← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 177

Sashe 37

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

san ni ya san halina kuma ya san suwaye iyayena ba zai taba yarda ya karya alkawarin da ya daukar min ba, domin ya san yadda zan hana shi zaman lafiya" Anty Shafa ta tabe baki ta kabbatar sallah, Farida kuma ta yi dan tsaki. Har abada dai Wallahi bana son Aliyu bana son iyayensa, domin shi ne silar bakincikin mahaifinmu" "Sai ki kashe shi idan baki son shi" Kameela na rufe baki aka turo kofar dakin, Mama Barakat ce ta shigo dakin da far'arta. Maa Shaa Allah, Kameela jiki yayi kyau" Kameela ta wani hade rai ta juyar da fuska kamar ba ita ake yi ma maganar ba. Farida ta amsa. Eh jiki yayi kyau sosai Mama Barakat" "Sannu Kameela ashe kuma dan be zo da rai Allah ya baki lafiya ya bada na aikawa yace shi din kuma mai ceto ne" "Ameen" Ta amsa daker kamar an mata dole. "Ayi ma Aliyu gaisuwa" "In shaa Allahu zai ji Mama Barakat an gode" Farida ce kawai take amsa mata Kameela kam ko gafen da da take bata kalla ba kai kace ba ita ta shigo ta yi ma sannu ba, Mama Barakat na fita Kameela ta ja tsaki. "Ni ban san abun da Abbah ya gani a jikin matar ba ya aurota, gashi nan ta zo ta tsika mana zuri'a da yarbawa, sai bakin munafurci da iyayi, Wallahi na tsaneta kamar mutuwa" "Saboda me? Farida ta tambaya. Kameela ta watsa mata harara. Ke har sai an fada miki? Wake son kishiya sai kin yi aure zaki gane kan gari, duk wani abu mai alaka da kishi ko kishiya ni bana ciki, gashi nan ta zo ta tsirka mana da nata jinin a gida" Anty Shafa da ta sallame sallah ta jefa nata baki. "Ai ba laifinta ba ne Wallahi laifin Abbah ne duk matan duniyar nan ya rasa wa zai aura sai bayarabiya" "Wallahi na rantse da nice Hajiyarmu ba zan yarda mijina ya kara aure ba, bayan duk wahalar da aka Sha an samu kudi yanzu sai kawai ya karo aure, tab ai sai dai a mutu" Kameela ta fada. Farida ta kallesu da mamaki. "Yanzu fa ana maganar shekara goma sha biyar da auren nan, toh miye amfanin yin maganar yanzu, tun da har yara ta haifa da ai sai hakuri" "Ke dalla gafara can baki san ma duniya ba" Anty shafa ta karasa tare da jan taja tsaki ta fice daga dakin. EMILY POV. Bata farka ba sai karfe biyu da rabi na rana wani wanka ta sake yi ta yi kwalliya cikin wata shigar ta kananan kaya ta canjan sarkar cross din dake wuyanta zuwa dabam wanda ita ta siya da kanta ba wanda Vito ya siya mata ba, even though da kudinsa ta siya but not t like wanda ya bata da hannunsa, jakarta ta nufa ya dauko agogon mutumen nan ta saka a hannunta sai dai yayi mata yawa yana zubo mata a hannu. Ta zabi haka ne domin ta shiryawa amsawa Vito ko wace kalar tambaya da zai mata a duk lokacin da yayi arba da sarkar wuyanta ko kuma agogon mutumen da baya fatan ta hadu da shi yanzu ko nan gaba. Ta saka turare sosai sannan ta fito daga dakinta tana sanye da fararen flat shoes. Babu karya duk wanda ya kalleta zai san ta yi kyau domin red dress din yayi mata kyau ya karbi farin fatarta, ga gashinta data sako a gaba ta kulle sauran a bayan kanta. Chidimma ma da take mace kallonta take ta ko'ina Emily ta hadu kuma ta kai mace, wata kila shiyasa Vito yake sonta baya sauraren ko wace mata sai ita, sam baya kallon yaranta data haifa ma da kuma yadda yarta take yarfashi a gaban kowa, haka ma yake ta wahala da danta marar lafiya amman ita ma bata gani, idan ba shi ba wake wannan wahalar yanzu... "Are you okay" Emily ta tambaye ganin yadda take kallonta har ta sauko bata san ta iso kusa da ita. Da sauri Chidimma ta sauke kai kasa jikinta ya dan yi rawa. Ina tunani ne" "Kina