Sashe 100
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da iyayena, domin iyayena babu abun da suka mata sai alheri, kuma ina tunanin da ace baki ga alamar za a rike Kameela da daraja ba, da ba za ku ba ni aurenta ba" A take Hajiya ta zaburo masa da fada. "Alherin me suka mata? Me suka kulla mata tun da aka yi auren? Duk tsabanin da kuke samu ummi ta taba tako kafarta gidan nan da sunan danta yayi ba daidai ba zata bada hakuri? Mahaifinka ma harkokin siyasarshi kawai ya saka a agaba, yanzu din ma ai ba kai ya kamata ka zo ba iyayenka tun da ba daga mu sai kai muka baka aure ba, kuma Kameela ba daga sama ta fado ba tana da gata, kar na sake ganin kafarka gidan nan da sunan biko wannan iskanci da tsageranci na surukan zamani ni ba zan dauke shi ba, kana neman bata min lokaci ina da abu mai muhimmamci a gabana" Ya koma cikin motar ta shige direbanta ya rufe sannan ya shiga motar yaja suka bar Aliyu tsaye kunshe da bakinciki kamar ya kashe shi, meya ma ya zo tun farko meyasa ya kawo kansa? Sai a yanzu yake bakincikin neman auren kameela tun farko, domin auren macen da iyayenta ba su dattijai ba ne abu ne mai illa sosai ko da kuwa ita yarinyar tana da tarbiya. Shi aka yi ma laifi ya daure a haka ya zo bikon matarsa amman mahaifiyarta take fada masa magana son ranta. Juyawa yayi ya shiga motarsa ya kama hanya yana yi ma kansa alkawari na damuwa ba ko cewa aka yi Kameela zata mutu akansa ba zai dawo bikonta ba. Yana hawa titin unguwar kiran Emily ya shigo wayarsa. Fakin yayi gefen hanya yana maida numfashi a hankali wani irin tafarfasa zuciyarsa take be san lokacin da ya daki sitiyarin motar da karfi ba tsabar bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya bi kiran Emily da already ya yanke bayan ta yi ringing be daga ba. KAMEELA POV. Tana can kwance dakinta bata san wainar da ake soyawa ba har sai da Hajiya ta kirata tana mata gargadi wai karta kuskura Aliyu yace ta zo suke ta bishi daga ita sai shi ko saukowa ma kar ta yi ya ganta ko da ya kirata. "Aliyu ya zo ne?" "Eh wai wani ya zo bikonki a nan na bar shi na tafi gurin sabgogina" Kameela ta bude baki kamar ta yi magana babu hali, domin ita kadai ta san yadda suka tsara da Mama Barakat har aka samu kansa ya zo, kuma ta san ita ce mai laifi amman be fada a gidansu ba kuma be fadawa iyayenta ba haka kuma ya danne komai ya zo bikonta meyasa Hajiya zata mata? "Hajiya kuma kika ki saurarensa" "Ke dalla can rufewa mutane baki, shiyasa yake wulakantaki ai, saboda baki san daraja kanki ba kina nuna masa rawar jiki da shegen so shiyasa yake gallaza miki yadda ya ga dama har da wani turo ki gida tsabar rainin wayo da wulakanci, kar na ga kafarki waje dan na san halinki shiyasa na kira na gargade ki" Ka kashe ta tashi ta sauri ta leka windows dakinta bata ganshi ba balle motarsa, saukowa tayi kasa ta shiga bangaren Mama Barakat ta tambaye ta ko Aliyu ya shigo bangarenta. "Ya shigo baki gan shi ba?" "Kai..." Ta juya ta fita da sauri tana kiran layinsa bugu daya aka daga sai ta yi shiru tana jiran ya fara magana. "Hello." Ta ji muryar karamar yarinya. "Wacece wannan?" "Hello can you hear me" Fatima ta sake fada domin bata fahimci yaren Kameela da kyau ba. "Yes who are you?" "Sunana Fatima Aisha Emily" Kameela ta sauke wayar daga kunnenta ta duba layi ta ga na Aliyu ne sannan ta sake maida wayar. "Ina mai wayar?" "Ya fita ya siyo min ice cream" "Ke kina ina?" Ta dayan bangaren Fatima ta kalli inda take. "Ina falo" "Falon wa? A ina?" "A gidan Uncle Aliyu" Da turanci Fatima take amsa mata. Kameela ta kashe wayar tana jin wani jiri yana debanta zuciyarta ma tafasa numfashinta har sama yake yana dawowa. Ta nufo bangarensu tana mamakim abun da ya kai wayar Aliyu hannun yar Emily domin ta san suna da ya kuma gashi yarinyar ma ta ambaci sunan mamanta. "Wato Aliyu ba zai rabu da matar nan ba, kuma be shirya rabuwa da ita ba, wai da ita ya zo ne ko kuma yaya? Ni ban gane ba?" Ta haura sama tana magana da kanta kamar wata mahaukaciya. Sai kuma ta sake kiran Number Fatima ta dauka kamar zata yi kuka. "Kina damuna ina kallon Cartoon ne" "Ke fada min a wane falon? PH ko Kaduna?" "Kaduna jirgi muka shigo muka zo Kaduna ko da muka zo ina bachi ma" Kameela ta kashe wayar tana jin kamar ta haukace tsabar bakinciki wato har Kaduna ya zo dayar Emily saboda ya raina aurenta kuma ya raina mata hankali, hijab dinta ta dauka ta saka ta fita dakin ta shiga dakin Hajiya ta