Sashe 147
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 "Idan Hajiya Baraka ta yarda mun tafi dake kuma Ammy ta amince toh wannan makarantar ya kamata a sakata, daman ina jin ana fadar suna karatu sosai" Emily ta yi murmushi kadan. "Na manta ban tambaye ki ba, ko kina zuwa coci a lokacin da kike can? Kar ya zama mun tauye ki a nan ki kasa mana magana" Emily ta kalli Ummi ta mamaki. "Aa bana zuwa coci ko a can" "Okay, tohm yayi kyau, idan kin gama kallon sai ki shiga Kitchen ki wanke kayan da muka ci abinci da su, zan shiga na kwanta" Ummi ta mike tsaye ta nufi hanyar Stairs, Emily ta bita da kallo tana murmushi, sosai take jindadin yadda Ummi take daukarka kamar wata wanda ta dade a gidan ba bakuwa ba, akwai mai aiki da Ummi zata iya sakawa ta yi wanke amman ta zabi ta sakata haka ya faranta mata rai, haka take mata idan za a jera abinci ko a kwashe kayan ita da Nafeesa suke kwashe, su kai Kitchen. Ummi na haurawa sama Emily ta tashi ta shiga kitchen ta fara hada kayan ta daurayewa kamin ta saka kumfa. Tana tsaka da wanke wanken ta ji muryar Aliyu ya shigo falon da sallama, duk yadda take zumudi da marmarin ganinsa bata aje ta fita falon ba, har sai da ya leko Kitchen din yana zaton Ummi ce a ciki, don ya san halin Ummi ba girkin kowa take ci ba, haka kuma bata yarda kowa yayi ma mijinta girki ba sai ita. Ta juyo ta kalleshi suka hada ido, sai suka sakarwar juna silent smile mai laushi. "Barka da zuwa" "Barka da aiki" "Kusan sati baka zo gidan nan ba" "Kirgawa kike yi?" "Har da mintunan da dakikun na sani" Ta amsa a nutse cikin sanyi hali mai shiga rai. Ya fadada Murmushinsa. "Na dan tsaya na huta ne, kusan tun da kika bata ban samu wadataccen huta da bachi ba, shiyasa yanzu nake ranko, kuma akwai guraren da ya kamata na leka sai a yanzu nake samun dama, and you need space too, bana son wani bacin rai ya samu zuciyarki a yanzu" "A space? Space din da zai karantar da ni yadda kewarka take? Ya zabtar da idona da kaikayin ganinka? Nisanta kamar hukunta ni ne Aliyu" "Kina ta siye ni da kalamai, ala dole so kike na ji cewar ban kyauta ba" Ta wanke cup ta dauraye. "Da kalamai suna siye mutum, da ka dade da karbar kudina, ina fada maka abun da yake zahiri ne kuma nake ji, ba wai ina kokarin wuce gona da iri ba ne, ina jinka kamar wani an'uwana na jini" Ya hade yawu yadda take maganar softly and calmly ya saka kara jin tausayinta, a kokarinsa na canja maganar ya dauko wata maganar. "Har yanzu lokaci be yi ba da ya kamata ki fara rufe gashinki Emily? Shi ma fa ba muharramina ba ne" "Gashin?" "Uhmm..." "Ina jin sakewa idan ban saka dankwali ba saboda na saba" "Ni kuma zan fi sakewa idan kika saka" Ya cire black facing cap din dake kansw ya jefa mata ta chabe, ta saka a saka a kanta da ta juyo ta kalleshi sai da gabansa ya fadi saboda yadda ta yi maya kyau ga wani lafiyayyen murmushi dake fuskarta. Fa sauri ya dauke idonsa ya juya zai fita. "Aliyu zan iya samu ayi min welcome back din layina?" Ya juyo. "Yeah amman yanzu? Ba sai gaba ba?" "Saboda Vito ne..." Aliyu ya jingina da kofar dakin ya rungume hannayensa. "Vito... Ba wanda ya san inda yake for now, ya boya inda babu wanda ya sani, saboda an tattara duk wani laifi da ya kamata a tattara a kama shi da shi, tun daga kan abun da muke zaton yayi min da kuma sana'arsa, yanzu haka neman sa ake ruwa a jallo, shi ne dalilin daya saka Ummi bata son na koma aiki har sai an kama shi, kuma Daddy ya fada min ana yin duk abin da ya kamata" Fuskar Emily ta sauya. "Idan aka kamashi kashe shi za'ayi?" "Ko dai ba a kashe shi ba, to za a daure shi a gidan yare ne, ba kuma saboda ni kadai ba har saboda ke" "Idan kuma yace ya tuba fa?" "Irinsu suna da wuyar tuba Emily, kuma suna da wuyar sha'ani mai shaye shaye tunaninsa ba daya yake da na sauran mutane ba, haka kuma zuciyarsa bushewa take shiyasa suke aikata abubuwan da ba'ayi tsammani ba, and ke kika ba ni labarin yadda ya dauki rai ba a bakin komai ba" "Ya taimake ni sosai, shi ne mutumen da ya fara yarda zan iya kamin kowa, mutumen nan ya tsaya a tare da ni lokacin da ba ni da gata, shi ya inganta rayuwata ya ba ni gata, ya kula da yarana, idan ya ji ni a cikin damuwa komai yake zai bari ya zo gurina, ba zan so wani abu ya same shi sanadina ba, a yanzu ne da na samu mahaifiyata nake fahimtar kyautatawar da mutane suke min