cikin wata matsala ne?" "Aa babu komai Ma'am karki damu" Emily ta daga kafadunta ta duba agogon da yayi mata yawo. "Yanzu na san Fatima tana kusan da dawowa, idan zata je makaranta islamiya fine idan kuma ba zata je ba, kar a barta taje ko'ina, zan fita maybe sai dare zan dawo, ki shafa min kan London kuma ki fada masa ina kaunarsa" "Tohm ranki ya dade" Ta amsa Emily ta kalli dinning ta dauke idonta ta nufi kofar fita falon ta fice. Gudun abun da zai je ya dawo ya hanata fita da motarta sai ta zabi tafiya a kafa, haka ta bi shagunan da ta gani dazun da safe ta gabatar musu da kanta ta kuma tallata kanta a matsayin ma'aikaciya idan suna bukata, sai dai ta manta bata dauko cv dinta ba sai a waya take nuna musu ko ta karbi number mai gurin ta tura masa. Kusan kowane shago kallonta ake domin bata yi kama da wanda zata iya aikin siyar abu a duka shaguna nan ba, dan haka wasu a take suke fada mata basa bukata, wasu kuma su yi tunani ko dai an turo ta ne, ko kuma an shirya yi musu wani zagon kasa ne, kadan ne suke bata tabbaci za su tuntube ta idan bukatar hakan ta taso. Ita kam a bakin gaskiyarta take neman gurin da zata iya tallafawa kanta, domin samun aiki na gobnati ko kamfani ba karamin abu ba ne ta san irin gwagwarmayar da ta yi kamin ta samu aikin da Amal ta yi mata sanadin barinsa yanzu kuma Aliyu yake son ta dawo saboda ya mulketa. Wani babban shago siyar da talkamin maza dake cikin quarters din dake kusa da unguwarsu ta shiga, sai suka yi mata maraba bayan security ya bude mata kofar shop din, kai tsaye ta tambaye manajan gurin sai da ta basu tabbacin babu wata matsala kawai tana son ganinsa ne sannan aka nuna mata shi. Ta doshi gurin da yake zaune tare da wani. "Ssnnu kai ne manaja a nan?" Ta tambaya mutumen ya kalleta Aliyu ma dake zaune ana sanya masa talkami a kafa ya juyo ya kalleta daga sama har kasa. "Eh sannu da zuwa fatan dai babu wata matsala ko?" Arba da ta yi da Aliyu ya saka duk wani hanzari da confidence nata yankewa, wani abu mai kamar fargaba kamar tsoro ya lullubeta, har take ji da ace ta san shi ne yake zaune a gurin ba zata karaso ba, gashi ta kasa sake hada ido ta shi kuma ta kasa cewa komai, ta jimke agogon hannunta dake kokarin zubewa dayan hannunta kuma ta rike jakarta. "Lafiya dai?" Mutumen ya tambaya, Aliyu ya sake juyowa a kallo na biyu sai dai wannan karon ya sauke idonsa ne akan agogon dake hannunta, fuska ba yabo ba fallasa ya mike tsaye. "Kala hudu nan sun isa for now" Ya saka talkamin da ya zo da su, ya ciro katinsa ya aje akan babban table din dake gabansa. "A kai min a wannan addireshin" Manajan ya kalleshi da mamaki domin be taba siye abu yace a kai masa gida ba sai dai a saka masa mota ya tafi da shi. "Okay ranka ya dade" Ya nufi gurin biyan kudi ya biya da amt dinsa har kudin kaiwar sannan ya nufi kofar fita, sai a lokaci Emily ta jiya juyawa tana kallon bayansa har ya fice. Sai kuma ta ji haushi kanta meyasa be mata magana ba ko ya nuna ya santa, and why ita ta kasa yin magana a gabansa. "Akwai abun da zan iya taimaka miki da shi" Ta karkarto hankalinta gurin manajan. "Eh, ina neman aiki ne a nan idan da hali" Manajan ya kalleta saka da sama domin bata yi masa kama da mai neman aiki ba. Ta gabatar masa da kanta kamar yadda take a sauran guraren ta karbi number wayarsa ta tura masa cv ta sannan ta fita jikinta na raya mata abu ne mai wahala ta samu aiki a gurin duba da wanda ta tarar da kuma irin kallon da mutumen yake mata kamar be yarda da ita ba. [4/27, 4:43 PM] : https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 ABOKIN RAYUWA
Chapter 37 · 0% Book details