← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 177

Sashe 12

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani abu amman bata samu ba sai da ta bar unguwar gaba daya ta shiga wata karamar unguwa dake kusa da su, sannan ta fara ganin masu siyar da abubuwa wasu ma yanzu suke fitowa domin goma ta dan gota. Abubuwan da ta fada su ta siya mota ta biya da Atm din sannan ta sake juyowa tana takowa a kafa, tun tana tafiyar tana jurewa har ta fara gajiya ranta ya fara baci, tana daf da isa kamfanin ta ji an yi mata magana da shigar da Vito ne kadai yake mata haka. My Beautiful Babe Ta kalli gefen da titi yake sai a lokacin ta lura da motar dake binta, yadda fuskarsa take hade kai kace ba shi ne yayi mata furucin mai dadin sauraro ba, dan murmushi ta yi ta tsaya har ta bude motar ya fito, tana mamakin ganinsa. Ko da yake ba abun mamaki ba ne domin ya san kamfanin take aiki kuma kamfanin ba boyayyen kamfani ba ne. Waya aike ki siyen abu? Ta kalli robobin dake hannunta da bubble tea. Uhmm... Ta yi shiru kamar mai tunanin abun da zata fada. Ba ki sha Bubble tea na sani, kuma na shirya miki breakfast kamin ki fito, so don't lie to me My Boss Ya gyara tsayuwarsa yana jin ba dadi. Are you a maid hare? A aike ki ki siyo abinci shi ne aikin nan Babe? No ita kadai ce ta aike ni, saboda a karkashinta nake aiki, kuma ta zo bata karya ba Ya kalli kayan dake hannunta da kyau sannan ya sake kallon fuskarta. Ba ki rasa komai a gida ba, ban san miyasa kika zabi wannan rayuwar ba A kokarinta na kawar da zancen ta ce. Me ya kawo ka nan? Ya sauke numfashi a hankali ya matsa kusa da ita sosai. Na zo ne na yi miki bankwana zan tafi Lagos yanzu, akwai kayana da aka rike dole sai na tafi za a sake su Drugs...? Ta tambaya kai tsaye, be amsa mata ba sai kawai ya kai middle finger dinsa yana shafa soft kuncinta na dama up and down, idanuwanta cikin nasa ita tana jira amsar tambayarta shi kuma kaunarta kawai ke kara zafafa daga idonta zuwa nasa idon then straight to his heart. Dauke yatsansa yayi ganin tana kokarin kawar da fuskarta ya juyo ba tare da yace da ita komai ba ya bude bakar motarsa mai bakin gilashi ya shiga ya ja ya barta tsaye a gurinta yana kallon sawunsa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta karasa cikin kamfani, a nan ma sai da ranta ya kara baci saboda tafiya ce mai tsayi daga gate din zuwa cikin kamfanin, haka dai ta daure saboda tana son aikin, daman hausawa sun ce daukarwa ya fi bauta ciwo. ALIYU POV. Yana daura necktie dinsa ta aje masa littafi a gaban madubin da yake shiryawa ta zauna gefen gado tana kallonsa. Kallon littafin yayi sannan ya kalleta List din yaudara za a fara min? So kike duk sai kin karar da abun da na tara kin maida ni talaka ko? Ta saka dariya tana kai apple din dake hannunta a baki. Aa Wallahi kasan jiya ka yi min alkawari, to ni dai ban gamsu ba so nake ka rubuta, domin a doka ya fi ka'ida Ya zauna kusa da ita yana murmushi mai sauti. Rantsuwa fa na yi miki jiya baki yarda ba? Na yarda amman dai kara ayi a rubuce ko da ka manta na rika tuna maka, ni fa a rayuwata babu abun da na tsana irin kishiya, ni bana sonta ko kadan, ko wata macen ka kalla a tv bakinciki nake ji, kuma mata a yanzu sun yi yawa da kansu ma suke kawowa mazan mutane hari, idan na mutu dai sai ka yi aure amman idan ina raye ban yarda ka yi aure gaskiya Ya girgiza kai, ya dauki littafin yayi rubutu a kai. Ni Aliyu Mudallab na yi alkawari ba zan yi ma Matata Aisha kishiya ba, har abada zata zauna ita kadai a gidana sai yayanta Yana rubutawa yana fadar alkawarin har ya gama yayi saka hannu, ba tare da tunanin komai ba, domin har ga Allah ba shi da ra'ayin kara aure. Hakan yayi miki? Ta daga mishi kai tana murmushi sonsa na karuwa a ranta. Bakinta ya sumbanta kadan sannan ya mike tsaye Sarkin kishi, anya zaki bar ni a aljanna na more hurul'aini kuwa? Wallahi ba zan bari ba Ta fada da karfinta, kyalkyalewa yayi da dariya sosai ya dauki abubuwansa ya fice tana masa addu'a tare da rakiya har kofar falo. Sai da yayi addu'ar fita daga gida sannan ya fice ya shiga motarsa yana dago mata hannu da blowing mata kiss sannan ya fice. Karatun Qur'ane ya kunna a motar kamar yadda ya