Sashe 55
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai mu tafi da ke" Sam bata yarda ba, saboda ta san Aliyu be san aikin Vito ba, kuma be san hatsarinsa ba. "Zamu tafi tare, mai gadin ma ba zai bari ka shiga ba" Aliyu ya kalli Tasmia. "Kin iya mota? Ko?" Ta daga mishi kai, sai ya shiga ya dauko makullin wata motar ya bata, shi kuma ya shiga motarsa tare da mai gadinsa, ya rigasu isa gidan amman ya tsaya har sai da Emily ta shiga ciki ta yi ma mai gadin magana sannan Aliyu ya shiga har dakin da London yake ya cire shi a cikin coffin ya saka bedsheet ya lullube shi ya fito da shi Chidimma na ta kallonsa Fatima kam ta dade da yin bachi a lokacin. A gidan suka dawo ya fada a musulumci idan mutum ya rasu ana masa wanka sannan ayi masa sutura ayi masa sallah. Tun a cikin daren Aliyu yayi masa wanka na aje gawarsa a wani dakin na dabam. Tasmia na zaune falo tare da Emily, Tamia ce kawai ta iya angaje Emily kam idonta biyu har safe. Misalin karfe shida da rabi Aliyu yayi waya da wani daga cikin yaran da yake sakawa aiki idan yana bukatar wani abu, suka kawo masa likkafani ya shirya London a ciki sannan ya sauko falon Emily na ta kallonsa ya ce. "Kina son ki ganshi?" Ta daga mishi kai. Sai Tasmia ta hana. "Ba lallai ne ta iya rike kanta ba" Aliyu ya kalli Emily. "Ba zaki ihu ba? Kin yi alkawari?" Ta daga mishi kai. "Shiga ki ganshi, kina da hakkin ganinsa ko a musulunci ana son iyalin mamaci su yi bankwana da shi" Tasmia ta ki shiga Emily kam ta taka ta isa har kofar dakin ta tura ta shiga. Ta hango shi kan tabarma an nade shi da zane ta cikin zanen kuma an masa sutura da farin kyalle wato likkafani. Ta karasa ta zauna kasa inda yake ta bude zagen ta bude likkafani har ta kai ga fuskarsa, tana ta kallonsa. "Mun wahala ni da kai, amman kai ka fini wahala saboda kai baka gane komai a cikin duniya, na dauki cikinka da yunwa da wahala na haife ka daker, kuma sai ka zo ba a lafiyayye ba, ammam a yau komai ya zama labari, rashin farinciki da samuwarka da mahaifinka be yi ba, rashin son sanin kana raye ko a mace yau duk ya zama tarihi, yau an rufe babin rayuwarka Ibraheem, ka tafi kana fushi da ni saboda cutar dake damunka bata barka ka fahimci ina kaunarka ba, kuma zan yi ta kewarka har karshen rayuwata" Ta kai bakinta ta sumbanci goshinsa hawayenta na sauka a fuskarsa. Sannan ta rufe masa fuska ta gyara komai kamar yadda ta tararda shi. Ta taso ya fito daga dakin Aliyu yana ta kallonta har ta iso gurin da yake tsaye, sai ya ji ta burgeshi, a iya saninsa wadanda ba musulmai ba idan aka musu mutuwa ihu suke suna faduwa suna tashi suna burgina da tambayar ubangijinsu Meyasa ya aikata hakan? Amman a gurinta ya ga banbancin haka. Misalin karfe tara yayi waya a gurin aikinsa duk wanda yake musulmi ya saka aka dauko shi aka kawo shi gidansa wasu suka suka zo da kansu, Emily tana tsaye jikin window falon Kameela tana kallo suka yi sahu Aliyu yayi jagoranci yi masa sallah sannan suka dauki gawar yaron suka fita da shi. Ta zauna a falon shiruuuuu tana ta tunani kala kala, Tasmia ta kwantar da ita a kafadarta. Suna haka Aliyu ya dawo tare da mai gadinsa domin sauran mutane daga makabarta suka wuce gurin aiki. Da ya shigo sai ta tambaye shi nawa aka kashe mutanen da ya kira suka yi masa sallah da kuma tafiya kai gawar makabarta ma nawa aka kashe. Yayi murmushi yana kallonta. "Mu a musulunci idan aka yi ma gawa sallah kana da lada mai yawa balle kuma ace ka raka gawa zuwa gidanta na gaskiya, ladar suke kwadayi ba biya ake ba, abubuwan da aka siya kuma ni na dauke ladar" "Na yi zatona akan daidai, kai kadai ne namiji mutumen kirki musulmi, na