← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 177

Sashe 47

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 2 Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku. Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi. Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa suka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace. "Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?" "Eh" Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da korafina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da yake yawan yi min. A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban san mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta sai ranar. Yace da abincinta ta zo da komai nata, kuma wai bana masa biyayya abu kadan zan fara cewa ba shi da adalci ina masa ihu da Allah ya isa. Iyayensa ma suka goya masa baya mai garin ya rufe ni da fada. "Ke mu fa irin tarbiyar da kuke a can ta arna ba ita muke a nan ba, tun da har kin yi aure kuma kin musulunta ya kamata ki watsar da wannan dabi'ar" Mahaifiyarsa tace "Ai matsalar auren tun farko bata san musulunci ba ko kuma bata tashi a cikinsa kenan, su fa tarbiyar su da auratayyarsu dabam take, musulunci ma ai suna yi ne kawai a baki" Mai gari ya fadi nasa iyayensa da shi kansa su fadi na su, na rasa ya zan yi sai kuka nake ina bashi hakuri. Da muka dawo gida sai ya fara dukana irin dukam da be taba min ba, dukan da zaka rantse dansa na kashi ko na aikata wani criminal abu, ina bashi hakuri yana duka wai abun nawa ya wuce ina fada a makota cewar yana bari na yunwa da sirrin gidansa ya kai har na dauki kararsa na kai gurin mai gari a nemi tozartashi. Duka yayi min ba na wasa ba, yana dukan yana min gorin wai daga ya taimaka ya tsamoni daga wuta da yanzu idan na mutu wuta zan tafi. "Iyayenki ma suna can cikin azaba, saboda sun yi shirka da Allah, kuma Allah kadai ya san ta hanyar da aka same ki, shiyasa kike butulu, matar ma data rike ki yanzu ai gudowa kika yi kika barta, ni kuma na dauko ki na musuluntar da ke na aureki amman kina min butulci, idan ba ni ba wane namiji ne zai auri arniya ya kuma ba a kawo ta da komai ba, marar asali ma irinki" A lokacin ne kalamansa suka fi yi min zafi da daci fiye da dukan da yayi min, na ji kamar ace ina da ikon da zan zare numfashi daga jikina na manta da kowa da komai. A daren na sha kuka washe gari na dora haka na kwashe kwana uku bana iya komai sai kuka. Abun da ban sani ba be sani ba shi ne, ashe lokacin da ya doke ni ina dauke da cikin dansa, shi be sani ba saboda ba nice a gabansa ba, ni kuma tunani da tashin hankali da nake ciki be bar ni na ankara ba, daukewar da al'ada ta yi min na tsawon wata hudu ban gane ba saboda hankalin ba nan yake ba, gashi kuma cikin fari ne ban san komai akan ciki ko haihuwa ba, domin a gidan marayun da muke zaune ban da karatu da sana'a ban maida hankali gurin koyon komai ba ko kuma sanin wani abu wai shi ciki da haihuwa. Sai da ciki ya kai wata biyar sannan na gane cewar ina da ciki shi ma Malika ce ta fada min. "Wata nawa ne Aisha" "Ni ban sani ba, ni na dauka ko yunwar da nake fama da shi ne ya janyo cikina yayi girma" Ta yi dariya. "Kai Aisha kina da wauta, ga abu har ya fito yaushe rabon da ganin al'adarki?" Na tsaya tunani ni kam bana ma iya tunawa. Ta bani shawarwarin yadda zan yi kuma ta fada min na tafi asibiti. Na dawo gida ina ta murna da dare da Khaleefa ya shigo na masa maganar sai yace min ai ya sani, shi mahaukaci ne da ba zai gane ba. Na yi mamaki ya gane amman be taba min maganar ba kuma be nuna min komai ba? Da na masa maganar zuwa asibiti sai yace shi ba shi da kudi yanzu na bari sai gaba idan ya samu kudi. Ma zan yi a lokacin idan ba hakuri ba, na san ba dan ba shi da kudin ba, domin yana cikin shirye shiryen