← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 177

Sashe 9

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cire gashin dokin dake tsarkafe cikin nata red hair din bata daina hawaye ba. Kwashe gashin dokin ta yi ta zuba a dusbin sannan ta gyara kanta, idan ba ka taba ba, ko kuma an fada maka ko ka sani babu wanda zai yarda gashinta ne domin jan gashi take dashi ba kamar sauran mata da suke da jan gashi ba, ko da yake blue eyes dinta da farin fatarta ya isa ya fahimtar da duk wani mai kallonta cewar ita ruwa biyu ce ba tare da tantama ba. Ta canja tufafin jikinta zuwa na bachi, ta gadonta ta jingina, ta dade a haka sannan ta mika hannu ta dauko file din da Amal ta bata a gurin aiki ta bude tana duba dokoki da ka'idodin kamfanin, bayan ta gama ta saka hannu a duk gurin da aka bukata, sannan ta aje ta kwanta ba tare da ta kashe wutar dakin ba, domin bata bachi da wuta a kashe. Kasancewar a cikin duhu yana firgita kwakwalwarta, ta kan kasa sakewa da rasa natsuwa sa sukuni, sanin hakan da Vito yayi ya saka shi tanadar mata duk wani abu da zai bata haske idan babu wutar nepa. Bata kwanta da wuri ba, hakan ya saka bachin yayi mata nauyi bata tashi a lokacin da ta so tashi ba wato 4am. Karfe biyar da yan mintuna ta farka tana murza ido, alarm din dake gefen gadon mai hade da agogo ta dauka ta duba. 5:14am ya saka ta zabura da kuzari ta sauka saman gadon ta saka bedroom slipper ta fice da sauri. Tun kamin ta sauko kasa ta soma jin kamshin yana dukan hancinta, tsayawa ta yi ba tare da ta karasa saukowa daga kam stairs din ba tana kallon hanyar Kitchen din da dan tsoro, a iyakar saninta Chidimma ba ko da yaushe take shiryawa yaranta abun karyawa ba, sai idan bata gidan ko kuma ta bukaci ta shirya musu din, and babu wanda ya san kudurinta na son shirya abun karyawa da wuri saboda fita aiki, ita kanta bata shirya musu abun karyawa sai 6am. To waye a kitchen din. Ta fara bin falon da kallo, har idonta ya sauka akan rigar Vito dake aje a kan kujera, siririyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin kamar hankalinta ya kwanta, daman idan wani abun cutarwa ne ai zata ji hayani ko a tashe ta, tun da akwai mai gadi a gidan. Saukowa ta yi a hankali kamin ta karasa Kitchen sai gashi ya fito rike da plate, dinning ya nufa ya aje plate din sannan ya nufo gurin da rigarsa take ya dauka ta nufota ta rufe mata jiki da rigar ya kai bakinsa saitin bakinsa zai sumbance ta. You already know how much i hate physical touch, i hate anything related to love Ta fada bayan ta kawar da kanta, sai ya juyo da fuskarta yana kallon cikin idonta zuwa gashin kanta dake red, irin na jajayen turawan nan da ake haihuwa da jan gashi. Good Morning Ya fada ba tare da murmushi ko sakin fuska ba, daman murmushi da far'a abu ne da suka yi ma fuskarsa tazara, abu ne mai wahala yayi murmushi idan ma yayi kadan ne ko na gefen fuska balle kuma dariya da yake jin bata zame masa dole ba. Hannayenta ta saka ta sauke nasa hannayen dake rike da fuskarta, ta nufi kitchen tana fadin. Me kake dafawa? Me yasa ka zo nan da wuri haka? Juyawa yayi yana kallonta madadin ya amsa mata sai ya jefo mata wata maganar da ya saba fada mata a duk lokacin da take kokarin kaucewa kaunarsa. Da ace zan yi arba da mutanen biyu da suka saka kika tsani soyayya, suka rikita miki lissafi, da na saka sun tsani kansu, da na rikita kwakwalwarsu Sun dade da mutuwa a gurina, rayuwa ta baya ma na jafar da ita, Emily din da ba ita ce yanzu ba, wacan ta mutu wannan kuma yanzu take rayuwa Ya taka ta bi bayanta har cikin kitchen din ya tsaya daga gafe yana kallonta, ita kuma sai duba abincin take, farfesun naman kaza, sai dankali da plantain, dayan cooler kuma samosa ne da zafinsa. Ta daga ta kalleshi da blue eyes dinta masu matukar daukar hankali. Meyasa ka shirya duk wannan Ya matsa kusa da ita sosai. Kin fada min 6:30am zaki tafi aiki, bana son ki tafi da yunwa, kuma na san idan kin farka zaki iya cewa sai kin shiryawa Fadima da Londom abinci zaki tafi, shiyasa na zo tun 4am, na shigo kina bachi Kallonsa take cike da tausayawa domin hidimar da yake ta yi da ita, bata san wata hanya da zata saka masa ba. Me yasa kake takurawa kanka da yawa saboda ni? A irin wannan lokacin kamata yayi ace kana kwance kana bachi ne, V baka bukatar hidima irin wannan saboda ni Hannunsa daya ya kai ya rika fuskarta, kaunarta yake karanta a fuskarta da idonta, da ta san yadda