← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 177

Sashe 150

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da Aliyu? Idan ma dafa shi zata yi ta ci ai sai ta yi" Anty Shafa ta fada, Kameela ta kalleta a fusa. "Aliyu mijjna ne, kina tambayar alaka ta da shi? Duk ba ku kika kashe min auren ba? Kullum mijina yana cikin bakinku cin mutunci babu wanda baku masa, idan ku ba ku san shi ni ina son mijina, yanzu ai gashi nan ya sake ni" "Uban waye ya aikeki saka masa guba a abinci? Ke ba dan ya sake ki ya kyale ki ba ai da yanzu ma gidan yari za a kaiki, karyar banza karyar wofi har ke fada mana wani wai kina son shi, kina son shi kika tashi kasheshi? Ko kina son shi kike daukar sirrinki ki kaiwa Bakar Mama Baraka? Yanzu wa gari ya waya?" Anty Shafa ta maida mata da martani. "Idan ban tafi da damuwata gurin Mama Baraka ba ina zan je? Saurarata kuke yi? Burinku Aliyu ya sake ni kuma ya sake ni, ita kuma zata dauki bakar kafirar yarta ta aura masa ai" Hajiya ta daka musu tsawa. "Miye haka wai? Sai yayanta sun kwashe komai sun fada mata an dawo amana mana dariya? Ke kuma Aliyu autan maza ne da zaki zauna kina fadawa yar'uwa ki magana saboda ya sake ki? Ke daga kin auna arziki ma baki haihu da shi ba? Nan da kwana biyu zaki shige wani gidan, daman can Aliyu ba sa'ar auren ki ba ne, manyan mutane suke sonki kika nace sai shi waya sani ma ko ba banxa ya barki ba? an makiyinmu kika dage sai kin aura kuma kika aura uwarsa ta mana cin mutunci" Kameela ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki a fusace. Turhan da ya shiga motar ya dauki hanyar gida, yana jin farinciki sosai domin Emily bata taba sake masa haka ba and he feel something special about her today. "Ina son Emily ba ki sani ba ne, na yi farin ciki kin samu family a yanzu, kuma na miki alkawari idan kika ba ni dama ta biyu ba zaki yi nadama ba, zan maida ke sarauniya zan baki gatan da ba a taba baki ba, ke kika fara dandanin dadin zama uba, ke kika fara saka ni wannan farinciki, kuma kika yarda kika aure ni saboda Ammy, na yi kuskure na sani, amman yanzu na miki alkawari zan jiyar da ke dadi na wadata ki da komai zan ninka miki farinciki fiye da wanda kika sani, shiyasa na yi alkawarin zan yi hakuri zan jira har ki aminta da ni, kalli yadda kike da kyau da shiga rai, kika ba ni a mai kamanina, to me kuma zan nema a gurinki? Sai dai ni na nemi saka miki, ina son komai naki Emily ina son duk wani abu daya shafe ki, zan kaiki inda ban taba kaiki ba, zan siya miki tufafi mai tsada, zan rumgume ki na nuna miki yadda nake kaunarki na baki kulawa" Yana tuki da hannu daya dayan hannunsa kuma yama shafa kansa yana magana da kansa sai murmushi yake kai kace Emily ce kadai matar da ta rage masa a duniya. Ya isa gidansu tun kamin ya faka motarsa harabar gidan Ammy ya fahimci akwai baki a gidan domin yayi arba da manyan motoci da be tantance na waye ba. Ya faka motar ya fito yana kallon motocin ya tun kari kofar falon, sai kamshin turaren masarautarsu ya tunkari hancinsa. Ya tura kofar da hanzari ya shiga, dogaran da ya fara arba da su suka saka shi fadada murmushinsa, ya kai tsakiyar falon yana jin wata madarar dadi sakamakon arba da yayi da mahaifinsa zaune a falon na Ammy. EMILY POV. "Na ga nadama sosai a gurin mutumen nan, kuma na jidadi da kika yafe masa, kuna da a a tsakaninku ya kamata ace kun fahimci juna" Emily dai ta yi shiru bata ce komai ba sai