bude shago a kusa da gida ne, idan kuwa ba shi da kudi ba zai bude ba, nice ba ya son kashewa kudin, sai na bawa zuciyata hakuri na saka masa ido, na jidadi samun ciki domin ya dauke min damuwa sosai ban sani ba ko dan saboda ina da son yara ne ko kuwa dai saboda ina kurciya ne, wata kila kuma saboda ina jin cewa zan samu iyali ne, ma'ana dai zan samu dan'uwa na jini daga gareni. Kusan sai ya dauke min rabin damuwa da tunanin da nake idan na ji motsinsa sai farinciki ya baibaiye ni. Ina cikin wata na shida ne da ciki, na ji yan'uwansa suna shelar Amaryarsa Hindu tana da ciki, shi kansa na lura da farincikin da yake da cikin, amman a nawa shi da yan'uwansa ba su nuna min jindadinsu ba kamar wanda zata haihuwa ba da igiyar aure ba, ashe wai kallon suke wata rana zan iya komawa kafira saboda iyayena da asalina ba na musulunci ba ne tun farko, kuma zan iya komawa da rayana, kusan a lokacin zamana a gidan da kuma aurena kamar ya zamewa Khaleefa dole ne. Wallahi akwai zafi akwai ciwo, ka ga mijinka yana zumudin zuwan wasu yara amman ban da naka, bayan wankin da nake na siyarwa da ya dauke me sakamakon abincin da Mahaifiyarsa ta dawo tana ba ni a kullum babu wani abu da Khaleefa yake min, ko dan siya min wani abun kwadayi babu ruwansa. Ashi ma kwadayi mace mai ciki guri yake samu, domin ba kasafai nake jinsa ba, idan ma naji sai dai na yi hakuri ko kuma na tafi makota gurin Malika na samu idan tana ta ba ni. Amaryarsa ita take girkinta a ranar girkinta ni kuma aka fashe da cewar ban iya girki ba sai idan mahaifiyarsa ta girka ta ba ni. Da cikina ya shiga wata na bakwai sai na fara rashin lafiya da amai domin ban yi laulayi a farkon cikin ba, da na masa maganar tafiya asibiti sai yace min na bari sai wani sati. Haka kuwa na hakura na zubawa sarautar Allah ido. Wata ranar jumma'ah gidan babu kowa sun tafi bikin yan'uwa mazan musu wasu sun fita wasu kuma sun tafi masallaci, ina zaune cikin dakina bayan sallah la'asar daya daga cikin matan gidan da bana magana da ita saboda yadda suka hade min kai. Sai gata a dakina da sallamarta na amsa ina kallonta sai ya duka ta ce. "Aisha, na zauna na yi nazari abun da ake miki a gidan nan an zalince ki, ki yi hakuri ki yafe min, ban gane ba sai da kika samu cikin nan, kalli yadda ake farinciki da cikin Hindu amman ke kamar kin kumsa cikin shege, kuma Hindu tana zuwa asibiti amman ke baki zuwa" Ta kowance gefen zagenta ya ciro kudi yan dari biyu da naira dari ta miko min. "Ungo wannan duku uku ne, ki shirya ki tafi asibiti a duba lafiyarki da abun da yake cikin ki" Na saka hannu biyu na karba na mata godiya sai ta gargade ni akan kar na fada ma kowa, ta miko min takardar da number waya a rubuce. "Kin ga number wayata, idan kina son magana da ni ki tafi wani guri ko makota sai ki kira ni ki tambaya, kin ga ba zai yiyu mu yi magana da juna idan Inna na nan ba, sai mijinki da ita kanta Inna da sauran jama'ar gida su ce na yi munafurci, amman idan kika fita makota kika ari waya sai ki kira mu yi magana ba san mun yi ba, amman ba karki bari a gane da ni kike waya" "Toh na gode" "ba komai Allah ya saukeki lafiya" "Ameen" Ta fita ni kuma na boye kudin, washe gari ban ma fada masa zan tafi asibiti ba saboda gudun kar ya hanani ko yace na bari sai lokaci kaza, domin ina jin rashin lafiya a lokacin, sai na shirya na fita ba tare da na fadawa kowa inda zan je ba, a tunaninsu na shiga makota ne. Kuma tabbas na shiga amman gidansu Malika na tambaye ta wace asibiti ce mai saukin kudi domin dubu uku ne da ni ina son na je, sai ta fada min na kama hanya na tari achaba na tafi, duk abubuwan da ake bukata na yi da na shiga ganin likita sai ta yi ta fada wai miyasa ban zo awo da wuri ba gani yarinya kuma haihuwar fari, ai yanzu
Chapter 47 · 0% Book details