← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 177

Sashe 31

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Dogon numfashi taja ta sauke ta matsa baya ta nufi kujerar dake dakin ta zauna. Ya bita da kallo for few seconds. Kina bukatar wani abu a yanzu? Ta girgiza kai alamar aa. Ya gyara tsayuwarsa. Baki bukatar yin aiki saboda ki gina kanki, baki bukatar tara kudi saboda ki gudu ki rayuwa a wani gurin dabam, daga lokacin da na baki gata ba zaki guje min ba, duk inda zaki je, duk iya gudun da zaki yi kina a cikin duniyata ne, ya kamata ki natsu karki jawa mutanen da suke kusantar kusa da ke mutuwa, bana sharing what ever is mine nawa ne har abada so you're mine Yana maganar zuciyarta na bugawa da karfi, hausawa suka ce idan babu rame me ya kawo maganar rame, ta san Vito yana kishinta, amman zancen ta daina kokarin gina kanta a ina ya ji wannan? Har ya juyo sai kuma ya juyo ya kalleta. Wannan mutumen da ya zo yau kin san cewa musulmi ne? Na sani Ta amsa tana hade yawu. Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da musulmi, kuma baki da alaka da kowa Ya juya ya fice ba tare da ya jiran amsarta ba, is like umarni yake bata, ya saba hanata hukda da kowa ciki har da kawaye be yarda da kusanci kowa haka ma baya yarda wasu su kusance ta. Ya mike tsaye ta nufi windows din dakinta tana kallon waje ta saka hannunta a baki tana cizon akaifarta, ita kam haka zata yi ta zama karkashin kulawar mazan dake da son zuciya? Kowane burinsa ta rayu a yadda shi yake so ba yadda ita take so, sai yaushe zata samu yancin kanta. Ficewa ta yi daga dakin ta sauko falo sai ta samu Fatima zaune tana zane. Kin yi magana da Uncle Vito Ba Uncle dina ba ne, bana son shi "Kin yi magana da shi? " Eh na fada masa, zaki yi aiki ki samu kudi zaki gina mana gida zamu koma can mu bar masa komai nasa Emily ta rufa ta fada. Wannan ai sirrinmu ne miyasa zaki fada masa? Saboda na tsane shi Toh miye amfanin abun da kika yi yanzu? Ya ssn manufata kina tunanin zai zuba min ido ne? Fatima me yasa kike da surutu ne? Kin lalata komai Emily ta zauna dafe da kai tana nadamar fadawa Fatima da ta yi tun farko. I hateeeeeee youuuuu Fatima ta fada cikin tsiwa da fusata. Emily ta dago ta kalleta cike da takaici. Idan baki tsane ni ba ai baki cika jinin Turhan ba Ta mike tsaye a fusace ta fice daga falon, dakinta ta sake komawa ta shiga bandaki da nufin wanka amman ta kasa aiwatar da komai sai kuka. Kuka ta yi sosai mai isarta sannan ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando ta dauki wayarta da keys ta fice daga dakin. Ta kai hannu zata bude kofar falon Fatima ta yi mata tambayar da bata yi zaton ta tsinci wani abu a maganar dazun ba. Waye Turhan Momy? Abokina ne Ta amsa mata kai sannan ta bude kofar ta fice daga falon. A mota ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya hana kanta kuka, bata tafi asibitin kai tsaye ba sai da ta fara shiga super market ta yi ma London siyayya abubuwan kwadayi da na wasa ta musu transfer sannan ta nufi asibitin. Sanin waye danta da kuma halinsa ya saka ta guzarin da ya rage mata ya tafi. Ta samu minti talatin zaune a motar sannan ta bude ta fito ta dauki kayan da ta siyo masa ta rufe motar ta nufi cikin asibitin. Kamin ta karasa ta inda zata karya kwanar da ward din London yake ta hango Aliyu tsaye yana waya, tun da ta sauke idonta kasa bata sake kallonsa ba har ta isa gurin da yake tsaye, ya sauke wayar dake kunnensa ya kalleta kadan ya dauke ido domin tsare mace da ido wanda ba muharamararsa ba halinsa ba ne. Me kake so? Miyasa kake bibiyata? Baka lura da irin mutumen da nake tare da shi ba? Be tsorata ni ba, be kuma burge ni ba Yana isa sanin komai nake aikawata, kuma ko'ina akwai mutanensa, shin baka yi mamakin yadda Williams ya baka address dina ba? Bayan kuma be taba zuwa gidan ba? Ki ba musulma bace bani da wata alaka da kai Be sake magana ba yayi gaba ya barta a gurin tsaye juyawa ta yi ta bi bayansa da kallo har ta daina hango shi, sai kuma ta ji babu dadi, a zatonta ta tsorata shi ne. Dip sakon kar ta kwana ya shigo wayarta. Ba halina bane tsayuwa da mata, balle kuma wanda addininmu ba daya ba, a duk lokacin da kika shirya zaki iya dawowa aiki zamu yi magana a can Ta maida wayar aljihu sannan ta shiga ward din, tsayawa ta yi jikin kofar ta daidaita fuskarta ta cusawa kanta murmushi da farincikin dole sannan ta tura kofar da shiga. Hello Big Guy "Dariya yake