← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 177

Sashe 155

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta mike tsaye. "Yanzu zaki tafi? Na zaki tsaya ko abinci ki ci ba?" "Bana jin yunwa" Mama Baraka ta dan yi shiru. "Toh jira ni ina zuwa" Ta juya ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta. Misra ta taso daga inda take zaune ta tsaya gaban Emily. "Idan baki kasance da Mama ba, baki bata dama ba taya zaki fahimci tana kaunarki? Kuma ita uwace a gareki? A tsawon lokacin kullum maganarki amman saboda bata son bata miki rai ya saka ta hakura ki zauna a can, idan kika tafi Abuja abu zai bata wahala, tana shan gori a gidan nan, ga Mahaifinmu ya juya mata baya, duk abun da muka fada mata bata ji tana cikin damuwa, amman na san idan kina kusa da ita zata samu salama" "Ni kaiwa bana son na yi nisa da Ummi ne?" "Why? Saboda Aliyu? Kar ki yi ya i akan namiji, amman ki bar namiji ya ya i duniya akanki, ke na ki kawai kyautata ce da biyayya, ta nan ake gane namijin da yake sonka da gaske da kuma wanda a baki ne kawai, indai yana sonki ba zai yi nisa da ke ba, kuma zai fiki shiga damuwa, idan namiji yana son mace duk wani baki da bakibaki nata ba zai gani ba, ke da kika sha wahalar rayuwa, ki bar mai sonki ya nuna miki son gaskiya" Emily ta yi shiruuu tana nazarin kalaman yar'uwarta, Mama Baraka ta sauko ta mikewa Emily waya. "Ga waya na siya miki na zo na baki ne idan naje, amman tun da kin zo duk daya ne" Emily ta karba da hannu daya sai Mama Baraka ta janye wayar bata bata ba. "Saka hannu biyu ki karba shi ne biyayya, musamman ga iyaye" Emily ta saka hannu tana jin wani abu a zuciyarta for the first time uwarta tana koya mata wani abu daga zamantakewar rayuwa. "Allah ya miki albarka" Mama Baraka ta fada. Emily ta mata godiya. "Na gode" Sannan ta juya Mama Baraka ta rakata har gurin motar da ta zo ta shiga. Direban yaja motar suka juya, sun fi to gate din kenan ta hango wata farar mota fara sol fake a can dayan bangaren dauke da bakin gilashi, slowing aka fara sauke gilashin har ta hango mutumen dake ciki, zuciyarta ta buga da karfi hankalinta ya tashi ta fara waige tana kallon motar kamar zata fita ta tafi can. Mutumen da Aliyu yace mata ana nema taya kuma ta ganshi a nan? Hakan yana nufin Vito yana bibiyar rayuwarta kenan? Taya ya san ta zo nan? Ko dai ta cewa direban ya juya ta yi magana da shi? Idan kuma ya sace ta fa? Ya daga hankalin sauran mutane? Domin ta san ba zai iya kasheta ba. Har suka isa gida bata samu amsa ko gamsuwa daga hasashen da take ba. Ta bude motar ta fito tana arba da Aliyu da ke tsaye da Tasmia a harabar gidan, take ta ji numfashinta ya fara gargada, kamar fa wannan tashin hankali da take gani na yanzu ya fi wacan, gaba daya sai ta manta da wacan kuma ta kasa boye hakan a zuciyarta. Tana tahowa Aliyu yana kallonta da murmushi a fuskarsa, hijab a jikin mace ba karamin kyau yake mata ba, sai a yanzu yake gane idan ya samu Emily ba karamar kyauta Allah yayi masa ba. Sai dai ga mamakinsa tana kawowa kusa da su sai ta wuce shi kamar bata gansu ba, Aliyu yayi hanzari shan gabanta. "Ayusher baki ga Tasmia ba?" "Na ganta?" Ta amsa cike da fushin da bata san na miye ba. "Gurinki ta zo fa?" "Kuma take tsaye tana magana da kai?" Ya daga hannayensa sama. "Forgive me my Lady" Ya juya ya nufi entrance yana murmushi, ba karamin dadin ya ji ba ganin yadda Emily ta sauya fuska na ganinsa da Tasmia hakan ya kara fahimtar da shi abin da yake hange a idanuwanta, ya nufi gurin ya tsaya ya juyo tana kallonsu domin zuciyarsa bata natsu ya tafi ya barsu ba. Emily ta juya ta kalli Tasmia with so much confidence. "Ya aka yi?" Tasmia ta yi murmushi ta taka few steps ta isa gabanta ta tsaya. "Bakuwar bata zafi ba ce, na san kina kallona da abubuwan da