← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 177

Sashe 148

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ta tambaya da motsin baki ba tare da ta fitar da sautin ba, sai ya girgiza mata kai alamar aa ya dauke idonsa tare da hade rai yadda ake yi ma yara, ta san ba zai wuce saboda bata saka dankwali ba sai ta yi murmushi ta karasa gurin motar daya bude mata ta shiga ta zauna tana ta kallon fuskarsa domin kallonsa na daga cikin abubuwan da take so, shi kuma be yarda ya sake hada ido da ita ba ya rufe motar ya juya ya nufi hanyar shiga Falon. Direban yaja motar suka fice daga gidan, tana zaune cikin motar shiru shiru sai kallon titi take, can kuma sai ta yi murmushi. "Aliyu" ta furta sunansa a hankalita kwanta jikin motar tana juya ido zuciyarta cike da nishadi, sai da direban ya shiga gidan sannan ta saita kanta tana kallon rayuwar baya da ta taba shigowa gidan, ta kai hannu zata bude Direban ya ce. "Hajiya dan jira, Alhaji Aliyu yace kar na bari ki fita motar sai matar ta fito, tun da ban san wane bangare take ba" Ya daga wayarsa ya kira Aliyu ya sanar masa suna cikin gidan. Babu jimawa Mama Baraka ta fito ta dayan bangaren da farinciki ta nufo motar da suke ta budewa Emily. Emily ta fito bata wani dauki sosai Mama Baraka ta rumgume ta tana jindadin zuwanta, sannan ta kama hannunta suka nufi bangaren da ta fito, da suka shiga gate din ta ratsa da ita suka shiga falonta, suna shiga falon Emily ta yi arba da Dr AB zaune sai ta saki hannun Mama Baraka ta nufi shi, shi mike tsaye da sauri yana murmushi suka rumgume juna. "Kina lafiya?" Ya tambaya bayan ya dago ta daga jikinsa, sai ta daga mishi kai. "Ina lafiya, yaushe ka zo ya aka yi ka zo nan?" "Saboda ke" Ya kama fuskarta ya rike. "Madam Baraka ta fada min komai, a washe garin da kuka bar gidan, kuma na jidadi da ya zama ina da alaka da ke" Hawaye ya sauko mata ta runtse ido tana jin wani sanyi na sanin cewar shi dan"uwanta ne kuma ya karbeta. "A yanzu na gane dalilin da yasa nake ta son kasancewa da ke Emily, kowace haduwa kaddara ce take shirya mana ita, amman na kasa cireki a raina na kasa manta duk wani abu daya shafe ki, ada ina tunanin kamar na samu mata ne, ban sani ba ashe ke jinina ce, tun dawowarki gidanku zuciyata ta fara raya min kamar kina da alaka da mahaifina saboda kamar da kike da shi ta yi yawa, amman sai na rika tambayar kaina ta ina? Taya yaya? Da kika ba mu labarin rayuwarki, sai na fara tunanin ko sace ki aka yi aka jefar a can? Ko kuma dai bayan Momy mahaifina ya zauna da wata matar? Ita kanta Momy ta fada min kina kama da Mahaifina" "Ina Momy take?" "Tana gida, ni na saboda ke na zo, kuma yau zan koma" "Ta samu labarin abun da ya faru?" "Eh sai dai bata yi maraba ba, bata shirya karbarki yanzun ba" Emily ta kalli Mama Baraka sannan ta kalli Dr AB "Tana da gaskiya, kuma be zama dole ta karbe ni ba, shi kanshi be zama lallai ya karbe ni ba idan ma yana raya" "Yana raye, na kan je na ganshi a duk lokacinda bukatar hakan ta taso, kuma shi mutum ne mai son yara zai yi farinciki dake na tabbata" Emily ta zauna. "Ina son na ganshi, kamanin da ake cewa ina yi da shi ina son na ga ya fuskata take a jikin wani" Dr A-B ya zauna kusa da ita ya ciro wayarsa ya kama hotonshi ya mika mata wayar. Yaran Mama Baraka duk suka fito suka zauna suna kallon Emily. [8/13, 10:39 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 148 · 0% Book details