← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 177

Sashe 57

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ke" Ta dago daga jikinsa ta kalleshi. "Emily lokaci yayi da ya kamata mu yi aure" Ta ji gabanta ya fadi ba tare da dalili ba. "Kin san ni kin san waye ni, na san ki kuma na so ki, kuma kin san cewa har kasa ta nade wani be isa ya so ki ba sai ni, toh bata lokaci na miye? Har zuwa yaushe zan yi ta jiranki?" Ya kama hannunta. "Na lura baki son na taba ki a yanzu, shiyasa nake daga miki kafa, a yadda nake sonki na fi son mu yi komai cikin farin ciki, kuma auren ki kadai ne zai tabbatar da hakan" Ta zare hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tsaya ba tare da ta ce komai ba. "Kina jiran mutanen da suka wulakantaki ne su dawo miki? Ko kuma wani kike dako a gaba? Mutanen da suka rasa ki sun rasa ki kenan har abada, wanda kuma yake zuwa nemanki idan wani abu ne a zuciyar sa toh yana wahalar da kansa ne kawai domin ke mallakina ce kamar dai haka" Ya cire zobe hannunsa ya nuna mata sannan ya maida zoben a dan yatsansa. Ya mike tsaye ya fice daga dakin ya barta tsaya tana mamaki da tambayar kanta wa ke zuwa nemanta? Wata kila Tasmia ce, amman namiji yace, bayan Aliyu bata san wani namiji da zai zo nemanta ba, ko kuma Turhan ne? Ta tambayi kanta, for the first time bayan dawowarta gidan ta ji tana bukatar wayarta, wayar da tun a ranar da London ya mutu bata sake bi ta kan wayar ba, a zamanta nan kuma tunaninta ya tafi a gurin danta da ta rasa bata damu ta nemi wayar ba. Tun da ya dawo da ita gidansa bata fita ko'ina daga cikin gidan sai harabar gida, ya dauko Chidimma da Fatima ya dawo da su gidan a tare da ita ga kuma mahaifiyarsa. Sai dai ko kadan Fatima bata son zaman gidan saboda mahaifiyar Vito da take ganin ta takura mata, kuma ga shi bata so bata masa biyayya Vito. Emily ta nufi kofar dakin ta fito ta sauko hawa na biyu a zatonta Vito yana gurin domin ya fi yawan zaman a falon dake hawa na biyu, a gurin ta zauna tana tunanin ko dai Aliyu ya bawa Turhan addireshinta ne ya zo nemanta? Ko kuma Aliyun ne da kansan yake nemanta.? Kamar an tsikare ta mike tsaye ta sauka falon na farko bata karasa sauka ba ta ji muryar Fatima tana ihu da fadin "I hate you... I hate you" Ta sauka da sauri ta nufi gurin da Fatima take tsaye Chidimma na gefenta tana rike da cups din da aka fasa, Vito na zaune kan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon Fatima fuska babu annuri. "Me ya faru?" "Me yake sabu a ciki? Rashin kunyar da yarki take yi ko kuma fadar bata son Vito a gaban kowa? Gaba daya yarinyarki bata da tarbiya, taya zata kalli idon mutumen da akarkashinsa kuke tana zaginsa?" "Ki yi hakuri Momy ina iyakar kokari gurin ganin na gyara halayyar Fatima na san abun da take ba shi da kyau amman ita yarinya ce" "Ina kokarin da kike yi nuna min na gani. yara nawa ne sa'ainta basa abun da take? Yarinya karama amman ta iya shiga idon manya? Idan ba Vito ba wa zai iya zama dake ko yarki?" Sai a lokacin Vito ya mike tsaye domin ya ji mahaifiyarsa ta fara saka Emily. "Okay that's enough" Yaja Emily ya maida ita bayansa. "Ba laifinta ba ne, wannan yarinyar da kika gani ga dukan alamu bakin halin mahaifinta ta dauko shiyasa bata kama da Emily ko kadan, saboda babu halin ta ko daya a tare da ita" Fatima ta sake kallonsa "I hate you i hatee youuuuuuuuu" Ta kalli mahaifiyarta. "Momi na ce miki bana son nan gida nake son tafiya bana son nan" "Okay zamu je" Emily ta amsa da sauri kana ta kalli Vito. "Ina son zan koma gida" Momin ta Vito ta yi dariya. "Baki da ra'ayin kanki kenan sai na yarki? Karamar yarinya zata juyaki tana fada miki yadda zaki yi? Shiyasa kike kyale ta tana abun da ta ga dama?" Emily ta daka mata tsawa. "Yata ita kadai ta rage min a yanzu ba ni da wata bayan ita, abun da take so shi nake so, ki cire idonki akan yarinyata, tun da muka zo gidan nan kullum sai kin ce ga laifinta" Momynta ta mike tsaye tana kallon Vito. "Kajinta ko?" Vito ya kalli Emily calmly yace "Je ki jirani gurin mota, Chidimma zata hado kayanku yanzu zan kaiki gida" Emily ta kama hannun Fatima suka fice daga falon, Chidimma ta sauke numfashi ta nufi Kitchen ta zuba cups din hannunta a shara sannan ta fito ta haura sama inda dakin Fatima da Emily yake. "Kana ji tana fadar abun da yarta take so shi take so? Daman ina tunanin bata lokacinka kake yi a kan yarinyar