yake jinta a ruhinsa wata kila da bata fada masa magana makamanciyar wannan ba. Be ce da ita komai ba ya saki fuskarta ya gyara mata jacket dinsa dake jikinta ya rumgume ta, ya lumshe ido. Ta jure iya juriyar da zata iya na bashi damar rabar jikinta na second goma ne kawai bayan wannan sai ta fara kokari raba jikinta da nashi. A tare suka karasa dan abun da ba za a rasa ba, sannan ta shiga ciki ta wanke bakinta ta fito ta yi breakfast din yana zaune yana kallon yadda take jindadin abinci, ba lokacin cin abincinsa ba ne, baya karyawa dai 10am, a yau kuma kallonta kadai da jindadin yadda take cin abincinsa ya wadatar da shi, farincikin fada masa abincinsa yayi dadi da ta yi ya kosar da duk wata yunwa da zai ji a wunin ranar. Ya daga mata kai yana murmushi kadan, yana jin kamar ace su daure a haka, su yi zama irin na masoya ko ma'aurata, sai dai ya san samun haka a gurin Emily a yanzu ba abu ne mai sauki ba. Kallon agogon falon da ta yi ya saka ta yi hanzarin karasa cin abincin ta mike tsaye. Bana son na yi latti, karfe 6:30am zan tafi aiki Wane irin aiki ne za'a tafi karfe 6am? Me yasa kike son takurawa kanki a yanzu Emily kina da komai a nan Bata ce masa komai ba, ta cire jacket dinsa ta aje a jikin dayar kujerar, ta kwashe kayan da ta bata ta kai kitchen sannan ta wuce ta haura sama. Mikewa yayi tsaye ya nufi jacket din ya dauka yana kallon stairs din kamar mai jiran fitowarta. TURHAN POV. Baka amsa ni ba Ta maimaita da yaren da ita da shi suka fi fahimta, wato Larabci. Lemun dake gefen Laptop din ya dauka ya sha ya aje sannan ya kalleta ta cikin Systems din dake gabansa. Ba yanzu ba, akwai wani aiki da ya taso min, ina son sai na karasa shi tukuna? Wane irin aiki ne Hayatie? Ya kawar da fuska kaminnya juyo ya kalleta yana shafa kansa, bata jira amsarsa ba ta sake aika masa da wani zancen. Ba zan iya jure rashinka a kusa da ni ba Abu mai muhimmanci baki bukatar sani, idan na kammala zan dawo Ka canja min a yanzu Ya shafa kansa yana jin wani sabon fushi na kokarin rufe shi. Saboda bana haihuwa ne, ko kuma dai ka gaji da zama da ni ne? Zaki iya ba ni a? Zaki iya haifa min jinina Jalila? Ta yi shiru tana kallonsa kamar yadda shi ma yake kallonta, kamin ya kai hannu ya rufe Laptop din ya kwanta jikin kujerar yana maida numfashi, me yasa ya fada mata haka? Al'adunsu da dokokin sa ake cilasta masa bi ba daga ita ba ne daga masarautarsu ne da kuma mahaifinsa. Ya tashi zaune yana jin fushinsa yana karuwa tunawa da yayi da yadda Ammy ta yi fushi da shi, saboda yarinyar da bata da ala komai da ita. Gaba daya an hada masa zafi ta ko'ina, babu wani daki daya da zai laba yaji sanyi. Wayarsa ya dauka ya kira abokinsa har lokacin be sauka daga fushi da bacin rai da yake ji ba. ALIYU POV. Yana zaune a kan gado, matarsa na kwance kanta na cinyarsa, ita da shi sun sakarwa plasma dake dakin idonsu, gadon da suke kai kuma ya karbi amanarsu, domin kana kallonsu zaka san hankalinsu a kwance yake basu da wata damuwa ko kadan. Wayarsa dake can kan karamin tebur ajeye ce ta yi ringing, a take ya ja tsaki domin ya ji dadin zaman baya son motsawa. Gashi be saba zama kusa da wayarsa ko yawo da ita idan yana tare da matarsa ba. Abu ne da ya sabawa kansa da shi aje wayarsa a nesa da matarsa a duk lokacin da yake tare da ita, doka ce ya sakawa kansa matukar yana gida tare da iyalinsa to lokacinsa na matarsa zai bata kulawa iyak ar kokarinsa. Gwanar na jin haka sai ta tashi zaune tana kallonsa. Na dauko maka ka ba ni dubu biyu? A take murmushi ya subuce masa. Wai ke ina zaki kai kudi da son kudin nan? Ta saka dariya. Zaka biya na dauko? Aa ni ma fa na san zafin kudi Hajiya, zan dauko kayata Sai ta maida kanta a cinyarsa. Ni gaskiya na jidadin kwanciyar nan ba zaka tashi ba Okay saboda ni zan dauko ko? Idan ni zan dauko zaka biya, idan ba haka ba gaskiya ba zan daga a cinyar nan ba, ai kasan idan kana gida kai nawa ne ni kadai Ko ma bana gida ni naki ne har abada, yanzu daga ni na dauko sai na biya 2k din, kin ga wannan tsohon cikin naki ba zan so kina wahala ba Ta daga masa saboda ta ji yace zai bata kudin kuma zai dauko wayar da kansa. Hmmm ku dai maza idan kuna tare da mu ku namu ne idan kun fita kuma na wasu dai Ya mike tsaye ya isa ya dauko wayar yana murmushi already kiran ya yanke. Ke dai kishi zai miki illa, me ya kawo wannan maganar kuma? Ai na san halin maza Bayan wa kika aura? Da
Chapter 9 · 0% Book details