Sashe 45
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata. "Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu" "Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can" Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba. Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita. Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage. Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba. "Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa" "Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan bangaren ba" "Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na dawo Aisha" Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka. "Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tashi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?" Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa ta bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya shigo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa. "Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutanen Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida" Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin mahaifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska. "Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa" "Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke" "Ko kawa ba ni da a garin nan balle na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa" "wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne" "ina yi saboda na samu abun da zan ci" "Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda da kaddara" Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne. "Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?" "Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi" Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi. "Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki" Ya fada, ashe kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abinci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa... Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin." ***. ***. *** Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce. "Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...! Yawancin irin wa annan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi. Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?' Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa ha ari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...' Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni kamar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na yi da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa. Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa karasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba