← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 177

Sashe 124

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 5 Kwantawa ta yi a kasa har gashin ta chudanya da kasa ta lumshe ido kanta na mata nauyi yana juyawa har lokacin bata iya fadin mafarki take ko akasin haka, can ciki kamar daga nesa take jin muryar Dr AB yana magana a wayar data saki ta fadi kasa har ta tsaga. Kamar jira ake ta rufe idon sai wani bachi mai nauyi yayi gaba da ita duk maganar da Dr AB yake a wayar bata amsa ba bata ma sake sanin yana yi ba, shi kuma baya son ya katse kiran be san ko idan ya kira zai samu ta shiga ba kar ya yanke wannan kiran kuma ya zama be sake jinta ba, dan haka ya cigaba da maganar yana fatan wani ya dauki wayar ya amsa masa ko kuma ita da kanta ta amsa. Da ya ga abun ba na yi ba ne sai ya yanke kiran ya sake kiranta shigow ar da kiransa yayi a wayarta tare da ringing ya saka Emily ta farka da mugun karfi, idonta ta fara budewa taja numfashi da karfi sai kuma ta yi hanzarin saka hannunta ta tare rana dake hasken fuskarta, ta tashi zaune ta dauki wayar ta duba. Sunan Dr AB ne a jikin screen din wayar data fashe, a take abubuwan da suka faru suka dawo mata, sai ta fahimci ba mafarki take ba kenan duk abun da take gani da ji a dazun matsayin mafarki ba mafarki ba ne zahiri ne. Ranar yau ta kama ta zame mata ranar farinciki amman abun da yarta ta aikata da kuma maganar da ta ji ta rushe duk wannan. Kiran ya katse ya sake kiranta a nan bata daga ba, sai ta mike tsaye ta kama hanya ta cigaba da tafiya, a yanzu kuma ina zata je? Wani guduwar zata sake yi? Haka rayuwa zata kare mata a tsuguno da guduwa, naman gurin zama da mutane? Ta shiga wata kwarkwada tada hango sai ta bulla ta wata hanyar har lokacin Dr AB kiranta yake amman ta ki ta daga. Guri ta samu ta zauna ta cire dankwalin data daure gashinta da shi ta aje gurin ta jingina tana jin ringing din wayarta da ya zame mata kamar wata wakar da zata taimaka mata gurin tausayawa kanta. Wayar ta sake kara wannan karon bakuwar number ce, sai dai ta san ba zata wuce Dr AB yake kira dan ya ji daga gareta ba, ta amsa kiran da nufin fada masa bata bukatar taimakonsa a yanzu, sai ta ji muryar Ummi tana magana cikin rawar murya da hanzari irin na wanda ya zaku ya ji daga wani da aka rasa. "Emily? Kina ina? Direba yace kin dawo amman baki shigo ba kin fita ina kika je? Ga kuma takardar mun gani Turhan ya sake ki ko?" "Eeh ya sake ni" "Kina ina kin daga mana hankali?" Ta kalli gurin da take zaune. "Ummi na shigo na tarar kuna wani zance kuma na ji, matar da na bari a gidanki muryarta na ji kamar tana ikiraran ita ce Mahaifiyata ko kuma ta san inda mahaifiyata take dan Allah ki fada min da gaske ne?" Ummi ta yi shiru ta rasa ta ina zata fara, can kuma sai ta nisa. "Yanzu dai kina ina? Idan wani abu kike son ji ko sani ai gida ya kamata ki taho, ba wai ki tafi wani gurin ba, kin daga mana hankali, ke da ya kamata ki yi farinciki Turhan ya sake ki?" "Dan Allah Ummi ki amsa min, abun da na ji gaskiya ne?" Ummi ta dauke wayar daga kunnenta ta mikawa Mama Barakat. 'Tana son sani idan ke ce mahaifiyarta ko akasin haka, ban san amsar da zan bata ba" Mama Barakat ta karbi wayar ta kara a kunne. "Hello... Emi... Eim...emi...emilllllyyy lyyyyy" Ta amsa murya can kasa. "Na'am" Sai kuma ta yi shiru. "Kina ina dan ki dawo" "Da gaske ke ce mahaifiyata?" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Ni na haife ki da cikina... Ni ce uwarki... Mahaifiya..." Emily ta yi murmushi mai hade da hawaye da kuka. "Waya raba ni da ke? Miyasa ban tashi tare da ke ba? Taya zan yarda ke kika haife ni ma?" "Ba magana ce da za'ayi ta ta waya ba, magana ce da ya kamata ace ina kusa da ke kina kusa da ni" "Ki amsa min dan Allah, tsawon rayuwata na karar da ita ne akan nema da son sanin su waye iyayena su waye dangina, dan Allah ki fada min waya raba ni da kowa? Ko kuma dai kina nufin kin san inda iyayena suke?" Mama Barakat ta fashe da wani irin kuka. "Ni ce...." Emily taja numfashi, tana mamakin wace irin uwa ce zata raba yarta da kowa. "Bari na canka, saboda kin haife ni ba ta hanyar aure ba ne ko?....." Mama Barakat ta fashe da sabon kuka mai karfi ta kasa amsawa na tsawon lokaci. "Dan Allah ki yafe min Emily ki zo mu yi magana ki fahimce ni, zan fada miki komai" Emily ta dauke numfashi na wucin gadi, a take duk wani farinciki da ta taba sani ya rushe, ko ba ta amsa mata da eh lallai ba ta hanyar aure ta haife ta, ta fahimci amsar domin shirun da tayi kamin ta amsa da kuma kukan da ya kwace mata sun tabbatar da hakan gashi kuma tana neman gafararta. "Sanin wannan amsar da dade ina tambaya, ya fi duk wani furuci da halin kunci da na taba shiga a rayuwata" Ta katse kiran ta share hawayenta, sauran da suka rage a ramen idonta suka kafe a nan take, kukan ya yanke zuciyarta ta kafe, ashe akwai ranar da bakinciki zai ninku hawaye su tsaya. Wayarta ta sake ruri wannan karon data duba sai ta ga number Aliyu ta daga jiran ta kara a kunne. "Assalamu Alaikum" Ta yi shiru. "Emily" "Aliyu... Ka gafarce ni dan Allah, na shiga rayuwar ka na rusa farinciki da amincin dake tsakaninka da matarka, na yi sanadin kwanciyarka Asibiti" "Me kuma ya kawo wannan maganar? Ni na kira ne saboda Ummi ta fada min kin tafi gidansu Turhan kuma har yanzu baki dawo ba ta ce na turo mata number ki tana son ta ji ko lafiya, Emily me yasa kika tafi? Already mun yi magana da Daddy kuma ya fada min yayi magana da mahafin Turhan komai zai zo karshe cikin lokaci, amman ban so kika tafi gidan ba" "Ba amfani Aliyu... Turhan ya riga ya sake ni, ranar da ya kamata ta zama ta farinciki a gareni wata mata daga dangin Kameela mai ikirarin ita Mahaifiyata ce da kuma yata sun rusa duk wannan, Fatima ta zabi ubanta ta ce ta tsane ni Turhan take so, a yau kuma na gane da wacece ni, tambayar da na dade ina yi a yau na samu amsarta, na gano inda tabarbarewar rayuwar ta samo asali ba ni da sa'a tun gurin haihuwa shiyasa kowa yake taka ni yake guduna, indai har uwa zata haifi ya kuma ta jefar da ita saboda gudun jin kunyar duniya ko shiga wani hali, ta zabi farinciki akan na yarta, ta fifita mutumcin akan na yarta, toh taya kake tunanin wani zai ga yar nan akan hanya kuma ya bata farinciki? Ashe har da uwar data haife ni bata bukata ta" "Ban fahimci me kike magana kai ba Emily amman dai ko minene ni ina da bukatarki, kuma ke ma kina bukatar kanki, karki damu da abunda Fatima ta yi daman na hango from miles away, ita ai yarinya ce wacce ta dade tana mafarkin samun uba, kowa yace zai tsaya a matsayin ubanta karba zata yi balle kuma ta hadu da ubanta na gaskiya, shiyasa data tambaya ni ban musa mata ba, sai na fada mata kin yi zaton baya raye ne shiyasa kika fada mata cewar bata da uba, idan kuma kin hadu da wata tace ita mahaifiyarki ce baki san uzurinta ba" "Wane irin uzuri ne zai saka uwa ta jefar da yarta? Shin bata yi tunanin ya rayuwa zata kasance min ba bayan babu ita babu kowa a kusa da ni? Shim bata damu ta san a wane hannu na fada ba? Saboda ta haife ni bata aure ba ni miye laifina ne? Miyasa bata yi tunani ba kamin ta aikata?, na girma cikin tsangwama da rashin daidai da abokin tafiyarsa, da kowane faruwa tambayar kaina nake ina iyayena suke? Ta san bata bukatata miyasa ta haifo ni? Ashe uwa zata iya jefar da yarta ko danta saboda jin kunyar duniya?" "Ita ta fada miki bata hanyar aure ta haife ki ba Emily ko kuma dai baki saurareta ba na fa san halinki, dan Allah karki jefa kanki a wata matsala, ki daina tunanin babu mai bukatarki ni ina da bukatarki ina son farincikinki" "Ni da kai kamar mafitar rana ne da mafadarta, dukanmu muna fuskantar mabanbanta hanyiyi ne. Baka bukatata a rayuwarka Aliyu, indai har mahaifiyata zata ji cewar ni illa ce a rayuwarta, yar da raina da azaba da damuwa ta zabi mahaifinta sama da ni to babu mai bukatata a rayuwarsa. Ni dai yau gaji na yi yaki har karfina ya kare, na yi iya yadda zan iya na kasa cin ma muraduna, an rusa rayuwata da farinciki tun ina karamata, a yau na haka rame na binne burina zan bar wannan shafi famko ba tare da digon tawada ko zanen alkalami ba, na ga rayuwa rayuwa ta gan ni, na wahala iya wahala daga karshe kuma na hadu da bakin labari, ni dai na fahimce wacece ni yau, tambayar dake yawan yi ma kaina na samu amsarta a yau. Na yi ta kokarin ganin kaiwa ga hasken farin wata, da na isa kusa da shi, sai kuma na fahimci daga nesa ya fi kyaun kallo, duk yakin da nake na samun kwanciyar hankali ne" "Kar idonki ya rufe ki aikata abun da za ki sake dawowa kina nadama, ni dai bana nufin komai a gareki sai alheri, ina son na same miki wani tsanin hawa ne a duk lokacin da kasar da kike taku ta yi miki zafi, ina son na zama wata igiya da zaki rika ki cimma burikanki, na so na zama kamar
Chapter 124 · 0% Book details