Sashe 76
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3 Ya duba agogon hannunsa. "Wani kake jira ne?" Ta tambaya tana jin sakewa da shi kamar yadda ta ji a farkon haduwarsa. Sai yayi murmushi "Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban sani ba ko abubuwa za su canja wata rana na zo ina jiranki" "Miyasa baka jira?" "Wani mataki ne Allah ya kaini, bana jira sai dai a jira ni saboda kullum na tashi aiko aiki har sai na ture idan ina son hutu, saboda haka ya zama mutane sai dai su jira idan na gama wani aikin sai na fara na su" "Toh amman me yasa kake duba agogo" Ya wara ido. "Hmmmmm ashe dai ke ma kin iya sa'ido" Ta rufe idon tana murmushi, likitan dake tare da shi yayi murmushi ya mike tsaye ya fice daga office din. "Ya kamata ki saka min number wayarki, saboda mu rika gaisawa ko? Domin na lura kin fini tsada shiyasa da na baki number wayana baki kira ni ba" Yana maganar yana kallonta har ta bude ido. "Gashi ko sunanki ban sani ba" "Emily, sometimes akan ce min Aisha" "Ehhhh nice name, Allah yasa baki kyamar musulmi" "Kai baka kyamar Cristian?" Ya girgiza kai. "No... Ko kadan Mahaifiyata ahlul-kitab ce ita christen ce kin ga ba ni da hujjar kyamar ki" Ta nuna shi "amman kai..." "Aa ni Musulmi ne mahaifina Musulmi ne, aljanar data aure ni ma ta hana ni aure musulma ce" Emily ta kyalkyale da dariya... "Interesting" Ya fada yana kallonta da murmushinsa mai kyau. "Wa yace aljana ta aureka?" "Haka suke cewa wai saboda kullum cewa nake na ban ga wanda ta yi min ba, amman ina tunanin ta fara gajiya da ni ta kusa sakina" Ta sake kyalkyalewa da dariya. "you're so funny" "Yeah my second job is to make you laugh" Tana kokarin saka hannunta ta rufe bakin daga dariyar da take, Dr da ya fita dazun ya kwankwaso ya turo kofar ya shigo Aliyu na bayansa. A lokacin ne Dr A-B ya mike tsaye "Bakonka ya zo a late jirgina ya kusa tashi" "Hakuri zaka yi Dr ka saurare shi kuma ka ba mu lokaci ba sai mun yi ta daku ba" Cewar Likitan dake tare da Aliyu, Dr A-B ya girgiza kai zai yi magana Emily ta kalli Aliyu da tun da ya shigo ita yake kallo tace. "Da dai ka saurare shi, ba zan jidadi ba idan ka tafi baka ji uzurinsa ba" "Emily ai ba zan ce miki aa ba" Ya koma ya zauna sannan ya nunawa Aliyu kujera. "Malam Bismillahi" Aliyu be zauna ba domin baya son yayi maganar cewar yana son a duba matarsa ne a gaban Emily and the way da ya samu Dr A-B jikinsa ya ba shi kamar ba za su jitu ba saboda alama sun nuna masa Dr A-B is arrogant. "No ka ba mu katinka kawai i will contact you though it" Dr A-B ya dan tabe baki kadan. "Okay Dr Osman zai baka Katina" Ya mike tsaye yana kallon Emily da murmushi a fuskarsa, ita ma ta mike tsaye. "Toh yanzu kuma sai yaushe?" "Sai randa kaddara ta yi nufin sake hada mu sai mu hadu mu gaisa" "Ehmmm hmmm idan kaddara ta sake hada mu, toh na san manufar hakan kuma zan baki mamaki, fatan alheri" Ya risina mata kadan sannan ya wuce ya bude kofar ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice Dr Osman yayi masa rakiya. Sai da suka fice sannan ya maida idonta kan Aliyu sai ya gwatsaleta. "Ashe haka kike da arha?" Ya fada fuska ba yabo ba fallasa. A take ta hade rai ta turo baki. "To miye na min magana ba mun yi fada ba" "Na miki magana zo ki saka wuka ki yanka ni" Ta sauke idonta kasa. "Breakfast kika kawo masa ne?" "Na Tasmia ne" Ta amsa da dan fushi. "Toh ki dauki abincin ki fice ko gadin office din ya barki ki yi?" "Toh ka daina min fada kamar wani ni yarka ce" "I'm your boss tarbiyarki a yanzu karkashina take dole na gyara miki zama" Ta duka ta dauki abincin ta nufi kofa ta bude ta fita sai gashi ya fito. "Tasmia da kika yi sanadin aka yi mata duka yanzu zaki dauki abinci ki kai mata babu ko kunya?" A nan ta zaburo masa ta juyo a tsawace tace. "Ni ban aikawa Matarka sakon komai ba, babu dalilin da zai saka na yi maka karya, babu dalilin da zai saka na turawa matarka wannan sakon, kai ma idan kana neman janye kanka daga jikina ba sai ka yi min shari ba, you can walkway ba tare da ka dasa min bakin ciki ba, ba sai ka zarge ni da abun da ban aikata ba" Ta karasa maganar idonta na cika da hawaye, kallonta kawai yake har hawayen suka zubo mata ta saka hannu ta share. