← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 177

Sashe 40

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 *June 4 2014* *Lagos State Nigeria.* *Little Saints Orphanage (ABULE EGBA HOUSE) 149, Carpentar B/stop, Ekoro Road.* *MAFARI...* Tafiya na ke a hankali ina kallon sababin talkamin da suke kafata wadanda wata kungiyar taimakon kai da kai ta kawo mana tun satin daya gabata. Talkamin sun min kyau sosai a kafa kamar daman dan ni akai su. "Emily.." Ina jin muryar mai kiran na juyo fuskata ba yabo ba fallasa na kalleta. "Ibo lo lo?" Ta tambayi gurin da zanje da yaren da mafi yawan marayun da suke zaune a wannan gidan na marayu suka fi ji, wato yarbanci. "Mo n l si ja lati ni aw n eso di . kilo de ti o bere?" "Ohunkohun. irin ajo ailewu" "O dara emi yoo pada wa ni tit Na karasa amsa mata tare ta mikawa mai gadin gate din gaisuwa "E kaaro arabinrin" Sai ya amsa min da murmushi. "O dara, run yoo bukun fun "Amen" Da kansa ya bude min gate din duk kuwa da kasancesarsa dattijo, amman yana ganin girma da kuma mutunci. Wani dogon numfashi na ja na sauke sakamakon iska mai dadi da take kadawa, daga kaina nai sama ina kallon hadarin da ke haduwa a tsararin samaniya rana tana ta lumshi tana budewa gwanin sha'awa. Babu mutane sosai daman unguwar ekero road, kamar gra take abu ne mai wahala ka ci karo da hayaniya ko kaikawo na jama'a kamar cikin tsakiyar lagos. Mini skirt ne a jikina mai aljihu sai wata farar vest mai kama da ta kwana wuyana na sanye da sarkar cross hannuna ma yana rataye da warwaron wanda akai da farin dutse. Kitso ne jan gashin dake kaina, na yi parking dinsa da ribbon tsorayen sun sauko har bayana. Tafiya nake cikin natsuwa da aminci, zuciyata kuma nata rara min wakar da muke a coci duk da kasancewar bana jin natsuwa da da wakar amman sabo yasa ni yake jin dadinta. Sai da na fito daga unguwar gaba daya na nufi hanyar da zata sadani da wata karamar kasuwa da take layin. A bakin titi na tsaya sai da motocin suka gama wucewa sannan na tsallaka zuwa gaban teburin wani mai siyar da kayan marmari. Na tarar da mutum biyu a gurin so hakan na nufin dole nai hakuri na jira har ya sallamesu. Da yaren igbo suka yi magana dayan ya siyar masa da abaya da kankana dayan kuma mai zubin hausawa sai ya mika masa dubu biya yace ya hada masa kayan marmarin da turanci. Na saba siyayya gurinsa magidanci ne mai jin yaren igbo domin shi baya jin turanci balle kuma yarbanci, rike kudin da mutumen ya mika masa dan be san abunda zai bashi ba, shi ko kyakkyawan saurayin mai kama da mazan novel ya dage sai bayani yake masa da turanci. "Kaji matsalar rashin jin yaren mutane" Ya fada cike da jin haushi. "Kuma ba zaka nemi taimakon kowa ba?" Da mamaki ya kalleni jin na masa hausa. "What did you just said?" Murmushi nai ban bashi amsa ba, na kalli mai siyardar kayan marmarin na fada masa cewar ya hada masa na dubu daya da dari biyar kamar yadda ya fada masa da yalshen turanci da farko ni kuma na fada masa da yaren da yake ji wato yaren igbo. "Nye ya puku akwukwo nri" Sai ya amsa da okay ya shiga hada masa. Mutumen ya matsa kusa da ni. "Kina jin yarena?" "Duk mutumen daya zauna lagos dole ne yaji yare kala biyu, ko dai ya iya turanci ko kuma yarbanci, har da igbo ma idan ta kama, domin shi wannan mutumen baya jin yarbacin igbo yake ji, ya kamata ka koya" Na fada masa ba tare dana kalli inda yake tsaye ba. Murmushin kasaita ne ya bayyana a fuskarsa da alama na burgeshi jin ina hausa kamar jakin kano. "Amman ina kika koyi yare nan har hudu turanci, hausa, yarbancin, igbo wace yare ce ke?" Kallonsa nai muna hada sai yayi saurin kawar da nasa, ba mamaki blue eyes dina ne suka firgita shi. "Ban san yarena ba" "Why?" "Because ni marainiya ce" Fuskar tausayi yai ya zuba hannayensa a aljihu. "Ayyah I'm sorry" "You shouldn't, it's not your fault" "Yeah i know, mi zaki siya a nan" "Ayaba ina son ayaba" "Owk you look cute" Ya fada yana kallona. "Thanks handsome" Na fada still ban kalleshi ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro dubu uku ya mika min. "Gashi ki siya" "No na gode" Na fada ba tare da na kalli kudin ba. "Wow ba kasafai zaka bawa yarinya kamarki a lagos kudi ba ta ki karba" "Likewise, ba kowa zai iya kyautar kudi a take ba a Lagos sai bahaushe" "Yeah musulumci ya koyar da mu rika kyauta saboda halin Annabin mu ne, by the way sunana Hamza Ali ana kirana Khaleefa" Cike da burgewa na ke kallonsa, ban san abunda yasa na ke son naji ana maganar abunda ya shafi musulumci ba Hannu na mika masa "Ni kuma sunana Emily