Sashe 72
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Toh Allah dai ta shirya ka" Nura yayi dariya. "Ya shirya mu dai. Yanzu dai ya gidan ya kowa da kowa" "Lafiya kalau, ya naka iyalin" "Alhamdulillah" "Nura kai ka fi kusa da ni cikin dukan mutanen da na sani masu aikin lafiya, dan Allah wane likita ne ka sani kwarare ta bangaren kwakwalwa da zai iya duba mutum kuma ya fadi gaskiyar komai" "Me yasa kake neman Likitan kwakwalwa? Lafiya?" "Lafiya amman ba kalau ba, Matata nake son a duba" "Subhanallahi Kameela? Meya same ta?" "Wani kalar azababben kishi take fama da shi da ya wuce hankali, shiyasa nake son a duba kwakwalwarta abincika ko akwai wani abu" "Ban katsi hanzarinka ba, domin ni da kai musan duk mata suna da kishi sai dai na wata ya fi na wata, amman miyasa ka ce tana da azababben kishi? Wata kila abu ne da ba saka shi a muhallinsa ba sai ka yi masa fahimta baibai" "Nura, tun da ka ji na ce maka tana da azababben kishi tana da shi ne, ya wuce hankali" "Kamar me take yi" "Kamai ma tana yi har abun da baka tunani, kawai so nake ka bincika min likitan kwakwalwa da zai iya dubata, da ace kai ba likitan kwakwalwa ne ba na yara ba da kai zan nemi ka dubata" Nura yayi shiru na few seconds sannan ya ce. "Aliyu, look idan akwai matsala ne za ka iya fada min, kasan sometimes mu bukatar abokan tattauna sirri, kuma akwai abun da iyaye ba zamu iya barin iyaye su sani ba, kuma da can ni da kai bama boyewa juna sirri sai dan girma da kai muna yanzu da aiki da kuma rashin zama a guri daya, ya saka dukanmu muka maida hankalinmu gurin wasu abubuwan, amman ni har gobe idan ina cikin wata babbar matsala Aliyu kai ne mutum na farko da zan kira na shaidawa, domin bana kallonka a matsayin aboki kawai ko abokin karatu ko abokin gari daya, ina kallonka ne a matsayin dan'uwa na jini, domin sanadinka na zama abun da na zama Aliyu sanadinka na samu komai da na samu a yanzu, idan kana cikin wata damuwa dan Allah ka fada min" Aliyu ya sauki ajiyar zuciya. "Nura ka san Turhan ai?" "Eh na san Turhan" "Amman kamin nan daman Kameela tana da kishi kai ka sani kuma...." Ya fada masa abubuwan da suka faru tsakaninsa da Kameela da kuma Emily ciki har da alkawarin da yayi ma Kameela cewar ba zai mata kishiya ba. "Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, a lallai Kameela bata da hankali, taya zaki yi kokarin kashe mijin da be bijiro miki da maganar aure ba ma? Gaskiya rayuwarka tana cikin hadari, kana iya yanzu?" "Ina hotel na bar gidan" "Ka yi tunani mai kyau, amman ka yi kuskure Aliyu, tun farko be kamata ka mata alkawarin cewar ba zaka mata kishiya ba, be kamata ka haramtawa kanka abun da Allah ya hallata maka ba, ita mace mai kishi daga lokacin da aka fahimci tana da kishi taka mata burki ake, tun tana haukan tana kishin har ta gaji ta hakura idan ta fahimci ba zaka fasa son wata ko auren wata saboda kishinta ba, bayan kuma kishi ka yi hakuri da abun da zan fada da alama Kameela bata da zuciya mai kyau" "Na mata alkawarin ne saboda bana da ra'ayin kara auren, kuma da farko na yi tunanin aikata hakan zai saka hankalinta ya kwanta mu samu zaman lafiya ni da ita, shi aure Allah yace idan baka iyawa adalci karka yi, kuma ba lallai ne na iya adalci a tsakanin mata biyu ba, saboda rayuwa ni ba mutum ne mai son yin nan na yi can ba, ba kuma zan so na tashi gaban Allah da hakkin kowa ba" "Na fahimce ka duk namiji mai son zaman lafiya a gidan sa dole zai bi hanyoyin da yake ganin sun dace domin ya samu salama da matarsa, shawarar da zan baka a yanzu karka sake cin abincinta" "Daman na yanke wannan shawarar, kwana da ita a gida daya ma ba zan iya ba a yanzu sai ta samu lafiya" "Bayan samun lafiyarta ma, Aliyu babban abun da zaka yi shi ne kara aure, ta fahimci ba a ketare iyakokin Allah, kuma hakan zai rage mata kishi wata kila har ta zabi rabuwa da kai, dan na fahimci kana sonta sosai shiyasa ba zan iya baka shawarar cewar