dauki makullin mota ta sauko kasa ta fice falon babu wanda ya sani ta shiga motar Hajiya ta dauki hanyar gidan Aliyu, yau kam ta shirya ayi ta kare domin ba zata juye wannan wulakanci da Aliyu yake mata ba akan wata kafirar banza da ba matarsa ba. EMILY POV. Ta sauka Airport around 5:02 tana fitowa ta kunna wayarta kamin ta kira Aliyu sakonsa ya shigo wayarta, bata wani tsaya duba sakon ba ta danna masa kira ringing daya aka daga. "Aliyu ina yata take?" "Hello" Muryar Fatima na dira kunenta ta tsaya cak ta lumshe ido. "Fatima my beautiful baby girl" "Hi Momy" "Ina kike?" "Ina falo" "Falon waye a ina? Ina Aliyun yake ina ya kaiki" "Gidanshi ya fita ya siyo min ice cream" "Momy ki daina damuna ina kallon cartoon ki kira dayan kira dayan wayarshi" "Okay my Love, i love you okay" Bata tsaya amsawa ta kashe wayar ta cigaba da kallonta, hawaye ya saukowa ma Emily sai kuma ta ji wani iri idan ta yi arba da Aliyu me zata fada masa bata yarda da shi ba? But she has no other choice dole ta sanar masa tana Kaduna kuma hankalinta zai fi kwanciya idan yarta na kusa da ita. Ta gwada kiran dayan layin nasa wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, kanta ta sauke kai ta kalli jacket din Dr A-B dake daure a jikinta sai kamshin turarensa take, kira ne ya shigo wayar ta dago da sauri a zatonta Aliyu ne sai ta ga Vito a nan ma bata daga ba har wayar ta gama ringing sai ga kiran Aliyu ya shigo. "Hello" "Aisha" "Naam" Sai kuma ta yi shiru. "Na gwada kiran wayarki bata shiga kuma na miki text baki maido min da amsa ba, lafiya?" "Lafiya alau, hankalina ne ya tashi da kace min ka tafi da Fatima na kasa natsuwa kuma na kira wayarka ban same ka ba..." Magana take a shagwabe tana yi tana yankewa. "Na zo da ita ne saboda na san kina bukatar space, kuma zuwa da ita ba wani abu zai haifar ba In Shaa Allahu lafiya kalau zan dawo da ita, gobe ma zan dawo, I'm so sorry na tafi da ita ba tare da neman izininki ba" "Aliyu ina Kaduna fa..." "What? Wasa kike yi?" Ta girgiza kai. "No da gaske ina Kaduna ina Airport ma yanzu haka, hankalina ya tashi ne please ka fahimce ni ina son yata ba zan taba samun natsuwa idan bata kusa da ni ba" Mamaki ya hana shi kara tambayarta wani abu. "Kina ina a airport din" Ta fada masa sai ya kashe wayar, guri ta samu ta zauna tana ya kallon mutanen dake kai da kawo feeling so guilty kamar wanda ta aikata wani laifi. Tana zaune a gurin har sai da ya sake kiranta ya fada mata inda ya faka ta daga kai tana kallo har ta hango shi tsaye jikin motar sanye da manyan kaya da hula. "Na ganka gani nan zuwa" Ya rike wayar yana ta kalle kalle har ya hangota tafe sanye da riga da wando sai kuma jacket din dake daure a kugunta, gashin kanta ya rabo gida biyu sai bin iska yake tana tarewa. Idan yace Emily bata da kyau yayi karya ta ko'ina ta kai mace duk wani abu da namiji zai kalla a jikin mace ya sota Emily tana da shi, a kokarinsa na haramtawa kansa kallonta gudun wuce gona da iri ya saka shi kawarda idonsa sai ya lura mutanen dake tsaye kusa shi ma kallonta suke, na nesa da ita ma kallonta suke domin ta ko'ina mace ce mai jan hankali, ko ba dan jikinta da kyauta ba dole a kalleta domin gashinta da idonta da kuma hasken fatarta. Hakan ya saka shi jin babu dadi domin a musulunci mace mai kima ce suturta ake. "Hi" Ta fada tana kallo nsa a yayinda take tsaye a gabansa, ya kalleta karab idonsa suka fada cikin nata idanuwan masu matukar daukar hankali, sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi da kyau, duk wani bacin rai da damuwa dake tare da shi sai ya ji yayi kasa kamar an jefa dutsen kankara a rijiyar dake cike da ruwa take fitar da kara tit tit tit haka zuciyarsa ke bugawa a hankali ba bugawar tsoro ko fargaba ba. "Wane irin dress ne haka? Kin sake komawa Emily dinki kenan nan?" Ta kalli jikinta sai a lokacin ta saka hannunta kwance jacket din Dr A-B dake daure a jikinta. "Haka na zo, Dr Adam Bello ne ya daura min wannan jacket din tasa" Ta yi zaton yadda ta dauro jacket din ne be masa dadi ba. "Waye Dr Adam kuma?" Ta fada masa shi ne likitan da suka hadu asibiti da Tasmia ta kwanta kuma ta fada masa irin hidimar da yayi mata a yanzu har ta samu sauka a airport din. Aliyu ya dan ji babu dadi kadan ko ba komai uwar yar abokinsa ce be kamata ace tana mu'amala da maza anyhow ba, ya san ta dana kyau karamin aikin yan'uwansa maza ne su kawo mata hari da alheri ko da sheri. "I thought i warning