Sashe 24
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Ta kalli Fatima ta sake kallon Aliyu dake zube a gaban wayarta. Amman ta kasa magana. My bad Ya furta sannan ya kashe wayar, hotunan da Fatima ta tura masa ta duba a lokacin ne ta sake kallon Fatima cikin tsawa ta ce. Me ma'anar hakan? Ina kika san shi? Ina kika samu number shi? A nan kuma ta kwashe labarin komai ta fadawa mahaifiyarta, babu abun da ta boye ko ta manta tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau. Amman na fada miki ki daina magana da mutanen da baki sani ba, miye amfanin abun da kika yi, baki san manufarsa akanmu ba, bayan ganinsa da nake a kamfanin nan ban san waye shi ba, ban san halinsa ba Cewa yayi ya sanki Meyasa baki bari na gabatar miki da shi ba? Kin taba ganin na nuna miki shi ko na masa magana? Kin taba ganina tare da shi... Ta sake daka mata tsawa har tana mikewa tsaye kamar zata dake ta, Fatima ta razana sosai ta matsa baya tana fashewa da kuka. Sorry Momy Ta dafa kanta ya juya ta juyo gaba daya ta tsoro kamar wata marar gaskiya, can kuma ta koma ta zauna ta dauki wayarta ta aika masa da sako. Me kake nufi da abun da ka saka yata ta aikata? Me kake nema a yanzu? Bayan korar da kuka min yanzu kuma wani sherin kuke neman bina da shi? Ya duba sakon amman be bata amsa ba, kuma da alama be shirya yin hakan ba. Kana wasa da rayuwarka ne yaro, baka san waye ni ba, kuma bari na fada maka idan wani abu ya same ni ko ya samu yata sai ka yi nadamar zuwanka duniya Boy? Huh? Hmm Ya rubuto mata as reply. Kana ya rubuto mata. Mutumen da ya fada min halinki ya fada min babu ruwanki da fitina, amman naga akasin haka, bana nufinki cutar da ke, mu musulmai bama cutar da kowa, kawai ina nemi yarinyarki ta turo min hotunanki ne saboda tantance Aisha da Emily, ina son na san banbancin wacan mai kibar da ke, ina son na gane banbancin wacan marar masifa da kuma ke Waye kai? Ta mike tsaye tana kallon wayar gabanta na bugawa da mugun karfi. Hoton Turhan ya turo mata. Kin san waye wannan? Ta amsa da sauri gumi na karyo mata, sai ta kashe data ta goge chat din ta jefar da wayar akan gado, ta fara safa da marwa cikin dakin kamin hawaye su samu matsugunni a fuskarta. A nan ta fara tambayar kanta? Waye wannan mutumen tun farko? Meyasa yake bibiyar yarta da ita kanta? Yanzu kuma da ya turo mata hoton Turhan me yake nema a gareta? A kokarin samun amsoshinta ta sake daukar wayar ta bude data sai kuwa ta ci karo da sakonsa. Meyasa kike boya? Meyasa kika boyewa yarki gaskiyar cewar tana da uba? Why? Ta kasa bashi amsa jikinta rawa yake kamar yadda zuciyarta ma take rawa. Baki san yarki ta yi farincikin ganin mahaifinta? Baki taba tunanin samarwa yarki iyali ba? Kiran sunanta da ake da Fatima Aisha Emily be taba damunki ba? Idan yarki ta girma ta mallaki hankalin kanta wane irin amsa zaki bata? Nan ma bata amsa masa ba. Turhan yana ta nemanki babu dare babu rana, yana ta neman hanyar haduwa dake, wata kila baki san da hakan ba, amman yana da kyau ki hadu da shi ko dan yarki Ba kasan komai akan rayuwata ba, baka rayu a cikin duhun da na rayu ba, har yanzu ban gama warkewa daga ciwon da zan bukaci kowane namiji a kusa da ni ba, balle kuma Turhan, ba ni da alaka da shi, alakarsa da yata kuma na yanketa, daman be san da ita, idan ya saka shiga rayuwata da rayuwar yata ne saboda ya san halin da nake ciki, to ka fada masa Aisha da ya sani a da ba ita ce a yanzu ba, kuma kar ya kuskura ya tunkaro gurin da nake Ban riga na sanar masa ba, amman zan sanar masa a yau? Sanar da shi zai jefa rayuwarka da tawa da tasa a matsala ne kawai, karka aikata hakan, karka jefa ni a matsala, ina da yara har biyu yanzu, kokarin gina rayuwa nake, karka maida ni a kangin da na fito, ina da kudi enough zan biyaka ko nawa kake so, zan nika maka abun da ya baka dan Allah karka sanar masa, ina son yata ina son rayuwata, farincikina kankane karka barar da shi Tana rubuta masa sakon tana hawaye. Na miki kama da mutumen da za a biya kudi a aikata wani abu? Ke kina ganina kin na girmi talauci, duk abun da kike takamar kina da shi, ina takama da ninsa sau dari Amman kace kai musulmi ne? Yes haka ne, babu shakka Ina hada da Ubangijinka Ubangijin gaskiya, da Manzon Allah ( S A W) yace ranar tashin alkiyama Allah baya magana da mutum uku har da wanda aka hada shi da Allah be aikata ba, na roke ka dan Allah dan Allah karka fadawa