suka faru a baya, ban kyauta na gano haka daga baya, kuma na zubar da komai saboda ni ma Allah ya ba ni mai kaunata, kwanan baya Kameela ta zo gidanmu ta same ni da labarinki, Wallahi sai tausayinki ya kama ni na hango da ace ni ce a yadda kike ya zan yi? Har na ji kunyar abun da na aikata shiyasa na zabi zuwa na baki hakuri ke da Aliyu kuma na biyo ta gefensa saboda ke ba a samum wayarki ba lallai ma idan na zo kai tsaye ki saurare ni ko ki yarda da ni ba, amman dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, ba kuma ina nufin sake alaka dake ba ne aa ina neman yafiyarki ne kawai" Emily ta sauke ajiyar zuciya. "Ba komai na yafe miki" "Na gode, kuma na miki murna Aliyu ya fada min kin musulunta na jidadin haka, sai dai kuma zan baki shawara ki yi taka tsantsan da Kameela, domin tana neman hanyar da zata cutar da ke ne har yanzu, zuwan da ta yi ma ta nemi na bata hadin kai mu yi miki wata illar wai ko acid ne a watsa miki, amman ban bata hadin kai ba daga karshe ma da fada muka rabu" Emily ta matsa baya tana kallon Tasmia da dan tsoro. Sai Tasmia ta yi murmushi. "Ke da kike da Aliyu miye na tsoro, kamin ya yarda ya zo nan sai da na sha wahala kuma ya gargade ni, jakar nan tawa ma sai da bawa wata yarinya a gidan nan ta bincike komai a ciki saboda baya son wani abu ya same ki" Emily ta juya ta kalli Aliyu dake tsaye hannayensa biyu a aljihu yana kallonsu kamar irin kallon nan da motsi kadan yake jira Tasmia ta yi yayi tsalle ya dira gurin. Tasmia ta ciro IV aurenta ta mikawa Emily. "Ba dole sai kin zo ba, tabbaci nake son ki samu babu ni babu cutar da ke har abada" Emily ta karba. "Congratulations" Ta juya, sai Tasmia ta kirata, ta juyo. "Aisha ko? Haka Aliyu yace na kira ki baya son sunan Emily. Ki rike Aliyu shi ne ABOKIN RAYUWARKI, kun dace da juna, ABOKIN RAYUWA ne na gari, ke ma kuma kin dace da shi domin baki da hayaniya" Emily ta juya tana kallon Aliyu. "Na barki lafiya" Har Tasmia ta fice daga gidan Emily bata sani ba domin idonta suna kan Aliyu. Ya sauko a hankali zuwa inda take tsaye. "Wai kokari kike sai kin kure kallona kin hango muni na? Idan ma kin ga haka sai dai ki yi hakuri da ni, domin kaddara ta gina mana gida kuma dole sai mun shiga, idan za a hau sama a fado ni dai ba zan yarda ki bar ni ba, na zama karfen kafa, yanzu akan Ayusher bana jin has, ni kadai nake gane abin da nake ji, idan na mutu ke ce sanadi" Yana maganar cikin sigar kaunar da soyayya. Murmushi ya zama matar wajib zuciyarta na lasuwa da kaunarsa. Ya ciro dayan hannunsa a aljihu tare da wata yar karamar fulawar Rose mai matukar kamshi ya shinshina sannan ya risina ya aje mata kasa a gabanta. "Hankalina yana kwantawa idan na yi arba da murmushinki, idan kika kalleni sai na ji kamar na fi kowa farinciki. Ga tukuicin kallonki Sarauniyar abar da ban fada ba" Ya wuce yayi gaba abunsa kamar ba daga bakinsa kalaman suka fito ba. Emily ta duka ta dauki flower ta kai hancinsa wani kamshi mai sanyi ya ratsa hancinta ya sanarwa kwakwalwarta, kwakwalwar ta sakarwar zuciyarta sakon kai tsaye. A lokacin da ta bude idon sai ta hango shi rike da kofar falon alama ita yake jiran ta fara shiga. Ta mike tsaye ta fara takawa tana kallonsa, shi kuma ya dake ya ki yarda ya hada ido ta ita wannan karon duk kuwa da ya san idanuwanta suna kansa ne. Takunta yake kallo yana kirga tazarar dake tsakaninsu har ta iso kusa da shi ta tsaya. "Na gode da kika karbi kyautata, ina hango rayuwa ta har abada a cikin idanuwanki" Ya kalleta suka sake sakarwa juna murmushi. A cikin wani sabon tattausan halshen ya furta. "Lady's first..." Yana nuna mata cikin falon da dayan hannunta, ta dauke kai ta wata zumar kauna na dibanta ta shiga falon. [8/19, 7:16 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 155 · 0% Book details