← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 177

Sashe 144

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ni, na rasa inda zan dafa, na gode Ammy na gode" Ammy ta yi murmushin jindadi. "Alhamdulillah da kika fahimci haka, ko kadan bana nufin cutar da ke, hada aurenki da Turhan ma ban yi dan cutar da ke ba, na yi ne da nufin sama miki mafita ta mijin aure ni kuma na samu mafitar ana a kusa da ni, idan har ina nufin cutar da ke taya zan aura miki dan da ni na haifa da ciki? Shiyasa da na fahimci akwai matsala na sauya masa na kasa saurarensa a dolensa ya bazama nemanki, gashi yanzu har ya gane kuskurensa yayi nadama babu abun da yake nema sai hada kan iyalinsa guri daya, kuma ina fatan zaki fahimce shi zaki yafe masa, ki yarda da shi ko dan yarki" Emily ta saki hannunta. "Yara ba su kai su hana iyaye farinciki ba Ammy, su yanzu suke tasowa rayuwarsu suke ginawa, shiyasa mahaifiyata bata bar farincikinta saboda ni ba, balle kuma ni da na yi ma Fatima komai da uwa zata yi ma yarta, idan har zan yarda a yanzu farincikin Fatima ya hana nawa hakan na nufin ni ban gina rayuwata ba kenan, abubuwan da suka faru sun faru kuma na ba su baya a yanzu, amman ba zan bar farincikina saboda Fatima ba, ba zan sake kuntata ma kaina sabida kowa ba" "Hakan yana nufin babu wani gyara tsakaninki da Turhan?" "Babu Ammy, ni ban taba son Turhan ba, har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kuma bana tunanin nan gaba zan ji, yanzu idan har nace zan sake zama da shi to ni ce zan cutar da shi, kuma na cutar da zuciyata to miye amfanin haka?" "Aisha ni kika kalli kwayar idona kika fada min baki son ana?" "Ki yi hakuri Ammy, kin san inda na fito kin rayuwar da ni, ke ma kin yi makamanciyar tafiya irin tawa, miyasa ba za ki fahimce ni ba?" "Saboda mahaifin Turhan be yi nadama ba, har yau be nemi ni ko neman afuwata ta ba, amman ke Turhan ya gane kuskurensa ya tuba kuma ya shirya faranta miki har hawaye ya zubar akanki, ya kauracewa abinci, bachi ma baya wadatarshi, da ace saboda Fatima ne kawai ai ba zai waiwaiyeki ba tun da ya same ta, amman saboda yana son ki yana son farincikinki ya kasa hakura, ki ba shi dama Aisha dan Allah" Emily ta girgiza kai. Sai Ammy ta kama hannunta ta rike. "Haba mana Aisha, ana na cikin mawuyacin hali saboda ke, ba shi kadai ba, Khaleefa ma ya munana miki iyayensa ma sun munana amman ni ban miki ba, miyasa ba zaki yafe masa ba, ki ma dakinki ki rumgume yarki da ke son Babanta? Duk wani sharadi da zaki gindaya mana ni na miki alkawarin za mu dauka" Emily ya sake janye hannayenta. "Ba zan iya ba Ammy ki yi hakuri, ba zan iya rayuwa da mutumen da ya shigo dakina a daren aurena ya tofa min yawu a fuska, ya kalli kwayar ido ya kira ranar da aka daura mana auren da bakar rana a gurinsa, ya shiga da ni gidansa a matsayin baiwa, yana kallo nake goge inda matarsa take takawa, yana sane ake dokana, be damu ya ba ni abincin da nake iya ci ba, ban taba dandanar dacin rashin magana ba sai da na auri Turhan, kuma ba dan bana iya maganar ba, sai dan ya gabatar da ni a matsayin kurma kuma ya saka min sharadin kar na kuskura na yi magana, a gidansa ban isa na saka kayan da nake so ba sai uniform din bayi, ban isa na kwanta a inda nake so sai tare da hadiman matarsa, ya kira ranar da ya kusance ni da bakar rana, ya fada min ba zai taba so na ko son abuj da na haifa ba, mutumen da yayi min duk wannan taya zai dauke ni a yanzu ya nunawa duniya yace ina da daraja? Ai ya gama kwance min zane a kasuwa kowa ya ga tsiraicina, Turhan ya haihu da ni kin samu jika har gobe ban isa na goge wannan ba, Ammy haka ma ya wadatar..." Ammy ya mike tsaye ba tare da ta kara cewa komai ba ta fice daga gurin. Emily ma ta mike tsaye ta nufi wani ice ta dafa shi da hannu daya dayan hannun kuma ta dafe kanta tana jin babu dadi na tunawa da rayuwarta ta baya. Tana tsaye a gurin bata motsa ba ta ji an kira sunanta "Aisha?" Ta juya ta kalli Turhan dake doso inda take tsaye hannayensa rumgume a baya yana tafiya daya bayan daya irin ta jinin sarauta. Ya tsaya gabanta yana kallonta daga sama har kasa for the first time ya ga kyauta irin kyaun da be taba ganin ta yi ba sai yau, duk kuwa da babu kwalliya a fuskarta, sai kuma kwarjininta ya kama shi gabansa har faduwa yake da take kallonsa ido cikin ido kallo irin na wanda