Sashe 160
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sauri ta saka hannayensa ta rufe fuskarta. Hannayen dake fuskarta ya sumbanta ya goga fuskarsa yana dariya sannan ya saketa ya fice dakin ya rufe mata kofa yana jin kamar kar ya tafi ya barta. TURHAN POV. A lokacin da ya fito daga falon na Daddy waje ya tsaya jikin motar da suka zo, ya ji duniyar kamar tana juya masa, ko da wasa be yi tsammanin Emily zata juya masa baya har haba ba, kuma a gaban iyayensa. Dadin dadawa kuma ta furta sunan wanda take kaunar a gabansa cikin kunnensa. Miya yayi ma Aliyu? Ita ce tambayar data fara zuwa masa a rai. Miyasa ya dauki bata masa ta wannan hanyar? Wace irin kiyayya Emily take masa har haka? Be samu amsoshin tambayayinsa ba Sarkin ya fito, kamin ya shiga motarsa Alhaji Bulama ya fito tare da Mahaifin Kameela, shi dai ya san ya shiga mota, yadda aka yi suka kama hanya har suka isa gidansu Ammy shi ne abun da be san yadda aka yi ba. Ya zauna cikin falon yana sauraren yadda Alhaji Bulama yake labarta mata abubuwan da suka faru, yana jin mahaifinsa yana magana da ita amman be fahimce me suke magana kai ba, a yau ne karo na farko da yaren larabci ya subuce masa a kai. "Aliyu... Aliyu... Aliyu..." Furucin Emily nata dawo masa, be san yaushe aka mahaifinsa ya fita ya dai ji Alhaji Bulama ya dafa shi yana fadar maganar da be gane ba, yana zaune a falon kowa ya fice be san an yi ba sai da Ammy ta girgiza shi. "Turhan nan?" "Ammy me na yi ma Aliyu? Ina ta kokarin tariyo rayuwarmu ta baya zaman da muka yi, me na masa? Ashe ko ba ni da rai bancanci yayi min hallaci ba?" Ammy dake tsaye ta zauna idonta cike da kwalla. "Ka yi hakuri Turhan, ba a taba cin amana aka yi nasara ba, muna nan da kai hakki zai bayyana" "Miyasa ita ma ba zata fahimce ni ba? Ko. Kalaman ne nawa ba su kai ba? Wallahi ina sonta ina kaunarta Ammy, kuma ba zan sake cutar da ita ba, Wallahi na yi alkawari ba zata sake zubar da hawaye akaina ba" Hawaye ya sauko ma Ammy, ko wace uwa bata son ganin danta cikin damuwa balle kuma Ammy da Turhan kadai take da shi, bata tana ganin tsananin damuwa a tsare da shi data gusar masa da hankali ba irin yau. "Tashi ka tafi ka yi sallah" Be haura sama ba sai ya fice falon a masallacin yayi alwala yayi sallah, suna fitowa masallacin mahaifinsa ya kira shi akan ya shirya, jirginsu zai tashi karfe 5pm, daga shi sai DR A-B ake jira saboda Dr A-B yace ba zai bar garin ba sai an daura auren Emily da Aliyu kuma karfe 4:30pm za a daura. A nan ya ji wani labari da yafi furta sunan Aliyu azaba a zuciyarsa. Daker ya iya kawo kansa falon Ammy. Yana shigowa ya nufi agogon dakin ya tsaya yana kallo yadda dakika take juyawa ta zama minti. Jikinsa yayi ma kafafuwansa nauyi yana ta lilo jiri na dibansa kamar zai fadi. Yana ta kallon agogon da second din ke dis da bugawar zuciyarsa yana jin wani dubu na haye masa kai. Har agogon ya nuna karfe 4:30pm. Turhan ya rufe ido, Ammy dake tsaye bayansa tana kallonsa ta karaso ta rike anta tana jansa baya a hankali har ya zauna kan kujerar dinning. "Ammy a yau na san rashi, na san miye kiyayya, na kuma san miye soyayya, da na sani eya, tsanar da Aisha take min ta kai har ta auri abokina ta bar ni? Shin ita bata tafiya ne? Ammy ina son yarinyar nan miyasa kika cilasta na sake ta? Ammy ma rasa Aisha, uwar ata na rasa ta, cikon farincikina na rasa shi a yau....!" Hawaye ne masu zafi suke sauko masa, ko Ammy sai da tsoro da tausayin anta suka kamata, domin bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na gasawa da rudani irin wannan ba. " Dady?" Ya ji muryar yarsa da sai a yanzu ta filo daga dakinta ta sauko kasa duk abun da ake bata sani ba. Turhan ya saka hannayensa biyu ya dafe kansa baya son yarsa ta ga hawayensa. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi. "I miss you... Dady ka dawo? Ina Momy kace tare za ku zo ba?" "Momy ki ta zabi Aliyu Fatima, ta barki ke da Dady, Momy ki ta auri Aliyu bata auri Dady ki ba, tace Aliyu take so ba Dady ki ba" Ammy ta fada mata tana hawayen tausayin danta gaba daya ta rikice. Cikin tsoro Fatima ta bude hannayen Turhan babu hawaye a fuskarsa amman suna kwance a cikin idonsa, sai kawai ta fashe da kuka sosai ta rumgume. Ya dauke ta ta dora saman jikinsa ya hade duk wani abu da yake ji ya fara rarrashinta. Wayarsa ta yi kara alamar shigowa sako, ya ciro wayar ya duba Dr A-B ne ya aiko masa da sako cewar za su tafi shi ya tsaya sai next week, ya aje wayar ya kalli mahaifiyarsa sai ya sakar mata murmushin karfin hali. [8/25, 8:41 PM] ABOKIN RAYUWA