nan baka yarda ba" "Bana bukatar Emily ta so ni, tun da ni ina sonta hakan ya wadatar, na sani tuntuni ban gama shiga zuciyarta ba, amman da sannu zata gane kuma zata gode min ta kaunace ni, zuwa lokacin da ta rasa Lisa (Fatima) za ta gane bata da kowa sai ni" "Idan kuma hakan bata faru ba fa?" "Abun da yake nawa nawa ne har abada ke kin sani, dole zan yi ma Emily uzuri saboda ta sha wahalar rayuwa, kuma ta tashi bata da kowa bata yan 'uwan bata san kowa a jininta ba sai yaran da ta haifa, daya ya mutu sauran daya to me zai saka ba zata ki abun da yarta take ki ba?" "Wai miye a wannan yarinyar da lekewa haka ne? Kana da kudi zaka iya samun kowace mace kake so a duniyar nan, idan ma fari ne akwai fararen mata, idan kana ganin kamar ita baturiya ce zaka iya tsallakawa ka auro wanda kake so wanda ta fita kyau da komai, ita wannan fa har ta haihu kana ta wahala da yaran da ba naka ba" Ta nufi windows din falon ya daga curtains din yana kallon Emily dake tsaye jikin motarsa tana cizon hannunta. "Abun ba daga kyau ba ne kawai, wani abu ne ya hada zuciyata da kaunarta ya daure, kamin ita ai na ga mata da yawa ban so kowa ba sai ita, bayan ita ban ga wata wanda zan iya so ba, yarinyar da dukiyata bata dame ta, sanin tana da damar da zata iya sakawa na wulakanta kowa akanta be taba burgeta ba, ita kadai ce macen da ta saka na ji ina sha'awar tara iyali, mutuwar danta nan tana da damar ta tuhume ni saboda ni na barshi na fita alhalin ba a barinsa shi kadai, amman bata tana ce min komai akan haka ba bata taba nuna min bacin ranta ba, a yanzu zuciyarta a bushe take, nakasassun mazan da suka rayu da ita basu gwada mata komai ba sai azaba shiyasa har yanzu bata san yadda zata so kowa ba" Ya juyo ya kalli Mahaifiyarta. "Akwai mata da yawa, amman masu irin halinta kadan ne, a idona kuma ita kadai ce, kuma baki fahimce ta, karki sake fadin wata magana marar dadi akan Emily indai kina so, ki so Emily...!" Yana kawai nan ya nufi kofar falon ya bude ya fita, Emily na hango shi yana saukowa ta nufo shi da sauri tana hawaye. "Vito I'm sorry kasan be kamata na yi magana da mahaifiyarka haka ba, raina ne ya bace kuma..." Be bari ta karasa ba ya rumgume. "Na fahimta" "Zaka iya bata hakuri?" "Eh, shiga mota muje" Ya sake ta sai ta zagaya ta shiga motar Fatima daman ta dade a ciki zaune sai cika take tana batsewa kamar wata babba. Be jira Chidimma ta zo ba yayi ma motar key. "Chidimma bata zo ba" Be ce mata komai ba yaja motar suka fita daga gidan. Har suka isa gidan da ya tanadar ma be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba, amman hannunsa na rike da nata yana tuki da dayan hannun. Be gama farkin ba Fatima ta bude motar ta fita ta bar masa gambun a bude, fita yayi ya zagaya ya rufe motar ya budewa Emily ta fito tana kallonsa, ta kai hannu ta taba fuskarsa sai ya matsa baya ya bata hanya ta ratsa shi ta nufi cikin gidan shi kuma ya koma motar yaja ya fice gidan. Ta samu gidan yayi kura yayi gummm irin na gidan da aka dade ba a shiga ba, guri ta samu kusa da Fatima ta zauna tana jin kewar danta London yana dawo mata. "Kin ce zaki nemi kudi zaki yi gida mu bar karkashin Vito amman har yanzu ba ki yi ba" Emily ta dube ta. "Zan yi Fatima zan nema har ma dace zan zama miki irin rayuwar da kike so, ba ni da wani nauyi da ya rataya a wuyana yanzu sai na ki, amman ki daina abun da kike yi, ba haka yara suke ba, meyasa ke kika fita dabam?" Ta yi shiru tana turo baki, Emily ta ja jikinta ta rumgume tana jin rashindadin fadan da ta yi mata a yanzu. "Momy, yanzu tun da London ya mutu zan iya amfani da sunan mahaifinta a makaranta? So that yan ajinmu su daina min dariya?" Ta tambaya murya kasa kasa, Emily ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi ta lumshe ido. "I miss him" Cewar Fatima cikin sautin kuka. Emily ma kukan take. "I miss him too" Ta kara kankame yarta hawaye masu zafi na sauko mata. A haka Chidimma ta zo ta same su bayan direban dake gidan Vito ya kawo ta. "Zan yi kokari na baki rayuwa mai kyau Fatima, ni kam ba zan miki abun da iyayena suka min ba, ba zan taba bari ki ji cewar baki da kowa ba, ba zan taba wulakanta ki kamar yadda mahaifin London da naki suka yi ba, ina son jini ko yaya yake" "Momy waye babana? Baki san bani da baba ba? To waye kuma baba na?" Fatima ta tambaya tana lafe a jikinta. Emily ta share hawayenta da
Chapter 57 · 0% Book details