Sashe 4
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tuba kika yi, ba wai an haife ki a ciki ba ne, sanin cewar na auri tubabbiya zai zubar min da kima, kuma babu wanda ya san maganar auren nan daga ni sai ke sai Ammy, Ammy kuma bata nan daga ni sai ke ne a nan Allah yana nan, be kamata ka yi min haka ba, be kamata ka wulakanta ni ba, wannan zalinci ne kuma Allah baya son haka Ya dalla min harara. Ke Allah kika sani? Kin san Allah kika tashi cikin kafirci? Karki kuskura ki ce zaki fadi wani abu akan hakan, domin ke baki san komai ba, sallah ki ma ba a fara karba ba, domin ba mai kyau kike yi ba Amman Turhan... Kul... Karki kuskura kiran sunana a nan, karki kuskura nunawa kowa cewar kin san ni, ni ba mijinki ba ne a yanzu, na aureki ne a inda aurenki ya zame min dole, a nan kuma ina da wasu iyalin... *** *** Madan a nan zan tsaya ko ciki za mu shiga Tambayar da direban Taxi din yayi mata ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, hannunta ta saka ta share siraren hawayen da suka zubo mata. Shiga ciki Ya kunna kai kamar yadda ta masa umarni har sai da ya isa gurin da aka tanada domin aje motoci, ta bude motar a hankali ta fita ta dauko kudinsa ta mika masa sannan ta nufi babbar kofar ma'aikatar da mutane suke hada hadar shiga da fita, sosai gabanta ya tsananta faduwa domin abu ne da bata taba yi ba zata fara a yanzu, wato aiki, a yanzu zata yi mu'alama da mutane bayan ta yankewa kanta mu'amala da kowa sai mutumen da shi ne silar dalilinsa take tsaye a yanzu wato Vito. Bata bukatar wani yayi mata iso domin wannan ne karo na uku da ta zo ma'aikatar bayan zuwanta na farko da ta kawo CV ta, sai kuma zuwan da ta yi interview. Third floor ta nufa bayan ta shiga elevator and she pressed the buttom. Kanta ta daga sama tana kallon gurin tare da aje numfashi a hankali, feeling awkward and excited as the same time. Elevator ya rabe biyu ta fita tana kara gyara gashinta, kai tsaye ta nufi office din da aka musu interview ta yi knocking sannan ta tura ta shiga. Wani saurayi ne a ciki da ba zai wuce sa'arta ba, ta dan yi mamaki domin wacan zuwan nata na farko ba shi ta tarar ba, ta gaisa da shi cikin mutunci ta gabatar masa da kanta. Nice to meet you Aisha, a nan an muku interview ne kawai, a hawa na hudu dama dake akwai wani office na farko shi zaki shiga, ki gabatar masa da kanki zai fada miki gurin da office dinki yake Okay na gode Ta juya ta fita har lokacin bata jin sakewa domin yau ne ranarta ta farko kuma abu ne da bata saba ba. A tsanake ta nufi gurin da Elevator ke daf da rufewa mutumen dake ciki yana tsaye yana kallonta ita ma kallonsa take bata dauke ido ba har sai da elevator ta rufe. Tsaye ta yi a gurin tana kallon floor din da kowane office yake rufe. Babu tsammani elevator ta sake budewa mutumen da ta hango dazun a ciki shi ne har yanzu, matsawa ta yi gefe domin ba shi hanya a zatonta fita zai yi, sai ta ga tsabanin haka, be ce ta shigo ba kuma shi ma be fita ba, ganin kofar na kokarin rufewa a karo na biyu ya saka ta yi hanzarin shiga sai ta matsa daga gefe. Kamata yayi ta gode masa? Saboda ita ya sake pressing floor din da take ko kuma dai wani abu zai yi, ya fasa. Ta dan dago ta kalleshi kadan sai ta ga idonsa yana kanta ta yi hanzari dauke kai. Okay Momy zan yi, i love you Ta ji ya fada sannan ya kai hannu ya taba black iPod din dake kunnensa. Da sauri ta dube shi jin ya ambaci uwa, a duk gurin da mutun yake tare da mahaifiyarsa ko ta ji ya ambace ta, ko kuma ta yi arba da alakar uwa da da, sai hankalinta ya tashi, sai ta ji wani abu ya tsaya a zuciyarta, domin ita bata san wannan gatan ba, bata san mutum daya a duniyar da zata nuna a matsayin dan'uwanta na jini ba balle kuma uwa. Ita din wane laifi ta yi ma iyayenta suka jefar da ita a gidan marayu? Su waye iyayenta? Wane addini suke yi? Wane yare suke ji? Ita ce tambayar da take yawan yi ma kanta. Excuse me, can i help you? Ashe kallonsa take da kyakkyawan blue eyes dinta masu matukar daukar hankalin mai kallonsu. Blue eyes din ne suka karafafa masa guiwar kallonsa har yake jin kamar ta taba wanzuwa a wani bangare na rayuwarta ta baya, wata kila kuma kyauta ne yake masa gizo har yake ganin haka, but this is the second time da yayi arba da mace mai blue eyes a Africa. No, I'm sorry Be sake ce mata komai ba, sai dai har lokacin kallonta yake ta gafen