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya kama chat din da Kameela ta aika masa daidai gurin da number wayar Emily ta fito ya nuna mata. "To wa aika? Vito?" Emily ta karbi wayar ta duba ganin Number wayarta ya matukar bata mamaki. "Wallahi ban aika ba, ban tura mata wannan sakon ba, kuma Vito baya daukar wayata..." "Toh waya aika?" Ya tambaye sannan ya karbe wayarsa. Ta yi shiru tana nazari babu wanda ta fado mata a rai sai Chidimma da Tasmia domin Chidimma ta taba daukar wayarta, Tasmia kuma ta karbi wayarta a jiya tace zata kira ta sanar da iyayenta, sai dai bata saka ran Tasmia zata shirya mata wannan Chidimma kuma bata iya hausa kamar haka ba, a ina ma number Kameela ta fito bayan ta yi blocking dinta. "Waya karbi wayarki jiya?" "Tasmia tace zata kira iyayenta bayan Kameela ta mata duka, amman Tasmia ba zata yi hakan ba" "Karfe nawa kika je gida?" Ta yi shiru tana nazari "Karfe tara tayi bayan mun gama waya da kai ne" Ya duba time din sakon sai ya ga da safen nan aka turo masa shi, ya duba kiran da Tasmia ta masa jiya sai ya kalli Emily. "Karki yarda na riga ki isa Office" "Kamar ya kuma? Yaushe na kai mata abun karyawa har na koma gida na shirya na tafi office" "Wannan matsalarki ce kamin ki zo nan ya kamata ki yi wannan tunanin ba yanzu ba" Ta kalleshi tana mamakin yadda yake kokarin tsanarta. "Why do you hate me now?" "I didn't hate you" "Zan aje mata abincin sai na tafi" Ya daga mata kafadunsa alamar he don't care. Da sauri ta yi gaba da abinci ya bi bayanta har ta shiga dakin da Tasmia take, tana zaune kan gadon tana waya Emily ta shigo, shigowar Aliyu ya saka ta yanke wayar tana yana jin wani yanayi da dabam tare da mamakin ganinsa a lokaci daya. Emily ba zata iya fadar zata je gurin aiki ba saboda kar Tasmia ta ji kamar ta fifita aikinta akan lafiyarta dan haka tace. "Ga abinci nan ki karya, zan tafi yanzu ina da uzuri" Ta kalli Aliyu sannna ta fice Tasmia na mata godiya murya kasa kasa. "Ina kwana" Tasmia ta fada bayan Emily ta fice ta bar Aliyu. Madadin ya amsa mata sai yace. "Do you plan all this?" Ta sake dubansa kamar da can ba kallonsa take ba. "Ban fahimta ba" "Kin fahimta Tasmia, don't deny it, Emily tace ba ita ta aika sakon nan ba" "Kuma ka yarda da ita?" percent" Ta nuna kanta gabanta na faduwa sosai. "To miyasa ni ka zarge ni? Me zai saka na aikata hakan? Yaushe ma na dauki wayar Emily?" Ya saka hannayensa duka biyu aljihunsa. "Ban sani ba tukuna, abun da na sani a yanzu shi ne Emily ta yarda dake, ban sani ba ko ta fada miki labarinta, ta sha wahala sosai kamin ta hadu da mu, ta hadu sa musulmai masu gurbatattaccen tunani da son zuciya sun bar mata tabon da take kallon kowane musulmi ma haka yake, sai dai haduwata da ita da kuma ke ya fara sauya tunaninta, toh be kamata ta same mu da wani nakasu ba, ko da musulma ce be kamata mu ci amanar junanmu ba, kuma mu watsar da yardar mutanen da suka minta da mu" Yana kaiwa nan be tsaya jiran abun da zata fada ba ya fice ba tare da ya bata hakurin zubar hawayen da take ba. Sai da ya fice sannan ta share hawayenta. "Shi namiji na gari nemansa ake ba sai ya kawo kansa ba, yadda Kameela tana walawa a gidanka tana watayawa abun so ne a gurin kowace mace, ko da ace baka da kyakkyawar sura kulawarce kawai, dole zata burge duk wata mace mai son auren namiji irinka, ballantaba kuma ka hada duka biyun ko uku ma, ga kyau ga kudi ga bada rayuwa irin wanda mace take so, ku kanku maza wata rana ba kusan wanda ya dace da ku ba, Aliyu kana bukatar mace mai hankali mai wayo ba irin Kameela ba" Ta sauka daga kan gadon "Kowa da kalar kaddararsa wata kila ni tawa a haka ta zo, son mijin kawata ko ba komai matarka ta kira ni da marar tarbiya kuma ta yi min gorin aure, toh sai na nuna mata rashin tarbiyan, kuma sai na koya mata darasin da ace kewa mace bata yi ma yar'uwarta mace gori" Ta zauna a kujera ta bude abinci. "Sai kace ni na fi kowa bakin jini daga fara plan har ya gano ni, wai ni haka rayuwata zata kare ne? Kalar mazan da nake son aure basa zuwa su ce suna so na sai yan wadanda basa cikin tsarina kamar ni na fi kowa bakin jini, gaskiya ba zan bari Aliyu ya subuce min ba, daman tun ganin da na yi masa da farko ya burge ni" Tana cin abincin tana magana da kanta kamar wata tabbabiya. KAMEELA POV. "Ai dama ya samu shiyasa kuma kin ji hausawa sun ce kowa ya ga rana yayi shanya, da bata karya farashinta ba tun farko ta zubar da kimarta Wallahi Aliyu ko marin uwarsa kike