Sashe 10
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
zaki ce kin san halin maza? Kai kadai na aura amman ai ana fadar halinku Ni dai na banbanta da sauran, yanzu wanda yake da mace yar dumaduma irinki har wata zata burge shi? Ya fada bayana bin bayan kiran da aka masa. Hello Allah ya taimaki Yarima Daga dayan gefen Turhan yayi murmushin karfin hali. Tsokanar ta tashi kenan, ya gida? Lafiya kalau Sorry na kira late na san kana tare da Madan ko? Aliyu ya kalli uwargidansa yana murmushi Kamar ka sani kuwa, daker ta bar ni na amsa wayar ma To a bata hakuri, wani uzurin ne ya taso min... Turhan ya shimfida masa kudurinsa sannan ya bijiro masa da bukatarsa. Aliyu ya dan sosa kansa. Akwai wandanda zan hada ka da su ba ma daya ba, amman Turhan kana ganin nemanta abu ne mai sauki? Ni ma fa na saka anbincika maka lokacin da na yi zama a Lagos din nan amman ba a dace ba Wannan karon ina son na bi gidajen marayun da yake cikin garin Lagos ne, na bincika ko zan dace Eh toh kuma ka kawo shawara, amman duk da haka ina ganin zai yi wahala saboda an kwana biyu, kuma ka fada min tun tana karama aka yi rikonta a can, kuma ba lallai ne ka sami ma'aikatan gurin na da ace su ne har yanzu? Yeah amman ina zaton indai sun santa sosai da sosai za su gane ta idan na bada misalinta wata kila za a dace Dama dai kana da hotonta abun zai fi sauki Haka din ma zan gwada wata kila a dace, ina tunanin duk wanda na fadawa sifofinta blue eyes red hair, fara mai kiba sosai zai gane ta matukar ya santa Allah yasa a dace, zan yi magana da wani yarona da yake can da safe sai na hada ku Okay thank you Ya aje wayar ya sake zaunawa kusa da matarsa, wannan karon sai ta tashi zaune tana kallonsa. Kyakkyawana Hmmm Ya amsata yana wani tunanin na dabam, har idonsa suna motsawa, sai kuma ya tabe baki zuciyarsa na raya masa abun da be isa ya fada a gaban matarsa mai tsananin kishi ba. Kana ji na Ya aje wayar ya mika mata hankalinsa gaba daya. Ina jinki Sarauniyata So nake ka yi min wani alkawari Na me? Ta yi shiru na wani lokaci kamar mai nauyi fada sai kallonsa take tana nokewa kamar marar gaskiya. Na miki alkawari cewar ba zan kara aure ba bayan ke? Ta daga masa kai tana mamakin yadda yayi saurin lagonta. Eh ya aka yi ka gane me nake son fada? Na sanki da kishi ne ai, zuciyarki zata raya miki idan na fita waje mata nake kulawa ko? Na san ba halinka ba ne, ba zaka kula mata ba, amman su matan za su iya kawo maka hari kuma zuciya bata da kashi, kuma ni gaskiya ba zan iya sharing dinka da kowa ba Yayi murmushi ya shafa fuskarta. Saka ranki a inuwa, Aliyu na ki ne ke kadai daga ke babu kari babu wanda zata kawo hari na rufe kofa, na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba Ta bude ido tana mamakin yadda yayi hanzarin bata hadin kai da wuri haka, ko da yake ta san waye mijinta ba mutum ne mai son mata ba, kuma ya sha fada mata tun kamin ya aureta cewar shi ba shi da ra'ayin aure mace sama da daya. ______________ Anya Aliyu zai rike alkawarin nan kuwa? Turhan zai samu ganin Aisha kuwa? Wane irin so Vito yake yi ma Emily? Meyasa Emily ta dage sai ta yi aiki? Bayan duk gatan da ta samu a gurin Vito? [4/20, 9:58 AM] ABOKIN RAYUWA