kallon titi take. "Duk inda namiji ya kai, Mutumen nan ya kai, kuma na tabbatar yayi nadama tun da har yake bibiyarki, wata kila baki san komai akan sarauta ba, amman dai samun dan sarki babban mutum kamarsa yana zubar da kai kasa da neman yafiya abu ne da ba a saba gani ba, shiyasa na yarda da nadamarsa, kuma dukanmu muna kuskure, turawa suka ce the devil you know is better than the angel you don't know, ina son ki san babu mai cilasta ki yi komai, amman dai ki yi a hankali, kar wani ya sake breaking heart dinki" "Turhan ya fada maka wani abu akan abokinsa ne?" Dr A-B yayi murmushi "Ya fada min yadda abokinsa ya ci amanarsa kuma yayi rawa yayi tsaki wajen ganin baki saurare shi ba, bayan wannan be fada min komai ba, ina miki wani furuci ne saboda ina hararo wani abu na dabam, kuma na san yadda halinmu maza yake ai, ki yi taka tsantsan" "Aliyu ba kamar sauran mazan da na hadu da su ba ne, a rayuwa ban taba haduwa da wani mutum mai rikon addini da gujewa tsaba addininsa ba kamar Aliyu, yana da amana, adan karamin lokacin da muka san juna da shi sosai na fahimci mutum ne mai kyaun hali ya nuna min kula, ba tare da duban addinina ba, ko Vito da ya maida ni yadda nake ya maida ni ne saboda na yarda na bar addinin musulunci na dawo nasa, amman Aliyu be taba duba wannan ba, ko a lokacin da ya taimake ni be san wacece ni ba, ya bi ni har a gidanku saboda ya damu ya san halin da nake ciki a lokacin da ban yi tunanin akwai wanda zai da mu da ni ba" "You trust him ko ba haka ba?" Dr A-B ya tambaya da murmushi a fuskarsa. "1,000%" Ta fada ba tare da fargaba ba. "Kin yarda da shi saboda wasu abubuwa da kike jin kin gamsu da su, hakan yana da kyau, amman dai duk da haka ki yi hankali" "Dukanku ba ku fahimce ni ba ne, Aliyu ba so na yake ba, ni ma ba son shi nake ba, ni ban shirya soyayya ba, ba a yanzu ba ko a nan gaba" "Time will tell, amman dai idan lokacin yayi ina fatan wani ne wanda na sani" Ya nuna agogon hannunsa sannan ya bude motar ya fita, ita ma ta fita, ta raka shi har ciki sai da zai shiga jirgin sannan yayi mata side hug. "Ki kula da kanki, a yanzu ina tunanin babu wata damuwa a tare da ke, idan ma akwai wani abun da kike so ko kike neman taimako ki sanar da ni" "Na gode sosai na jidadin da kake nuna min kulawa" "Always, idan komai ya laba abubuwa suka tafi daidai zan gabatar da ke a gurin Daddy, babanki mai kudi ne yarinya zaki shakata... Na gode da kika karbe ni a matsayin dan'uwanki na yi farin ciki da hakan" Ta yi murmushi tana kallonsa "Bye Sis" "Bye Bro" Ya juya zat tafi sai ta rumgume shi tana kuka, ya juyo ya rumgumeta yana murmushi, ta sake shi ya share mata hawayenta, sannan ya daga ma Mama Baraka hannu ya wuce. Emily ta juya ta nufi gurin da su Mama Baraka suke tsaye ta tsaya gaban mahaifiyarta tana kallonta Mama Baraka ta kasa tsayar da idonta guri daya saboda kunyar Emily take ji. Emily ta rumgumeta ta ji sanyi a ranta a yanzu tana da mutanen da zata kira da sunan yan'uwanta na jini. Mama Baraka sai hawaye ya sauko mata ya rumgume Emily kamkam ta lumshe ido. Misra ta kai hannu tana shafa bayan Emily tana murmushi. Motar Mama Baraka Emily ta biyo, Mama Baraka ta tuka ta har gidansu Ummi tana jin kamar ace za ta iya ta roke ta ta kwana a gidanta, amman ta kasa, daman kuma Emily ta fada cewar tafi son zama a gidan Ummi. [8/16, 8:57 AM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 150 · 0% Book details