Turhan komai akaina, idan kuma har ka fada masa to ka canja, dan darajar Manzon Allah S A W na san indai kai musulmin kwarai ne ba zaka aikata ba!!! Bayan wannan sakon bata sake aika masa wani ba, shi ma be sake cewa komai ba, ta aje wayar ta mike tsaye hawaye na cika mata ido har suna zuba ta fice daga dakin ta nufi dakin Fatima da tunin ta fice daga dakin na mahaifiyarta bayan ta fahimci nufinsa abun da ta aikata babban laifi ne. Emily ta tura kofar dakin sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Fatima dake kwance akan gadonta tana kuka, ta fara takawa tana tafiya jiki babu karfi, wayen da suke zubo mata a yanzu sun sha banban da na farkon. Jinjirar yarta take jangowa tana tuna lokacin da farinciki da kuma kishiyarsa suka lullube a rana daya, ranar da ta haifi Fatima, ta dauki cikin yarta ta yi rainon cikin ba tare da sanin Turhan ko danginsa ba, ta raini yarta irin rainon da bata fatan ko makiyinta ya fuskanci rayuwar data fuskanta, ta tuna lokacin da Nurses suke fadar a kawo kayan jaririya, kuma aka rasa abun da za a lulluba mata sai da wata ta taimaka mata da zane daya, ta tuna tsawon kwanakin da Fatima ta dauka a hannunta tana lullubeta da zane saboda babu tufafi. Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta saci nonon akuya ta shayar da yarta, ta tuna yadda ruwa yake dukanta a rumfar wani bakanike da take fakewa idan dare yayi, ta tuna yadda take bin gidajen masu hali tana neman abun da zata kai a ciki, taya rana tsaka a yanzu Turhan zai bayyana yace nemanta yake me yake nema a gareta? Ya rabata da yarta kamar yadda ya rabata da sauran farincikin da ya rage mata a wacan lokacin? Ya sake dawowa rayuwarta ya haifar mata da matsala? A yanzu ta samu mai bata komai yayi mata ginshiki shi ne yake neman rusawa? Ta kai hannu ta dago yarta, wani mummunan furuci da yayi mata a wani lokaci da farinciki ya juya mata baya ya dawo mata. Karki sake nuna kin san ni, akwai banbanci tsakanina dake Ta lumshe ido tana tuna wata rana da matarsa ta saka bayinta suka yi mata bulala yana kallo be yi kokarin hanawa ba har sai da suka bar mata tabo a jiki. Ta rumgume Fatima, wani kalar ruwan hawaye ne yake mata zuba mai zafi da dacin zuciya, ashe duk bayan wannan zai dawo nemanta? Momy me yasa kike kuka? I'm sorry Tambayar Fatima ta dawo da ita hanyacinta, sai ta bude idon ta share hawayen tana murmushi. Ina sonki Fatima, no matter what happen, daga ke sai London ne Iyalina, na wahala na yi sadaukarwa kamin ku kawo inda kuke a yanzu, a yanzu ma ban gama ba dan Allah kar wata rana ta zo ki fifita wani akaina Ta rumgumeta, sun dade a haka sannan ta sake ta tashi ta fice daga dakin, kasa ta sauka ta zauna a falo zuciyarta cike fal da tunani. Vito be dawo gidan ba sai after 8pm, ya shigo falon tare da Chidimma dake rike da leda tana biye da shi a baya. Emily ta kalleshi ta kalleta. Ina London? Bachi yake, na zo na dauki wasu abubuwan ne na yi wanka Ta maida dubanta gurin Vito, ya san abun da take bukatar ji tun kamin ta gabatar masa da tambayar ya bata amsa. Ya sauko ya daina fushi, na yi magana da shi Thank you Ta gyada mata kai kawai, sannan ya kalli Chidimma. Ki shirya da wuri direba zai maida ke asibitin kar a barshi shi kadai Okay Sir Ta amsa tana wani karairaya daman idan shi ya bada umarni ba ta bata lokaci take aikatawa. Sai da ta fice Emily ta maida dubanta gurin Vito da idanuwansa suka dade a fuskarta. Zan tafi na kwana can Ya amsa mata kawai da ido sannan ya nufi kujera ya zauna, ita kuma ta haura sama ta shirya ta fito ta shiga dakin Fatima ta yi mata sallama sannan ta sauko suka fice a tare, ya rigata isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya nufi bangaren da Chidimma take ya fada mata an samu sauyi zata kwana da Fatima saboda Emily zata kwana da London a asibiti, ya dawo motar ya ke kunne tun a lokacin da ya faka a harabar, daman a ka'ida baya kashe mota sai idan ya gama fita gaba daya a wunin ranar. Yana tukin yana karantar yanayinta har suka isa asibitin. Aikin fa? Na aje Ya kalli irin kallon mai cike da tambaya, sai ta sauke kanta kasa tana taba yatsun hannunta. Saboda na bawa yarana lokacina Ko dai sun koreki? Ya tambaya ne kawai ba dan hana da tabbacin haka din ba, domin ya san yadda ta kwalla fa rai da son aikin kuma har ta fara zuwa ba karamin abu zai saka ta aje aikin ba. Ta bude motar ta fice ba tare da tace masa komai