar hanyar asibitin sai kuma ya sake juyowa haka zuciya ta yi ta juya shi kamin yayi nasara cin galaba akanta ya kawo kansa gida gurin Ammy, ya shigo cikin falon ya zauna takaici ya hana shi magana. Ammy ta dube shi daman ta fahimci damuwa tun a dazun da suka yi waya. "Me ya faru? Ko yunwa kake ji ne? Ko dai minene ka saita kanka be kamata Fatima ta kanka a cikin wannan yanayin ba" Ya kalli Ammy sai a lokacin ya tuna da wani zancen abinci daman rabonsa da abinci tun wanda ya ci a jirgi. "Wato Aliyu munafiki ne Ammy, Wallahi ban tana tsammanin haka daga gareshi ba, wai kin ga yadda yarinyar nan take kuka? Ashe duk shi take yi ma kuka kamar wani ubanta? Shiyasa aka ce makiyinka yana tare da kai Allah kadai ya san abun da ya shuka mata? Shi ko kunya baya ji ma? Ai na yi zaton ko mutuwa na yi Aliyu ba zai min haka ba, har da Ummi ta zo ta rumgume ta yadda kika san wani shirin film wata kila gidansa ko gidan Ummi take zaune, haka yake ta kallonta yana rayuwa da ita kuma ya san ina nemanta, ya boye min komai, ba wai ina kishi ba ne, sam amman dai ni ko dolo ne ai dole na nuna takaici ko?" Yana maganar yana jin abun da be saba ba, daman babu wanda ya kai balarabe mugun kishi na bala'i, Balaraben mutum da muryar matarsa be son aji, ko da yake shi a yanzu ba kishi ba ne haushin Aliyun ne yake ji na abun da yayi masa. "Zaka iya kwantar da hankalinka ka yi min bayani? Ni duk ban gane wannan kewaye kewayen ba" Ammy ta tambaya yana kallonsa domin bata fahimci inda ya dosa ba, sai ya mike tsaye yana huci. "Idan ma na yi kishi ai ina da hujja ko dan Fatima? Emily ko mutuwa ta yi dole na kare martabarta saboda wannan yarinyar, ai ba zan jidadi ace uwar yata ce take wannan shigar ba? Har tana hulda da abokina, lallai Aliyu ya hadiye kashin da zai zame masa masifa a wuya, ba fita ba wucewa, kuma har abada ni da shi Wallahi Tallahi babu wani uzuri, abun da yayi min ya fi ka dauki wuka ka chakawa mutum" Ya koma ya zauna yana cizon hakora. ALIYU POV. Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi sosai kamar ba na shi ba, kuma yayi matsa tsami, amman karfin hali irin na namiji da juriya yana hada ido da mahaifiyarsa sai ya saka matar murmushi. Yayi yunkurin bude baki yayi mata magana sai ya ji bakin yayi masa nauyi kansa kuma ya fara ciwo daman shi ma kan na shi yayi masa nauyi. Ummi ta yi ma wata yar'uwarta magana ta fita ta kira likita ya shigo da sauri ya duba shi ya cire masa ruwan dake jikinsa ya taimaka masa ya tashi zaune aka kawo roba ya wanka bakinsa Ummi ta hada masa tea ya sha aka ba shi magani ya sha. Ummi na kusa da shi zaune sai matsar kwalla take tana kallonsa. "Ummi da sauki fa kina gani to kuka na me kuma?" Cikin kuka Ummi ta ce. "Allah kadai ya san zafin da kake ji amman ba zaka nuna ba dan kar na damu, kalli yadda suka maka rauni a kafa, jiki ko'ina duka" "Saukin abun ma babu karaya, amman ko suwa gaskiya kashe ka suka so yi" "Ni ban san ko suwaye ba, ni dai ina tsaye ina waya da Ummi kawai na ji duka ta ko'ina da itace da hannu, Allah yasa inda na tsaya kusa da mutane ne kuma ana hada hadar shiga Sallah Magariba domin an yi kira ne lokacin sai mutane suka hankalta da wuri suka kawo dauki, mutanen suka gudu, na ji dai ana ta Innalillahi ni ma kuma ina ta tun da suka hau ni da dukan, a nan jama'a suka taimaka aka dauke ni aka dora ni a babur din wani aka yo asibiti da ni, suka ce ba za su karba ba, saboda kaina da kafata suna zubar da jini lokacin ga hannayenta sun duka bana ma iya daga su, to daga nan dai hankalina ya bace ban san ya aka yi ba sai yanzu da na farko nan" Ummi ta ce. "Muna wayar nan da kai na ji kana ambaton innalillahi sai ina jin karar duka na san ba lafiya ba, ko dai ita yarinyar ko kuma Kameela tun da su ma ba hankali da su ba ko kuma shi Turhan din cikinsu akwai wanda ya saka aka yi maka haka, kiran yankewa yayi na fito na shiga bangaren Daddynka na fada mishi da ya gwada kira sai ta shiga, Allah yasa yana gida a lokacin shi yayi magana da su ya fadi asibitin da za a kaika kuma ya kira CP ya sanar masa maka, yanzu haka kofar nan police ne awaje ba abarin kowa ya shigo, sun ce sai ka farka za su shigo su dauki bayanai" "Ummi ya aka yi kika zo?" "A dare nan ban iya kwana a Abuja ba ai, mota muka biyo da rakiyar jami'an soji sha biyu na dare na sauka garin nan, kowaye ya maka wannan abun ba zai tsira ba In Shaa Allahu" "Allah y sauwake, idan kun dan gana sai a bar shi ya samu hutawa saboda ya ji ciwo a kai yawan magana zai iya haifar masa da matsala" Likitan ya fada sannan ya fice. "Emilyn ma tun dazun take kira ta zo nan ba su barta ta shigo ba" Aliyu ya kalli Ummi. "Taya aka yi ta sani?" "Ban sani ba, amman dazun wayar tana hannun mubarak ya fada min ta kira ya fada mata kana asibiti" Ummi na rufe baki sai ga kiran Emily ya shigowa a wayar Aliyu dake hannun Ummi. "Gata nan ta sake kira" "Ummi abarta ta shigo mana" "Kana ta ciwo wa yake ta wani Emily? Waya sani ko ita ta saka aka yi maka haka saboda yarinyarta" "Ba zata yi haka ba Wallahi na san ranta ya bace amman ba zata saka yi min haka ba, ita ma fa tana cikin matsala, dan Allah Ummi ki barta ta shigo kuma dan Allah Ummi karki nuna mata wani abu ko da ta zo dan ta yi fada da ni ne, Wallahi ta fi ni gaskiya kuma ni ne ban kyauta mata ba, sannan kuma yarinyar ancutar da ita an kuntata mata har tana kallon musulmai a matsayin azzalumai, tana son musulunci na fada miki kafira ce ta musulunta wahala ya saka ta koma ruwa, wannan abun nake son na kankare a ranta kuma na dawo da ita tafarki na kwarai, labarin da na baki jiya ko rabi ban fada miki ba na wahalar da sha a rayuwa, ni kadai ne mutumen da ta yarda da shi, dan Allah karki nuna mata wani abu, idan muka kyautata hali da kuma zamantakewa da ita har ta fahimci musulmai mutanen kirki ne kuma ta dawo addinin ai mun yi jihadi babba ba karami ba" "Ya isa haka, likita yace karka