Emmanuel" Kin karbar hannun yai. "Mu musulmai bama gaisawa da mace musulumci ya hana mu sorry" "Never mind" Sai da mutumen ya mika masa ledar kayan marmarin sai ya karba yana kallon. "Fada masa ya rike canjin" Da yaren Igbo na fada masa cewar ya ce ya bar canjin, sai ya mikawa mutumen dubu ukun. "Ki fada masa abunda kike so ya hada miki, nice to meet you young lady" Ya fada yana kallona kasa da sama, kamin ya buga babur dinsa ya daga min hannu yana murmushi ya wuce. Murmushi nai na rashin dalili na bishi da kallo har na daina hangoshi. *** *** *** Godiya mutumen igbo yai min sannan na fada masa abunda zai bani ya hada min da sauran canjina na kamo hanya cike da farincikin da ban san dalilinsa ba, kawai dai ina jin nishadi ya cika min zuciya da ruhi. Ina tafe ina wasa da dayan hannuna mai nade da sarkar cross sai aka fara yayyafi, kowa ya fara gudu an fakewa a wani gurin domin ruwan ya sauka da karfi, ni kam tafiyata na ke da dai daya ina daga kaina sama ruwan yana saukarka min a fuska da kai. Hango bakin shagon wani mutume dake road din mu babu kowa a gurin yasa naje gurin a guje na aje ledar hannuna na fito tsakiyar titi da babu motoci na tsaya ina waka da ruwan saman ina juyawa ina rawata domin babu abunda ya dame ni. Shakaf ka jike a guri a gurin idan na hango mota tafe sai na koma gurin shagon a guje na fake dugun kar a min daukar mahaukaciya sai motar ta wuce sannan na fito na cigaba haka nai ta yi har aka gama ruwan a kaina. Sannan naje na zauna bakin teburin mutumen na saka hannuna a aljihu na ciro yar karamar wukar da babu wanda yasan ina yawo da ita na dauki lemu daya na yanka na sha. Sai da naji na koshi da kayan marmarin sannan na faki idon mutane na maida wukar ajihuna, na dauki ragowar kayan marmarin na kamo hanyar gidan marayu wanda zan iya kiransa da gidanmu ko kuma na ce gidana. Kamar dai dazun yanzu ma sai da muka gaisa da mai gadin gurin har yake min sannu da jikewar da yai sannan na wuce sashenmu wato block C. Rossy na ganina ta rugo da gudu ta tare ni, daman ta saba min haka ita ba ma ita kadai ba har da sauran an block din, domin ni mutuniyar kowa ce komai nawa na kowa ne, idan na samu bana iya ci nidai ko da basu san da shi ba. "Ku aab pada. arabinrin mi" Ta min sannu da zuwa da yaren yarbancin tana kokarin karbar ledar hannuna. Sakar mata ledar nai ina murmushi na ce. "Kije ku raba tare da du Elina" "Wow wato oga shakur yayi miki sallama ta kwarai kenan nan yau" Da yaren yarbancin muka yi maganar ni dai murmushi kawai nai na kama hanyar dakinmu, daman na san kowa zai dauka cewar kyautar oga Abdulshakur ce, domin ya saba min irin wannan sallamar idan rana tai hi kyau. Oga Abdulshakur wani oganane a gurin aikin gyara mota, shi yake da gurin a gurinsa nake zuwa ina koya duk kuwa da kasancewarsa musulmi, na fara aikin ne a lokacin dana kare makarantan kuma ban samu damar shiga babba ba, an rubuta takarda zuwa ga gabnatin Lagos domin daukar nauyin karatun mu zuwa mataki na gaba mu yan wannan shakarar da muka gama, amman har yanzu babu wani abu da ya fito daga can, wata kila dan aikin har yanzu be kai ba, ko kuma ta manta da sha'aninmu ne. Ni kuma bana son zaman banza ba aiki, bayan kuma shugaban gidan marayu ya bawa kowa damar mai son aiki ko sana'a yayi domin tallafawa kansa. Ko da na shiga dakinmu babu kowa sai Nine ackor ita kadai a gafenta tana bachi, dakinmu babban daki ne mai daukar mutum takwas kamar sauran dakunan, an kawata dakin da kananan gadaje na kwanan mutum daya da yar karamar waduruf ta saka tufafi. Gadona kusa da window yake hakan kuma na min dadi duk kuwa da kasancewar wani lokacin ina jin tsoro. Tufafin jikina na fara cirewa na canja zuwa wata yar karamar gown, sannan na dauki wukata na saka a cikin jakata inda na saba ajeta, gado na hau na kwanta fuskata da murmushi mutum dazun ne har yanzu na kasa daina ganinsa a idona, yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi fari ni kuma ina son fararen mutune duk kuwa da kasancewata fara. 'Musulmi ne fa!' Zuciyata ta fada min, miyasa zan yi tunanin musulmi bayan a coci ana yawan fada mana cewar musulmi yan ta'adda ne kuma basa son kistoti irina, a take gabana ya fadi sai na ji kamar nayi wani sabo, take nai saurin praising Jesus na roki gafarsa, nai saurin tasowa na baro dakin gudun kar tunanin ya sake dawo min na samu zunubi. Haka muka raya yammacin ranar da laraba tare da yan'uwana marayu, sai da dare yai sai na nufi gurin dana saba zama na zauna karkashin wata bushiyar lemu na jingina jikina
Chapter 40 · 0% Book details