Sashe 28
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
sonta Amman ka cutar da ita? "Sau nawa zan amsa maka tambayar nan ne Aliyu? Shi daman zaman aure sai an yi hakuri, saboda zo mu zauna zo mu tsaba ne, kuma al'adarmu da addininmu ba daya ba, kuma yarinyar nan bata da asali Ban fahimta ba Ba a san su waye iyayenta ba, kuma ko da na zauna da ita zuwa can gaba idan an yi zuri'a baka tunanin zata iya juyar da hankalin yaran zuwa addininta? "Ita miye laifinta dan an haife ta a inda be dace ba, ba a shawara da mu kamin a zaba mana iyaye ko irin rayuwar da za mu yi kai kasan haka A haka din kuma addinin musulunci ya hore mu da auren mai asali, abubuwan da suka faru dai sun faru shikenan, sun wuce yanzu kuma nemanta nake na shirya tsakanina da mahaifiyata Allah yasa a dace Ya fada sannan ya aje wayar ya kalli Kameela dake ta leken motar tana dora kunnenta a jikin gilashin ita ala dole sai ta ji da wa mijinta yake magana. Murmushi yayi ya bude motar ya fito. Wannan ba halinki ba ne "Kai ma ai ba halinka ba ne idan kana waya ka boye min, me yasa baka son na ji Dole ai kin san akwai sirrin da zan yi da yan'uwa ko abokai ba zai yayu kiji ba ko? Kamar yadda ke ma na san akwai abun da ba zaki fada min ba Ni ai bana boye maka komai? Uhmmm Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan. Baka yi breakfast ba ka fita, kuma gashi ka dawo da damuwa, yanzu kuma ka yi waya ban san da waye ba ka rufe ban ji komai ba Be shafe ki ba ne ai "Abun da ya shafe ka ai ya shafe ni, ka fada min minene dan Allah dan Allah" Allah da ta hada shi da shi sai ya ji ba zai iya boye mata ba, kamar yadda ba zai iya fito mata da komai a zahiri ba. Yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba musu abun karyawa sannan shi ma ya zauna. Cin abinci kawai yake baya jindadinsa ba dan matarsa bata iya girkin ba sai dan bacin rai da ya fi kama da damuwa dake tare da shi. Dan Allah ka fada min Ya kalleta yana murmushi. "Kina da son gulma, toh akan Yarinyar da Turhan yake nema ne An same ta ne? Be same ta ba har yanzu, yana cikin damuwar rashin samun nata, hakan kuma ya shafe ni Toh ai be kamata hakan ya shafe ka ba, damuwar wani be kamata ace ta zama damuwarka ba Ya aje fork din hannunsa ya kama hannunta Ki daina wannan tunanin, indan akwai tausayi a tare da mutum dole ko da ba musulmi ba ne ya shiga wani hali marar dadi zaka ji babu dadi balle kuma musulmi dan'uwanka To wai shi ba zai je ya nemi yarinyar da kansa ba sai ya rika dora maka lalura waya sani ma ko yarinyar kyakyawa ce? Ta fada tana turo baki, hakan ya saka shi yin murmushi. Idan kyakyawa ce fa? "Idan kyakyawa ce ko ka ganta ai ba zaka fada masa ba" Baki yarda da mijinki ba? "Tohm zuciya ita kuma ai bata da kashi" Wai ke da na yi ma alkawari na yi ma rantsuwa aka yi abun har a rubuce cewar ba zan kara aure ba, ina ruwanki da duk inda zan shiga" "Shedan fa yana nan kusa zai iya sakawa ka karya alkawarin nan, kuma yadda kake da kyaun nan kake wanka idan zaka fita, ai dole hankalina ya tashi "Wallahi Kameela ba zan miki kishiya ba, ba zaki taba sharing dina da wata da sunan kara aure ko akasin haka ba, shikenan? Ya sumbance ta sai ta yi murmushi ta kwanto jikinsa. [4/20, 10:01 AM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA