← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 177

Sashe 101

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

you about this, ko ba komai ke fa mace ce kuma uwa, idan ma baki duba duk wannan ba why not ki girmamani kamar yadda kike yi a wacan karon ki saka tufafi masu kima? And baki fada min matsayin wannan Likitan a gurinki ba har kika karasa labarinki" "Ba shi da wani muhimmanci a gurina wannan ne haduwata da shi ta uku" "Me ya same ki a fuska" Bata amsa masa ba ta ce. "Tafiyar ta gaggawa ce shiyasa ban yi tunanin saka wani kayan ba, ma tsorata ne na yi tunanin... I'm sorry ka fahimce ni please, ka san halin da na shiga ba wai ina nufin ban yarda da kai ba amman hankali zai fi kwanciya idan Fatima tana kusa da ni, na zo na dauke ta ne sai mu koma gobe dan Allah karka min rashin fahimta" Ya motsa bakinsa a hankali har wani iri yake ji saboda yadda ta marairaice murya da fuska tana masa magana sai ya dorawa kansa laifin tayar mata da hankali na tafiya da yarta ba tare da amincewarta ba. "Ma fahimta, shiga mota mu tafi" Ya bude bangaren da yake tsaye ta zagaya ta shiga baya ta zauna gudun kar ayi masa mummunar fahimta domin ta fahimci shi din mutum ne mai mutunci kuma kai addinin. Be ce me yasa kika zauna a baya ba yaja motar suka fara tafiya be yi nisa ba ya samu kansa ta saita madubin gaban motar zuwa saitin da Emily take zaune a baya ba dan komai ba sai dan yana son karantar yanayin da take ciki, jikinsa na bashi wannan kwancin jinin dake fuskarta dukanta Vito yayi ko kuma wani abu ya faru tsakaninta da Dr A-B din ne, waya sani ma ko Vito ne ya cilasta mata zuwa ta tafi da Fatima, sai tausayinta ya kara kamashi, mutanen da babu zumuntar nesa ko ta kusa suna ta juyata yadda suke so saboda rashin dangi da wanda zai tsaya mata. "Shi likitan yayi kokarin taba mutuncinki ne?" "Aa" Ta amsa tana kallon titi. "Ba zaki fada min abun da ya sami fuskarki ba?" "Duka ne" Tun da ta amsa da duka ne ya fahimci wanda yayi mata dukan ba sai ta fada ba. "Saboda na taho da Fatima ne?" "Ba yau ba ne tun wacan ranar ne da na saka Abaya" "Shiyasa kika hana na ganki? Karya Tasmia ta min kenan?" Ta yi shiru idonta na cika da hawaye ta share, be sake cewa komai ba ya cigaba da tukin har ya iso gida yayi horn mai gadin ya bude masa ya shiga ya faka motar harabar gidan ya fito, Emily kuma ta zauna domin bata san su waye a gidan ba kuma be ce ta fito ba. Zagayawa yayi bangaren da take ya bude kofar bayan ya bar kofar a bude ba tare da yace mata komai ba. Tana ganin haka sai ta sako kafafuwanta kasa ta fito tana rike da jacket din. "Na taho?" Ta tambaya kamar mai jin tsoro, Aliyu ya juyo ya kalleta ya girgiza mata kai. "Bari na daukota" Ya shiga ciki ita kuma ta tsaya a gurin ta rumgume hannayenta, ba a dauki lokaci ba ta ga ya fito da sauri ya nufi gurin mai gadi. "Malam Tahir ka ga wata karamar yarinya ta fito nan waje?" "Eh sun fita ita da Hajiya, ba su ma wani jima sosai ba Hajiya ta zo da mota ta dauke ta suka fita" "Hajiya? Wace Hajiya? " Hajiya ta gidan nan" "Kameela" "Eh ranka ya dade" "Me ya faru" Emily ta tambaya tana karasowa inda suke tsaye. Aliyu be ce mata komai ba yayi hanzarin ciro wayarsa aljihu ya kira Kameela kusan 3 missed call bata daga ko daya ba. "Ina Fatima? Ni fa ban gane ba" Ta tambaya hankali a tashe "Kameela ta dauke ta" "Kamar ya Aliyu karka min haka idan ma wasa kake dan Allah ka daina ba haka muka yi da kai ba ina yata take?" Bata tsaya jiran amsarsa ba ta nufi kofar falon ta shiga da gudu. Aliyu kuma ya bude motar sa a fusace ya shiga yana jan numfashi da karfi ya dauki hanyar gidansu Kameela. Emily ta duba duk inda zata iya na falon domin ba wani sanin gidan ta yi ba, ta kalawa Fatima kira shiru ta shiga har dakunan data gani ta duba bata ta ga Fatima ba ta sauko tana kiranta bata ji ta ba. Da wayar dake hannunta ta yi amfani ta kira layin Aliyu na farkon wanda ta kira da shi dazun har Fatima ta daga. Kiran ya shiga yana bugawa tare da bugun zuciyarta. "Hello Fatima my baby girl where are you?" Shiru ba'ace komai ba. "Hello Baby Girl talk to me, ina kike?" Shiru ba'ace komai ba. Ta yi zaton Kameela ce dan haka ta fara magana cikin kaushin halshe. "If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki" "Your Baby is in safe hands..... Aisha... Emily..." Ta ji an fada cikin wani sauti mai kamar rada kamar rarrashi, da wata murya da bata fatan sake jin irinta, dip bugun zuciyarta ta tsaya wayar ta subuce tsakanin hannunta da kunnenta ta fadi kasa... _________________ Na biya bashin jiya kuma na yi long page Kar inji wani yace Pim.... [7/4, 5:08 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA
Chapter 101 · 0% Book details