← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 177

Sashe 154

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 6 Aliyu da kansa ya daga waya ya kira Mama Baraka ya yi mata albishir da labari mai dadi, sai gata ta dira gidan cikin farinciki ita da duka yaranta suka wuni gidan har dare sannan suka tafi. Washe gari Mama Baraka ta yi waina ta yi sadaka kuma ta aiko musu da ita a nan tace su yi sadaka. Kwanakin da suka rage ma Aliyu na bin Ummi Abuja da su yayi amfani yana ta koyawa Emily addinin musamman karatu da bata iya ba, da kuma wadansu hukunce hukunce wasu baki ne a gurinta wasu kuma ta taba saninsu saboda ta taba kasancewa a cikin addinin a baya. Ana sauran kwana biyu Ummi ta tafi Ummi ta umarce Emily ta tafi gidan Mama Baraka ta fada mata zancen tafiyarsu kuma ta tafi gidan Ammy ma ta sanar saboda Fatima dake can hannun Ammy tsawon lokacin nan da Turhan yayi sati daya da barin garin Kaduna, Emily bata wani damu ba saboda ta yankewa kanta hukuncin zata bi Ummi ba kuma dan komai ba sai dan bata son ta yi nisa da Aliyu, dan haka bata damu ta sanar da Mama Baraka ko Ammy ba a ganinta kamar ita take da ikon kanta, saboda rayuwar ta da saba yi a baya, haka kuma take ganin idan ta tashi tafiyar da Fatima zata tafi ne kawai ta dauko ta a gidan Ammy. Ba Aliyu kadai ba Ummi ma tana taba mata wani bangare na karatun, Nafeesa ma haka Mama Baraka ma ta yi maganar daukar mata malamin islamiya da zai rika zuwa yana koya mata a gida, Emily ta nuna bata so wai ai Aliyu ya ishata, kuma bata yi karya ba, domin karatun da yake koya mata kawai take ganewa saboda yana mata komai daki daki, yana mata bayani ta irin sigar da take so shiyasa idan karatun ya shiga kanta baya fita, amman sauran sai dai ta yi ta tunanin me aka ce a nan ma. Idan Aliyu ne yake koyarda ita tana maida hankali ta iya waninsa kuma karatun wahala yake mata. Shi kanshi da ya fahimci hakan sai ya zama kullum a gidan indai ba wani abun ya fita ba, ko ya bijiro masa, a gidan yake karyawa yayi mata karatu idan ya fita ya dawo da rana su dorada dare ma kamin ya tafi gidansa sai ya fada mata. A yau bayan Aliyu ya gama koya mata karatun Sallah wanda shi yafi kowane muhimmanci yake tambayarta. "Kin yi magana da Mama Baraka? Akan tafiyarki?" Ta fara lilo da kafafuwanta kasancewa tana zaune kan kujera ne can kusa da motocin da suke aje a gidan. "Aa sai idan za mu tafi zan mata bankawana" "Kamar ya? Ta amince ki tafi ne?" "Sai ta amince? Na saba yin komai bana jiran umarnin kowa" Aliyu yayi murmushi ya aje littafin akan teburin dake tsakaninsu. "Da kika ce, yanzu ke ai yar gata ce ba ke zaki yi ma kanki hange ba, yi miki za'ayi, a musulunci mace ita ta ko'ina yar gata ce, idan tana yarinya tana karkashin kulawar iyayenta ne, idan ta girma tana karkashin kulawar mijinta, idan ta tsufa tana karkashin kulawar yayanta, a yanzu ke kina karkashin kulawar iyayenki ne, daga lokacin da kika ce ke zaki yankewa kanki hukuncin ba tare da neman izinin miji ko iyaye ba, to kin jefa kanki a matsala kenan, kuma raina iyaye a zauna lafiya, karki yarda zuciyarki ta raya miki wani abu akan Mama Baraka, ita uwace duk yadda ta zo sai dai ki yi hakuri da ita ki yi mata biyayya ki samu aljanna, ke da yanzu Allah ya cika miki burinki? Ga iyaye ga yan'uwa? To me ya rage? Sai idan miji ko?" Ta yi murmushi tana fahimta ko wane harafi na bayaninsa. "Gwanin Hikima, shiyasa na yi alkawari indai har zan sake aure ba zan auri kowane namiji ba sai mai irin sifofi da halinka" Ya bude ido. "Allah ko?" "Uhmm" "Ki ce kawai idan namiji yana da irin halina ya shigo za a bude masa kofa. "Aa fa, kai tsaye ba sai ya kasance kuma yana da irin sunanka" Ya dauke kai yana murmushin da ya bayyana hakoransa, ita ma ta yi murmushi ta yi kasa da kanta tana wasa da yatsunta can kuma ta dago tana masa wani kallo mai tafiya ta zuciya. "To ni wane hali ne da ni haka? Har Gimbiya da kanta tace ba zata zo kowane Yarima ba sai mai dabi'un wazirinta?" "Ba waziri ba ne, Sarki ne, na birnin wata zuciya da ta dade da jefar da kowa da komai ta shiryawa karbar kowane kalar yaki, ta yarda ta jure ko wane mashi da hakura da tsuka, da Gwarzon ya bayyana a cikin gonarta, sai ya nome duk