tana da girma" "Rayuwarsa a fili barazana ce ga rayuwata da kuma ta ki, ban sani ba amman na san ba lallai ya fahimci kyautata muke miki ba, zai iya cewa zai dauki mataki da zai iya illataki, don a yanzu zuciyarsa a rufe take kuma daman ya saba dukanki, sannan shi baya son ki zauna da kowa fa karki manta da wannan, kuma idan ya dawo kusa da ke kin san kudinsa, yana son ya aure ki, ke zaki iya aurensa? Bayan kuma ba son shi kike ba?" Ta girgiza kai. "Bana fatan sake komawa dakin soyayya na rufe wannan kofar, bana marmarin zaman aure da kowa, yadda na sami rayuwa a haka ta wadatar" Aliyu yayi shiru be ce komai komai ba, ita ma ta yi shiru ta cigaba da wanke wanke da take cikin rashin dadin rai har da hawaye. Ya juya ya fita ta nufi inda mahaifiyarsa take, ya kwankwasa kofar dakinta kusan sau uku sannan ya tura ya shiga, kwance ya same ta waya a kunnenta tana ta magana da waya Inlaw dinta gwaggon Aliyu. Sai da ta gama wayar sannan ta kalleshi. "Ai na dauka ka yafe mu" "Na isa ne? Na dan huta ne kuma kuma na ba ku dama ku huta, yanzu ma ba zuwan kaina ne ba, Mama Baraka ce ta ce tana son na taho mata da Emily" Ummi ta tashi zaune. "Nice ko jiya ta zo gidan nan kuma sun yi magana" "Toh wata kila tana son ita Emily din ta tafi gidanta ne" "A yadda na karanci yanayin Emilyn kamar bata marmarin zuwa gidan ne shiyasa ban matsa ba, kuma ni kaina ba son zuwanta nake gidan ba saboda Kameela, kasan yarinyar zafin kishinta ya wuce misali za su iya sanadin da za a karawa uwar sauran igiyar ma, da dai ace bata gidan ne zai fi kyau Emily ta tafi, kuma ko zata tafi ba kai zaka kaita ba, ita zata aiko a dauke ta ko kuma a saka direba ya kaita gidan daga nan" "Ta fada min ta shirya mata wani abun mamaki ne, kuma bata son abun ya wuce yau, ban san miye ba amman ya kamata ta tafi" "Sauka ka fada mata idan ta yarda direba zai kaita, kai kam baka da alaka da gidansu Kameela a yanzu dan haka bana son ganinka a gidan, ka bari sai idan Allah ya kaddara Hajiya Bakara ta zama Inlaw dinka wannan dole ka shiga gidan, amman ba yanzu ba" Aliyu yayi mata kallon rashin fahimta. "Ta ina zata zama Inlaw dita?" "Ta abin da kake karyatawa mana" "Babu abun da make karyatawa, Ummi ba abun da kike tunani ba ne, bayan haka kuma Emily fa tsohuwar matar Turhan ce? Ko mutuwa yayi ai idan nw auri matarsa ban kyauta ba, sai yace daman kudirina kenan shiyasa na aikata abun da yake zargina, alhalin har ga Allah ba dan na aikata hakan ba ne" "Saboda me? Haramun ne? Da ka yarda da abun da yake ranka da karka yarda alaka dai tsakaninka da Turhan da Ammy ta riga ta lalace, kuma ba zata taba gyaruwa ba har abada, ni kawai ina fada maka abun da yake gaskiya ne, ba saka ka zan yi na ba hana ka zan yi ba, ai lokaci alhali ne, kuma komai rufin da aka yi idan ta yi tsami dole sai ya fito, na mu ji ne kawai" Ya mike tsaye ya fice daga dakin yana murmushi don ya san duk yadda zai buga misali ko ya ayyana Ummi ba fahimtarshi zata yi ba, nata tunanin take dabam. Falon ya sake dawowa ya nufi Kitchen kamin ya shiga Emily ta fito tana rike da hullar da ya bata, kamar mai tsoro haka ya waiga ya kalli upstairs sannan ya mika mata hannu. "Zan iya samun hulata yanzu?" Ta karasa ta mika masa sai ya karba ya saka a kansa tana kamshin gashin Emily da ya sha gyara da mayuka da turare. "Mama Baraka ce ta kira waya wai tana son ki zo yau gidanta, kuma yanzu nan ma" Emily ta dan wara ido. "Jiya ai ta zo nan, shekaranjiya ma ta zo kamin shekaranjiya ma ta zo kullum tana zuwa" "Toh yau so take ki tafi, kin san daman na mata alkawarin zan kawo ki, amman dai na zan samu zuwa ba direba zai kaiki, ki shiga ki shirya yanzu?" "Ni bana marmarin tafiya gidan" "Haka zaki daure, umarni ne ai nake baki ba neman ra'ayinki ba I'm your boss" Ta bude ido sosai da mamakinta. "Ai ba a gurin aiki muke ba, a nan gida ne, baka isa kamin dole ba" Ya saka hannayensa alhaji duka biyu. "Really?" "Yeah..... Kuma gwada ka gani" Yayi murmushi kawai. "Kin san daman mun saba fada ko? So kike mu tuna baya kenan? Direba yana jiranki?" Ya fada yana nuna mata kofa da ido, sai ta nufi upstairs ta canja riga da skirt din dake jikinta zuwa gown din atamfa har lokacin kanta babu dankwali bata samu Aliyu a falon ba, kai tsaye ta nufi kofar fita ta bude ta fita sai ta hango shi tsaye jikin wata mota dake kunne, na yi kyau?