ka saketa ba, amman Wallahi zama da ita hadari ne sosai ga rayuwarka" "Zancen aure ko rabuwa da ita be taso ba yanzu Nura, shiyasa ban fadawa Ummi ba, dan na san ba zata bari na zauna da ita ba idan ta ji, kuma komai dan hankali ne, a sannu ake bi ayu bincike, shin yanzu zaka samo min likitan da zai dubata ko kuma na kashe wayata" "Zan samo maka mana dole na, akwai wane babban likitan kwakwalwa sunansa Dr Adam Bello, sai dai yana da wahalar gani gaskiya kamin ka sami ya duba ka ma sai kana da Connection, zan yi kokari na nema maka appointment da shi idan zaka ganshi sai ku zo Abuja" "Shi kenan na gode sai na jika" "Okay" Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Emily ya shigo wayarsa, ya dade yana kallon kiran baya cikin yanayin da yake son magana da ita a yanzu, sai dai kuma ba zai iya ganin kiranta ya kasa dagawa ba, domin be san dalilin kiran ba, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya kara a kunne, daga ita har shi shiru suka yi babu wanda yace uffan. "Ba zaka yi magana ba?" "Ba ke kika kira ni ba" "Da ka dauka amman kai ya kamata ka fara cewa Hello" Yayi shiru be sake magana ba. A shagwabe Emily ta fara magana. "Daman dai kawai na ji babu dadi abun da na yi maka dazun ne" "Kin san baki kyauta ba miyasa kika kira ni yanzu?" Tana jin hakan ta san ransa a bace yake wata kila har yanzu be sauka daga fushin fadan da ta yi masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, tana jin haushi meyasa ma to ta kirashi yanzu. After ta yanke kiran sai kuma ya ji babu dadi na furucin da yayi mata, ko ba komai ta fahimci beta kyauta masa ba ta kira be kamata yayi mata haka ba, a yanzu zata kara jin babu dadin ne. Without second thought ya kira layinta ringing daya ta daga. Ita dai data daga sai ta ari irin halinsa ta yi shiru ba tare da tace komai ba. "Dazun da kika kira cewa kika yi ni ya kamata na farawa cewa Hello" "Na san yanzu ka kira ka yi min bakar magana ne ko fada" "Me kika sani a halina da zaki yanke hukunci?" Ta yi shiru, jin shirun ya saka shi katse kiran, a take ta biyo shi da wani kiran domin bata san dalilinsa na kiranta ba gashi ta yanke masa hukunci kuma ta kara bata masa rai. Da ya amsa kiran ita da shi sai suka yi shiru babu wanda yace uffan har na tsawon lokaci. "Hello..." Suka furta a tare, ita a kokarinta na yanke shirun shi ma kuma a kokarinsa na yin magana kar tace ta kira ya amsa be ce komai ba. Sai kuma shirun ya sake biyo baya. "Zaki ce wani abu ne? Ko wani abu kike bukata?" "Idan baka da abun da zaka ce, ba sai ka sake kirana ba, mu ba yara ba ne be kamata muna haka ba" "Remember I'm your boss, ni da ke waya kira wani yanzu?" Ashe fa ita ta kira shi, bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, shiru yayi yana sauraren dariyarta a kunnesa tun da yake da ita be taba jin dariyarta ba sai yau, and ya san dariyar zata mata kyau domin farinciki ya dace da ita a yanzu dan haka ya fara imaging yadda take dariyar, kamin ita da shi su sake hada baki gurin cewa. "Okay Bye" Ya mata sallamar ne saboda ya fahimci bayan dariyar bata da wani abun fada, ita kuma ta masa sallamar ne gudun kar ta bata masa rai tun da ba wani abun zai fada ba. Bayan ta katse kira ya bi number ta da kallo sai kuma yayi murmushi. Be dauke idonsa ba wani kiran ya sake shigowa wayarsa da bakuwar number. Wannan karon ya amsa da sallama domin be san waye ba. "Sallamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam barka da dare" An fada cikin wata murya mai sanyi da be fahimci waye ba. "Barka dai" "Na san baka gane ni ba, Tasmia ce kawar Kameela, daman na zo gidan ne ban tarar da ita ba shi ne nace bari na kiraka ko kuna tare dan na kira wayarta ban samu ba" "No ban koma gida ba tukunan" Yana bata amsar ya katse kiran yana mamakin da ya kamata ace tambaya yayi mata cewar ina ta samu numbersa. [6/1, 9:15 PM] : https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03 ABOKIN RAYUWA