amman yana ganinta sai ya hade rai ya juya baya daga kan gadon da yake zaune Har yanzu fushi kake da ni London? Sannu da zuwa Chidimma ta fada, ta mike tsaye London ya rike hannunta alamar baya son ta tashi. A haka dai Emily ta danne zuciyarta ta karasa kusa da shi ta gefen da fuskarta take ta leke shi da murmushi a fuskarta. My Handsome Guy... Aiko yace me zai mata ba ihu ba, yana ihu yana matsawa nesa da ita kai kace be santa ba ne, ko ayi zaton sace shi zata yi. A gurin ta watsar da kayan dake hannunta cikin tsawa da fara magana. Kullum damuwata akan yarana ne, tun ina karami ban san wani wanda ya damu da matsalata ba, ban san wani wanda ya damu da farincikina ba, kowa da na gama masa amfabi jefar da ni yake, guduna yake yanzu kuma ta kai har ga Yayana? To ka zauna da wanda kake so Ta fice daga dakin a fusace. Chidimma taja shi jikinta ta rumgume jikinsa sai rawa yake domin ba kasafai take masa fada ko tsawa ba. Momy bata son London, Momy ta yi fushi ta tafi ta gurin Fatima, Fatima kawai Momy take so, bata son London, ta gaji da London ta tsane shi Tana masa maganar tana shafa bayansa. Bata son yayi wasa da kowa, amman Chidimma tana son London tana barinsa yayi wasa da ruwa tana fita da shi yawa London ya bata rai sosai ya labe a jikinta kamar zai yi kuka, sauka ta yi daga kan gadon ta duka kasa. Hau bayana zamu yi doki Da sauri ya hau yana dariya domin yana son kalar wasar da take masa. TURHAN POV. Sai da Faruk ya gama yi mata bayanin dalilinsu na zuwa gidan da turanci, domin Turhan baya jin turanci sai larabcin Sudan sai kuma hausar da ta kasance yaren mahaifiyarsa. Matar ta yi murmushi ya gyara zaman kujerar da ta yi mata kadan kasancewar kujerar one seater, ita kuma mace ce mai jiki sosai ba kadan ba. Bani da wata alaka da Emily a yanzu, tana raye ko a mace ba matsala ta bace, ban kuma damu na san kowane irin hali take ciki ba, mu dai mun daukota daga gidan marayu ne da nufin bata kyakkyawar rayuwa da gata, sai gashi ta watsa mana kasa a ido ta gudu ta bi saurayinta, idan ma wani laifin ta yi muku ko to ku tafi can wani gurin ku nemata, bana da alaka da ita a yanzu Amman baki san wata hanyar da zamu iya ganinta ba? Ko jin labarinta? A lokacin da ta bar nan kina da labarin inda ta koma da zama Ban sani ba Ta mike tsaye ta fice ta bar musu falon, Faruk ya fadawa Turhan abun da ta fada, sai ya tabe baki yana magana da kakkausar murya. Butulu ce ma shiyasa ba zata ga daidai ba a rayuwarta, gashi nan ta zo ta shiga tsakanina da mahaifiyata, an kai karshen ba zan sake nemanta a ko'ina ba yanzu A tare suka fito da Faruk suka shiga mota, kamin su isa masaukinsu Turhan ya kira mahaifiyarsa a waya, sai da yayi mata kira biyu sannan ta daga wayar. Hello Ammy Kuna lafiya? Lafiya kalau, Ammy na yi iya yadda zan iya, na yi neman yarinyar nan har na gaji ban samu inda take ba, macen da ta rike ta ma tace bata da labarin inda take a yanzu, ban san ya zan yi ba Ammy Ban cilasta maka nemanta ba Turhan kai ka cilastawa kanka Amman Ammy fushi kike yi da ni fa, idan ban samu yarinyar nan ba ba zan samu yadda nake so a gurinki ba Na dade da yafe maka, kuma bana fushi da kai, iyakar abun da na sani shi ne, Aisha ta tafi da farinciki, ta tafi ta bar min wani tabo da na kasa kankare shi a zuciyata, a duk lokacin da na kalleka sai na ga wannan abun a tare da kai, a dawo lafiya Allah ya tsare hanya Ta aje wayar. Turhan ya ji kamar ya buga kansa da motar. Allah ya kara tsine miki albarka Emily mushirikar banza, yadda kika jefa rayuwata a matsala kika raba ni da mahaifiyata Allah ya hana farinciki kusantarki Ya dafe kansa ya rufe ido, a yanzu kam ba shi wata babbar makiyiya irin Emily. Macijiyace yarinyar nan kawai rab ar mutane take tana cutarsu haka zuciyarsa take raya masa. The fallowing day yayi sallama da Faruk yayi masa alheri sannan ya kamo hanyar dawowa Kaduna. Yana sauka Airport ya sanarwa mahaifiyarsa babu bata lokaci da aika masa da direba ya dauko shi zuwa gida. Ko da ya iso ya samu an shirya masa abinci mai kyau a dinning, amman be kula komai ba saboda hankalinsa yana gurin mahaifiyarsa, dakinta ya shiga sai ya zame ta zaune tare da Jawahir suna dariya da alama hira suke, sai dai shigowarsa ya saka Ammy sauya dariyarta zuwa murmushin da ba kasafai take masa ba. Sannu da zuwa Jawahir ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin. Cikin wata irin tafiya ta kaisaita
Chapter 31 · 0% Book details