Sashe 5
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
din da ta fito. Vito na daga cikin dalilinta na son ta inganta rayuwarta ita kadai a yanzu ba tare da taimakonsa ba, duk kuwa da kasancewar shi ne silar komai nata a yanzu. But tana son ta samu freedom so take ta samu yancin rayuwa ita da yayanta kamar sauran mata, ta jika a kangin bauta har yanzu so take ta yi rayuwa ita kadai ta tsayu da kafafuwanta, ta zama Independent woman. Sai da ta daidai tsayuwarta ta nemi kwarin guiwa da confidence ta lullube zuciyarta da shi sannan ta kai hannu ta yi knocking Office din. Shiru ba ta ji ance ta shigo ba, hakan ya saka ta sake kwankwasawa a karo na biyu, ta sani a yanzu kam ba zai yi ace bata ji ba, sai dai dan wulakanci zata aje ta a gurin, kuma ba ta yi mamakin wulakancinta ba, saboda ga dukan alamu macen musulma ce, a iya kar ilimin Emily kuma musulmai ba su da kirki. Ta kusa minti biyar a tsaye sannan ta yi mata izinin shiga. Emily ta tura office din ta shiga sai dai wannan karon babu irin murmushi dake fuskarta a wacan karon. A nan din ma sai da ta sake gabatar mata da kanta, matar ta dan kalleta ta dauke kai, after like 10 seconds, ta dubi Emily tace. Aisha sunanki ko what so ever, za ki yi aiki da ni a matsayin Assistant dita, aikinki shi ne kullum zaki shigo 6:30am 7am ta yi miki a nan, zaki yi mopping office din nan ki gyara komai, kamin na shigo, zaki hada min abun karyawa kamar tea ko coffee duk abun da yake available dai ko kuma nake ra'ayi, and duk abun da nake bukata na aika ko yi ke zaki min, and lastly Office dinki yana next to mine Ta mike tsaye cikin izza ta isa gurin wata karamar durowa ta bude ta dauko file da keys ta dawo ta mika mata. Akwai ID na aikinki a kamfanin mai dauke da sunanki da hotonki, zaki saka a wuya ne kullum idan zaki shigo kamfanin nan, a cikin file din akwai rules and regulations na kamfani ki yi saka hannu ki dawo da shi gobe Ta dora mata keys din a saman file. Wannan key din office dinki ne, hadi da nawa saboda ki samu damar gyara min nawa ko daukar wani abun idan bana kusa Okay, Ma'am Thank you Emily ta furta sannan ta juya. And... Sunana Amal not Ma'am, ba dole sai kin yi aiki ba, idan kin duba office din ki yi tafiyarki, gobe ki shigo da wuri Okay Ta amsa ba tare da ta juyo ba, Amal ta bita da kallo tana yatsina fuska har ta fice sannan ta nufi kujerar. Da wasu idanuwa blue kamar na aljannu, ko mage, waya sani ma ko mayyace, ko wace yare ne ma oho Sai kuma ta bawa kanta amsa. Zata wuce Igbo dama sune kafirai ai emily na fita office din ta nufi office din dake kusa dana Amal, sai da ta karewa kofar kallo sannan ta saka key din ta bude ta shiga. Komai fes ga computer da karamin tebur daidai ita, ita ma tana da karamin dorowa kamar Amal. Window ta kuma yana facing din gari da makwantan gine gine da suke wajen kamfanin sai titi da zata iya hango hada hadar mutane, ta dan samu sakewar zuciya wanda har ta kaita ga murmushin jindadi. TURHAN POV. Bude motar yayi ya fito yana shafa fuskarsa ya kalli kofar falon bayan ya rufe motar, sai da sauke ajiyar zuciya irin ta manyan mazaje yayan sarauta sannan ya sake komawa falon mahaifiyarsa. Yana turo kofar falon Ammy ta juyo ta kalli kofar, ba yi mamakin sake ganinsa ba, domin haka yake mata naci a duk lokacin da ya zo gidan. Jajirtacen namiji, gwani na gwanaye, mai isa da tinkaho da burinkasa da sarautar gidansu, mai son farinciki ubansa fiye da na uwarsa, mai martaba auren ubansa ya watsar da na uwarsa Ya zube kasa yana taba kafarta damuwar dake fuskarsa kadan ya rage ta saka shi birgima, domin ya san ma'anar kirarin da Ammy take masa. Ammy ta matsar da kafarta daga hannayensa. Da haka kake da na ci da jajircewa a baya, da yanzu Aisha tana nan tare da mu, bata gudu ba Kansa a kasa ya soma magana cikin magiya tare da fatan zata amsa rokonsa. Ammy na dawo nan ne saboda na tambaya, a dan zaman da Aisha ta yi a gidan nan ta taba fada miki suna da kuma unguwar da gidan marayun da ta zauna a Lagos yake? Zan tafi Lagos din na bincika ko Allah zai saka a dace Har Ammy ta yi shiru sai kuma ta kalleshi. Eh ina zuwa Ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta, wani sanyi ya ji ya sauka a zuciya jin cewar kamar ya kusan samun hanyar da zata sadashi da Aisha. Babu jimawa Ammy ta sauko tana kallonsa idauwanta a kankance irin bacin rai, sai da ta zauna sannan ta mika masa takardar dake hannunta. A lokacin da ta shigo ta dauki danta ba tare da na sani ba, ta bar min wannan akwai address dinta a ciki Turhan ya karba da sauri ya warware takardar da kana ganinta kasan ta jima a ajeye. _Kin ce danki ya sha babban da sauran, wata kila dai baki fahimci danki ba ne, wata kila kin hada aurena da shi ne saboda kina neman mafitar yadda zai dawo gareki, amman duk halinsu daya, shi ma be san daraja ta ba, na fada miki musulmai ba su da kirki kika karyata ni, akan abun da yake zahirinsa, musulmai basa kaunar tubabben basa son kowa sai wanda ya tashi dan asalin dan musulmi, ba su da mu'alama mai kyau, basu san darajar kowa ba sai junansu, abun da kuke aikatawa dabam karantarwarku dabam, shi ma an da kike cika baki da shi ya wulakanta ni kamar wancan, duk akan me? Addininku? To na bar muku, zan koma a gurin da nake da daraja Tun gabani ya gama karanta wasikar zuciyarsa ta tsinke hawaye suka taru a idanuwansa har suka sauko a fuskarsa. Saboda kai Aisha ta ji cewar bata da gata a gurin Musulmi, ka karyata duk wani abu da na yi amfani da shi na karfafa guiwar yarinyar nan, kuma ka saka ta ji cewar na yaudareta, ba ni da wani addireshinta bayan wannan Turhan ya daga kansa ya kalli Ammy, ganin hawaye a fuskarta, ya saka shi cikin tashi. Zan nemo ta Ammy, zan nemo ta ko da hakan yana nufin na yawace duniyar nan, zan samo ta ko da hakan yana nufin rasa rayuwata ne, zan kawo miki Ammy wannan alkawarina ne Ya mike tsaye ya share nasa hawayen ya fice daga dakin rike da takardar. _________________________ Wai me Turhan ya aikatawa Aisha ne? Me yasa Ammy ta gagara shiryawa da shi? Anya kuna ganin Emily zata jure aiki a karkashin Amal kuwa? Bayan kuma Amal bata son kafirai, Emily kuma bata kaunar musulmai? [4/20, 9:57 AM] ABOKIN RAYUWA