gade Aliyu" "Ina rokon Allah yasa ki samu musulmai fiye da yadda kike kyautata min zato, Allah ya sanyaya zuciyarki Aisha" Tasmia ta amsa da Ameen tana jin dadin abun da Aliyu yayi har cikin ranta ta ji ya burgeta. Emily ta kalleta. "Ban takura ki ba idan na biki zuwa gidanki?" "Aa babu takura haba Emily ni da ke ai mun zama kawaye" Tasmia ta kama hannun Emily suka fice daga falon, kamin su isa gate Aliyu ya iso gurinsu da mota suka shiga ya kai su unguwarsu Tasmia, sannan ya juya ya koma, suna shiga ciki Tasmia ta hada ma Emily ruwan tea Emily ta sha kadan ta kwanta akan gadon Tasmia, tana ta kallon sama hawaye na mata zuba. Misalin karfe biyu na rana Aliyu ya dawo gidan domin babu wayar da zai iya jin Emily kuma yana son ya san halin da take ciki, ya kwankwasa kofar dakin Tasmia ta bude be shigo ba ya tsaya daga bakin kofa. "Na zo na duba Emily" A lokacin Emily ta samu yin bachi dan haka Tasmia ta amsa masa da. "Bachi take, ka shigo ciki" Ya girgiza mata kai ya juya zai wuce Tasmia ta ce. "Karka damu ba zan fadawa Kameela komai ba, ban san a ina kuka hadu ba, ban gama saninta ba, amman alamu na nuna ta sha wahalar rayuwa ina tausayinta sosai" "Wata kila da zaki saurari labarinta da zaki fi tausaya mata sosai, dan Allah ki zama jekadiyar musulunci ki canja rayuwar yarinyar nan tun da har ta yarda da ke" "In Shaa Allah" Ta juya yayi tafiyarsa ta bishi da kallo tana murmushi sai da ta ga zai shiga mota sannan ta rufe kofar gudun kar ya ga tana kallonsa ta koma tana lekensa ta windows. Bayan ya tafi ta dawo falon ta zauna after like 5 minutes ta ji an kwankwasa kofar ta tashi tana mamaki Aliyun ne ya dawo ko kuma wanene. Ta fara lekawa ta hango mutumen da annuri be samu gurin zama a fuskarsa ba, gabanta ya fadi ta matsa baya. "Waye wannan?" Bata samu amsar tambayarta ta aka sake buga kofar dakin. "Waye" Yaki magana sai kwankwasawa yake, sai a lokacin take dana sanin yin magana da tayi domin bata san waye ba gashi ta yi magana ya ji cewar akwai mutum a ciki. "Bude..." Ta juyo ta kalli Emily dake tsaye bakin kofar bedroom dinta. "Wani ne mai kama da marasa imani" "Na san waye bude" Ta bude ta yi baya tana kallon kofar Vito ya turo kofar ya shigo hannunsa daya a aljihu. "Ina tunanin mun kai karshe da ke cewar babu ke babu alaka da kowa? Amman gashi kin tafi gurin wani kato ya rufe danki yanzu kuma kin zo nan, Emily kina manta waye ni ko? Duk wani motsi naki akan idona yake" "Bayan wannan bana da wata kawa ko yar'uwa da nake alaka da ita, dan Allah ka bar min wannan ita kadai" Ta fada ta sigar magiya, ya kalli Tasmia da tuni mararta ta cika da fitsari ya ciro hannunsa ya nuna mata wata yar mitsitsiyar bindiga dake aljihu mai kama da ta wasan yara. "Ki yi taka tsantsan" Tasmia ta zube kasa "Wallahi har taka tsaki da tsakuwa ma sai na yi idan baka son alaka da ita ba zan sake ba, kai ni ban ma santa ba" Ta juya gurin Emily. "Ke na sanki? Kin san ni, ka gani ba mu san juna ba" Sai kuma ta fashe da kuka. "Wallahi ba ni da kowa a garin nan dan Allah ka rufe min asiri, bautar kasa na zo amman idan kace yau na kama hanyar garinmu Wallahi zan tafi..." Vito ya mikawa Hannu. Emily taka ta isa gurin da yake ta rika hannunsa tana kallon Tasmia ya jata suka fice daga falon. Motarsa ya bude mata ta shiga sannan ya shiga yaja motar be zame da ita ko'ina ba sai gidansa. Yana yin fakin ta kalleshi. "Me zamu yi a nan?" "A nan zaki zauna for now" Ya fita ya zaya ya bude mata, fitowarsa ta yi daidai ta fitowar mahaifiyarsa ta nufo inda take. _____________________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/17, 1:00 PM] ABOKIN RAYUWA