ido, ita din ai ta kai ayi mata kallo fiye da goma ma, ba daya ko biyu ba, but wait ina ilminsa da tarbiyarsa da koyarwar addininsa suka tafi? A take yayi hanzarin dauke idonsa gaba daya daga barin kallon abun da ba halalinsa ba. Astagafullah Ya furta a ransa a daidai lokacin da elevator ya bude a hawa na hudu, ta dan kalleshi tana jiran ya fara fita sai ta ga be fita ba sai danna Apple watch dinsa yake, hakan ya saka ta fita cikin rashin sakewa ta fara tafiya. Sai a lokacin ya dago mistakenly idanuwansa suka sauka bayanta, sai ya rufe ido da sauri ya taba numbers din da suke jikin Elevator a take ya rufe yayi sama da shi to 5 floor. Office din farko ta fara murdawa kamar yadda aka fada mata ta tura ta shiga. Ya san ko dai ta tsaya a 4 flour ko kuma kasa zata koma, domin ma'aikatan kamfaninsa basa wuce 4 Flour the 5th floor is his and his entire team, and be taba ganin fuskarta a kamfanin ba, maybe she's among the new employees ko kuma ta zo gurin wani ne, ko dai minene she should be tsakanin fourth to first floor. Sai ta samu kanta a babban guri da wasu dakunan a rufe, da dan tsoro irin na rashin sabo ta tura kofar Office din da shi ne farko ta shiga ba tare da ta yi knocking ba. Matar dake sanye da abaya da karamin hijab half sunna, tana amsa wayar telephone ta dago tana kallonta fuska babu annuri. Emily ta tsaya a gurin gabanta na faduwa zuciyarta na tsanar matar da ko sunanta bata sani ba a yanzu, ba dan komai ba sai dan shigar ta wato suturar jikinta ta isar da sakon addininta ga duk wanda yayi ko zai yi arba da ita. Ta tsaya a gurin har sai da ta gama amsa wayar, sannan ta karasa kusa da ita. Am... Sunana Aisha Muhammad ina daya daga cikin sabin ma'aikatan da aka dauka, kuma yau ne zuwana na farko, a office din da aka mana interview yace na shigo nan Ta fada cikin sakin fuska da murmushi, sai matar ta kara hade rai ta jefa mata wani kallo. Amman dai baki manners, ta ya zaki shigo cikin office ba tare da knocking ba? Kuma a farkon Shigowarki ai ya kamata ki tsaya sai an miki izini tukuna Emily ta sassauta murmushinta tana dan ji babu dadi, matar dake gabanta ba san yadda Vito ya jikata da gata ba, wata kila da bata fada mata magana irin wannan ba. Ki yi hakuri, mantawa na yi Koma ki yi knocking idan na miki izini sannan ki shigo Ta fada kai tsaye tana bude wasu files dake gabanta, Emily ta tsaya kallonta like are you serious right now? Ganin hakan ya saka matar ta sake duban Emily. Kurma ce ke? Ta amsa sannan ta juya jiki ba kwari ta fice daga office din. Taja tsaki after Emily ta fice. Mtswwww, na ga Aisha Muhammad na dauka ke kadai ce Musulma a cikin sabin da aka dauka, ina cewa zan samu yar'uwa ashe kafirar ce, irinsu ne ke batawa musulmi suna, suna aikata abu ace musulmai ne, sunan mahaifinta da nata na musulmai amman fuskar kafirai da sarkar Cross a wuya, na tsani kafiran nan Wallahi Sai fada take kamar zata yi duka, abu ne da ta boye a zuciyarta saboda mu'amalarta da mutanen da suke garin Port Harcourt da kuma kamfanin mafiyawancinsu kistoci ne, amman bata kaunarsu ko kadan. Na riga na zabe ki, na dauka Musulma ce Wallahi, amman zaki ci ubanki Ta fada tana dora hannunta a laptop din dake gabanta. Emily na fita kai tsaye ta nufi gurin Elevator yake a fusace domin ta manta when last a wulakanta, kusan wani be taba gwada yi ma makamancin wannan wulakancin ba a sabuwar rayuwarta ta yanzu. Kamin ta karasa wayarta ta yi kara sai ta saka hannu a jaka ta ciro wayar, ganin sunan dake jikin screen din ya saka ta tsaya ta daidai numfashinta, ta sani idan har ta amsa wayar a cikin yanayin da take a yanzu na bacin rai zai ji haka a muryarta zai iya tashin building din ba tare da tsayawa ya ji dalilin bacin ran ba. Hello Emily miyasa baki fita da motarki ba? V, idan na dawo za mu yi magana Ta fada a daidai lokacin da ta dora hannunta Elevator zata danna. Answer me...!!! Ya daka mata tsawa har sai da zuciyarta ta yi rawa, and yes this is not the first time da yake tsawa, ya saba dukanta ko ya takata ko ya yi mata fada ko raunatata but shi kadai zai iya mata haka, idan wanin da ba shi ba yayi mata kallon banza sai ya saka an cire masa ido. Ta kashe wayar da sauri tana maida numfashi da karfi, rauni da damuwa irin na wanda ya rasa madafa suka bayyana a fuskarta. Dauke hannunta ta yi ba tare da ta taba ba, ta juyo ta nufi office