← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 177

Sashe 7

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yi ma Ammy magani haka ta juya min baya, gaba daya na kasa gane kan mahaifiyata Mannir dake kallonsa ya ce Amman dai ka san abun da ka yi mata baka kyauta ba? Baka ji haka ba? Na san ban kyauta ba Manir kuma na ji babu dadi, ina kan jin babu dadin ma a duk lokacin da na tuna, amman yadda Ammy ta hau karamin abu ta maida shi babba shi ke daga min hankali kuma ya ba ni mamaki Iyaye sai hakuri, kuma kasan Ammy ta dora hope sosai akanka game da yarinyar nan, sai kuma gashi ka bata kunya, waya sani ma da ace ita kake aure har yanzu wata kila da yanzu kun haihu, gashi nan wannan yarinyar da ka fifita akanta har yanzu baka baka a ko ya ba A take yanayin Turhan ya canja duk kuwa da ya san gaskiya aminin nasa yake fada, kuma samu a ko ya wani abu da yake fata kuma ya dade yana mafarki. Mace bata bawa kanta haihu, duk wanda ka ga ya samu haihuwa hukuncin Allah ba yin kansa ba Haka ne, sai dai kuma wata kila yana cikin dalilin Ammy na yin fushi da kai, kuma yarinyar nan fa abar tausayi ce Na sani, amman Manir ana samun sabani sosai akan abubuwa kuma sai ka samu iyaye sun yafe sun duba dansu, amman ni Ammy ta kawar da idonta a kaina gaba daya Manir ya sauke ajiyar zuciya. Yanzu ka aje duk wani hange hange da tunanin banza, ta ina zamu fara? Nemanta, zan shirya duk abun da zan yi a yau, gobe zan sauka Lagos zan fara nemanta Wane tabbaci kake da shi cewar tana Lagos? A can aka haife, acan ta taso kuma bata san kowa a nan arewa ba, kamin ta bar nan Ammy ta fada ta ganta a coci, bana tunanin zata iya zama garin nan ma gaba daya, idan har zata zabi zama cikin kista yan'uwanta ba ta da wani gida da ya wuce Lagos, matsalar kawai a Lagos din ban san wane gida take ba Shi ne Matsalar, kuma Ammy bata ffada maka wane gidan Marayu ta zauna ba? Bata fada min ba, amman dai zan yi ta bincike har na gane Baka san kowa a Lagos ba, nemanta ba zai maka sauki ba, gaskiya Ammy ta dauki abun nan da zafi Turhan ya busar da iskar bakinsa. Zan tuntubi Aliyu yayi zama Lagos kamin ya koma Port Harcourt, maybe zai iya hada ni da wani da zai iya taimaka min mu yi neman tare Oh na manta ma da shi Wallahi, ka yi masa magana mu ji ba zai rasa wanda zai taimaka maka gurin nemanta ba, ni kuma zan yi ta lallaba Ammy a nan ko zamu samu wani abu daga gurinta Turhan ya sake daukar Mug din ya sha tea. Ta fa yafe min, kawai dai ita wai yadda muke a da ne, ta ki ta dawo min a haka Irin wannan ai sai ya saka ka ji ka tsani yarinyar, ko da yake.. Manir yayi shiru ba tare da ya karasa ba. Turhan ma be sake ce masa komai ba ya maida dubansa wani gurin sai tunani yake. EMILY POV. Jin an taba fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali tana kallon Vito dake zaune gefen gadon kusa da ita. Tashi ta yi zaune tana kallonsa, kallonta yake shi ma irin kallon nan mai cike da kauna, sai dai girman kai da jin isa ya hana shi sakin fuska balle har ta ga murmushinsa. Ina London? Yana dakinsa, me yasa baki fita da mota ba? Bana son kowa ya san wani abu akaina, na fada maka wata sabuwar rayuwa nake son yi Ta yaye blanket din dake jikinta ta matsa ta saka kan gadon ta dayan gefen, sai yayi hanzarin rikota ya juyo da ita da karfi. Fita mota zai hana wani abu daga canjin rayuwar da kike so ne? Mi kike shiryawa ne Emily? Me kake tunanin ina shiryawa? Na sha fada maka ina son na yi rayuwa kamar kowa, ina son rayuwata ta zama daidai, dole ne sai na shiga mota? Bana ra'ayin haka? Me yasa kake cilasta ni yin abubuwan da bana ra'ayi? Why? Ya matsa kusa da ita sosai yana kallon cikin idonta. Saboda ni kadai na isa na cilasta ki, kuma idan tunaninki ko shirinki na rabuwa da ni ne, to kina shiryawa kanki wani rame ne na halaka, domin ban gane duk wannan abun da kike ba? Me ye ban aje miki ba? Amman tunaninki yana wani gurin dabam, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba ki saka wannan a ranki, you're forever mine Ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata amman ta kasa. You're hurting me... Ta yi magana cikin yanayin dake nuna tana daf da fashewa da kuka. Mami Jin muryar Fadima ya saka shi saurin sakin hannunta domin ko kadan baya cin zafinta a gaban yaranta ko da kuwa me ta yi masa. Emily ta nufi kofar da sauri tana budewa murmushin dole ya ci karfinta a yayinda take kallon Fadime dake kokarin sauke school bag dinta. My Baby kin dawo Ta karasa kusa da ita ta rika mata jakar, Vito ya fito daga dakin ya karaso kusa da su. Lisa Ya kai hannu zai shafa kanta, haka yake kiransa saboda ya tsani sunan da Emily ta saka mata na musulmai. Sai ta kauce daga taba kanta da zai yi tana hade rai. I'm not Lisa I'm Fadima Hakan kuma be hana shi yin gutun murmushin da yayi niya ba, domin idan da sabo ya saba da halin yar Emily na nuna masa kiyayya a fili wani sa'in har ta kan fada masa bata son shi, duk kuwa da irin hidimar da yake da su. Ta kaunce daga gurin gaba daya ta nufi dakin dan'uwanta, daga Emily har Vito binta suka yi da kallo. I don't know why, Lisa hate me so much Yarinya ce zata daina nan gaba Emily ta amsa masa tana kokarin kare yarta, ta san shi ma be cancanci irin wannan kiyayyar daga gurin yarta ba. I hope so, i can't ki haifo min babyn da zata kira ni da babanta Ya fada yana kallonta tare da karantar reaction dinta. I thought i told you ni na gama haihuwa Nope... Baki gama ba sai kin haifo na wa Kallonsa kawai ta yi ta dauke kai ta nufi hanyar kitchen, binta yayi da ido har sai da ta shige sannan ta juya yayi ficewarsa. [4/20, 9:57 AM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 7 · 0% Book details