ya tanadi amsar kowace tambaya. "Za mu iya yin magana da Allah?" "Yau kai ne kake neman izinina akan wani abu?" "Haba ki bar abin da ya wuce ya zama ya wuce mana Aisha! Na yi kuskure na sani kuma na karbi kuskurena, ke ma a yanzu kina cikin kuskure na barin wanda ba muharraminki ba yana kallon surar jikinki da kyaunki yana magana da ke yana jindadin muryarki, be ma kamata ki zauna a nan ba shiyasa duk abun da na fada ba fahimta kike ba, saboda ba zai taba bari ki fahimce ni ba, kuma ba zaki gane hakan ba sai nan gaba." "Na fada maka wani? Aliyu ya fi min kai amfani sau dubu, shi be taba fada min magana marar dadi ba, be muzantani ya fada min magana marar dadi ba, be doke ko ya saka a doke ni ba, be kira ni fasika ba, da na ba shi labarina be musa ba, ban roke shi alfarma ya gagara yi min ba, be yarda an wulakanta ni ba, ne gan ni a cikin damuwa ya bar ni balle har ya jefani a ciki, dan haka ba zan yarda wani ya fadi wata magana marar dadi akansa ba" Turhan ya hade wani abu mai daci da tsayawa rai yayi murmushi. "Ban zo nan saboda wani da be kamata ko sunansa na furta ba, na zo ne nan ne saboda ni da ke" "Babu wani abu tsakanin ni da kai, zama ne dai ada mun yi yanzu kuma ya kare, idan har zaka zo mu tattauna wani abu to ya kasance akan Fatima and Only Fatima" "Aisha miyasa idonki ya rufe har haka ne? Mu fa iyaline be kamata kina haka ba, ki yi hakuri da duk abubuwan da suka faru na san ban kyauta ba ina neman afuwarki ki yafe min dan Allah, Wallahi na yi nadama, kuma na yi bakinciki abubuwa na da na yi miki, ina neman afuwa, kuma na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba" Ya bata fuska sosai kamar zai mata kuka. "Na yafe Turhan, that's okay zaka iya tafiya ka yi rayuwarka" Ya kalleta da sauri domin be yi tsammanin zata yafe masa haka da sauri ba. "Kin yafe min Emily? Zaki koma zama da ni kenan?" "I forgive, never forget ba za mu sake zaman aure ba Turhan, na kasa manta abubuwan da ka yi min, ka fada min ba zaka taba kaunata ba wannan ya zauna a kaina" "Baki yafe min ba kenan, indai kin yafe min to zaki yarda ki zauna da ni ne Aisha, Fatima ma zata yi farinciki, idan har baki yarda kin aureni ba zan shiga mummuna hali Aisha, Wallahi ba ina fada miki haka saboda kan karya ba ne, har cikin raina ina kaunarki Aisha, kuma ina son zama da ke, idan kika guje min ban san iya halin da zan shiga ba, Wallahi ba dan ke ba, ba zan taba tako kafata a cikin gidan nan ba, ni yanzu damuwata ki amince da ni ban damu ko kina so na ko baki so na ba! Zan iya zama da ke a kowane hali, Aisha karki ba ni kunya a gaban makiya dan Allah, don't break my heart please" "You broke me first.... Shin baka yi tunanin ya abun yake da zafi ba? Ni ma a yanzu ban damu da duk wani zafi da zaka ji ba, ka tafi ni dai na yafe maka amman zama a tsakaninmu ya kare" Ya lumshe ido ya rasa ina zai saka kansa ya zai yi Emily ta fahimceshi. Emily ta wuce shi ta fice daga gurin, tana shiga falon ta samu Ammy zaune ita kadai a falon Fatima na saman jikinta, kallo daya Ammy ta yi mata ta san anta be samu nasara ba. "Momy nace dady ya dawo nan mu zauna tare gaba daya, ya fi dadi kina nan Ammy ma ta zo ga Uncle Aliyu ga Dady ko?" Emily ta girgiza mata kai. "Aa Dady zai zauna gurin Ammy, idan kina so zaki je ki gan shi" Sannan ta kalli Ammy ta ce. "Ammy na gode da ziyara, zan haura sama" Ta nufi stairs, Ammy ta bita da kallo har ta haura sannan ta sauke fatima a jikinta ta kama hannunta. "Fatima muje ko?" "Aa ki tafi sai gobe zan zo" "Baki son gurin Daddynki?" "Ina so gobe zan zo tare da Momy" Ammy ta saki hannunta ta fice rai a bace. [8/6, 11:10 PM] ABOKIN RAYUWA Khadeeja Candy* Page 6 Ammy ta same shi zaune a motar cikin wani yanayi marar dadi. Bata ce masa uffan ba shi ma be furta komai ba yaja motar suka kama hanya sai da suka isa gida ta bude motar ta fita sai ya ji shi ya kasa fita, yana mamakin yadda Aliyu ya shige masa hanci, haka zai zura ido wani katon banza yana kallon masa mata? Yana jindadin yayi nasara akansa? Miyasa wai tun farko be yarda girmama zabin mahaifiyarsa da yanzu duk be samu wannan matsalar ba. Ya dade a zaune a cikin motar sannan ya fita ya shiga falon ya zauna, Ammy ta kalleshi cikin tausayi da kuma bacin rai ta ce. "Turhan ka hakura da yarinyar nan, tun da ba mata suka kare duniya
Chapter 144 · 0% Book details