saba, domin baya sauraren waka idan ma yana son rage kadaice ne sai dai ya saurari karatun ko ya karanta ko ya rera kirar da kansa. Kamar kullum baya shigowa sai 11am ko fiye da hakan ma, idan yayi sakammako shi ne zai shigo 10am, kasancewar CEO na kamfanin, sai dai kuma baya barin kamfanin sai 3pm ko 4 sometimes har 5pm ya kan kai idan aiki yayi yawa, ko wani Meeting. Ya faka motarsa a gurin da aka tanadar masa sannan ya bude motar ya fito, iPod dinsa ya saka a kunne ya cigaba da sauraren karatun Qur'ane a kunnensa na hagu, ta ko'ina ya wuce gaishe shi ake har nufi elevator, matar dake cikin yake kallon irin kallon nan da ya kasa kyabta ido ma balle ya dauki, kallonta yake da kyau yana tantancewa, tunaninsa kuma yana tafiya wani gefen. Yana shiga ciki sai ya taba 5, a take Emily ta taba 4 ba tare da ta kalleshi ba. Ni na fara zuwa Be ce mata komai ba bayan karkatowa da yayi ya kalleta ya kalli ID din dake kirjinsa, ita kuma sai ta yi zaton kirjin nata yake kallo, hakan ya saka ta kokarin gyara rigarta da maballi sama yake bude ya bayyana wani bangare na kirjinta sai dai be fito da dukiyar fulaninta ba. A kokarinta na yin hakan Bubble tea din dake hannunta ya fadi ya zube. Bakinciki ya saka bata san lokacin da ta fara yi masa ihu ba. Kallo har na bala'i har na masifa, ka kura min ido har na zubar da abun da na yi wahalar tafiya can wata unguwa nesa na siyo Nan din ma dai be jin magana ta zame masa dole dan haka ya adana kalamansa ya kalli gurin da ya bace kawai ya dauke kansa, his mind is somewhere else shi dai jin yake kamar ya taba ganinta, and he won't lie tana da masifar kyau, ta ko'ina ta kai mace, shiyasa William ya rikice jiya yana ta masa santinta. Suna isa four floor ta Elevator ya bude sai ta fita suna hada ido ta watsa masa masa wani kallo na jin haushi wanda ya fi kama da harara. Ya dauke idonsa da sauri ta har Elevator ya rufe, number 5 ya taba, ya ciro wayarsa ya kira Turhan. Hello Aleeyou Turhan ya fada da dan sautin labarancinsa kadan. Turhan, yarinyar nan da kake nema fara ce sosai? Eh fara ce, tana da jan gashi, da blue eyes and tana kiba Kibar da Turhan ya fada ya saka Aliyu kwankwanto, domin ita dai wannan da ya hadu da ita daga jiya zuwa yau siririya ce. Tana da masifa? No bata da fada ko kadan, tana da tsoro idan ma aka mata fada sai dai ta yi kuka ba zata iya maida magana ba Okay, sunanta Aisha ko? Eh bata da wani suna bayan wannan? Ba zata rasa ba, amman na manta sai na bincika Ammy ko zata fada min Ta yi dogon boko ne? No bana jin ma ta gama Secondary School, ba wai na san komai ne akanta ba, amman dai zan bincika, me ya faru? Aliyu ya amsa masa yana ficewa daga Elevator. No na tambaya ne kawai saboda na taya ka nema Na gode sosai Aleeyou, yau zan tafi Lagos din In Shaa Allahu, ka taya ni addu'ar Allah yasa na dace, ga matsalar masarautarmu, ga matsalar Matata ga matsalar neman yarinyar nan Karka damu komai zai wuce, ita haihuwa ai lokaci ne, ita kuma za a same ta In Sha Allahu Ina fatan haka Okay bye Allah bada sa'a Ya sauke wayar yayinda yake tura office din farko ya shiga. Good Morning Sir Morning Nick. Please inform Michael to notify our new staff members that buying food during working hours within the company premises is not allowed. They can only do so either before work begins or after closing hours, as it seems they are not familiar with our rules. Also, remind them to sign in when they arrive and sign out when they leave Okay Sir Ya amsa yana dan sirinawa alamar girmamawa, sai da Aliyu ya shiga office dinsa sannan Nick ya zauna ya fara cika umarnin boss dinsa da System kamar yadda aka saba, duk wani abu da za'ayi a cikin kamfanin sai dai a tura ta email, sai idan uzuri ne ko kuma wani abu ne da ya shafi mutum personally sannan ake amfani da Telphone din da aka tanadar a kowane Office. _______ Allah yasa Aliyu ya cika alkawarin da ya dauka, domin maza sai Allah. Anya idan Vito ya san kudurin Emily na guje duk wani abu nasa zai barta kuwa? Kuna ganin Emily zata iya jure aiki a karkashin Amal kuwa? Shin Turhan zai yi nasara idan ya tafi Lagos neman Aisha? [4/20, 9:58 AM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 12 · 0% Book details