wata ciyawa dake hana ta sukuni, har ta kai ganin sawun dokinsa kadai ya wadatar da ita da farinciki, da ya yaye komai sai ya maida zuciyar fara da taushi kamar auduga" "Idan kuma Jarumin ya kasance ba shi da sunana fa?" "Sai jarumar ta kasance a raye babu igiyar aure" "Ai mace bata iya rayuwa sai da ABOKIN RAYUWA" Ta yi murmushi kawai ta sauke kanta kasa, shi ma yayi shiru na tsawon lokaci kowane yana nazarin dan'uwansa. "A cikin idonki akwai wani haske dake hana mai kallonsu hango abun da ke ciki, balle ya hango ajiyar da ake, mai tafiyar yana wasiwasi, ya wuce ciki ko ya tsaya a inda aka ba shi masauki?" "Idan idanuwan suna da raunin hango zahiri, to abar zukata su yi aikinsu mana, ba mu isa mu hana su karasa abun da suka fara ba, na gode da karatun yau" Ta mike tsaye ta fara tafiya. "Wai likitan yana tsoron ko zuciyar bata warke ba ne, kar garin dinki liki ya sake sabon tsagi" Ya fada ba tare da ya juya ya kalleta ba domin shi ya bawa kofar shiga falon baya ne. Sai ta juyo ta kalleshi. "Wai sadaukin da furucinsa kadai ya shafe duk wani tabo dake zuciya ta zama sabuwa, shi ne kuma yake tsoron tara hannu ya rike ta daga faduwa? Ko dai shi ma yana raunatata ne?" Ya juyo da sauri. "Waya isa duk duniyar nan ya taba Ayusher, ko da kuwa Aliyun ne da kansa? Humaira sha zamanki ki huta, babu mai tuge shukar da kika yi, zuciya tana son abin da take so" Ta juya murmushi da farinciki sun bayyana a kowane gaba ta jikinta. Ya kwanta jikin kujera yana lilo idonsa a sama ya bude hannayensa sai murmushi yake. Ba zai karyata kansa ba, a da be sani na amman a yanzu karatun a bude yake, zuciyata tana son abun da take so, kuma take ganin ya dace da ita, ba dan kasan kadai ba, sai dan yana jin kamar idan ba shi ne ba, Emily ba zata samu farincikin da ya cancance ta ba ga waninsa, a yanzu kam baya jin saurari shawarar kowa bayan ta iyayensa duk wani abun da zai biyo bayan haka be damu ba, za a iya fadar gaskiya ko abin da ake hangowa amman be damu ba muradinsa ya samawa Emily abun da take so. Daga lokacin da ya fara lura ya fada, sai tunanin Turhan ya bijiro masa, be sani ba ashe wanda yayi nisa baya jin kira, a yanzu baya ganin laifi ko illar hakan, domin be shiga tsakanin Emily da Turhan da nufin bata tsakaninsu ba. Ganimar da ta biyo baya tsakaninsa da Emily kuma wani nauyi ne da ba zai saukewa daga zuciyarsa ba, kamar yadda be isa ya kaucewa kaddara ba, domin haka ya shirya bawa zuciyarsa salama da abun da take laso masa da halshen wuta mai zafin gaske. A tunaninsa kamar Emily ba zata karbe shi ba a yanzu ba ko nan gaba, be sani ba ashe ya gama cinta da yaki, a yanzu ikon garin nasa sai yadda ya juyata. Ya rike wannan a matsayin hujjar da zata hana shi cin amanar ko hana cikar burinta. Bayan La'asar Ummi ta saka direba ya kaita gidansu Mama Baraka. Emily ta shiga tana jin bakonta domin har yanzu bata iya sake jiki kamar gidan Ummi ko gidanta. A falo ta zauna kanenta na fadar ta shiga ciki Mama Baraka tana dakinta, ita kuma ta ki ta zabi zama a falon har sai da dayar ta shiga ta sanar mata, sai gata sun sauko tare da wanda ta shiga kiranta ta karaso inda Emily take zaune tana farincikin ganinta gidan. "Sannu da zuwa? Sun ce ki shigo ciki baki shiga ba why?" "Zan fi jindadi idan ke kika sauko" "Eh amman dai nan ai gidanku ne, ki sake jiki ki yi yadda kike so Aisha" Ta daga kai sannan ta gaishe da mahaifiyarta. Mama Baraka ta rumgume tana amsawa, sannan ta tambaye ta ina su Ummi, Emily ta amsa suna lafiya. "Ita ce mace na zo na nemi izini a gurinki, jibi za su tafi Abuja saboda can suke zama daman, ta ce na tambaya idan za ki aminta za su tafi da ni" Mama Baraka ta kai hannu ta dafa hannun Emily tana murmushi. "Tafiyar ta tashi ne? Ummi ta yi kokari matuka kuma ta kyautata na jidadi, sai dai hankalina zai fi kwanciya idan kina tare da ni, na yi ta son na samu lokaci na kasance da ke ban samu ba, saboda kin fi sha'awar zama a can, idan nace zan amince na barki ki tafi tare da su, na cutar da kaina, kuma babu wani lokaci da za mu samu mu kasance a tare" Emily ta sauke kai kasa alamar bata jidadin maganar Mama Baraka ba. "Ki yi hakuri Aisha, amman ban amince ba ina son na kasance a tare da ke, shiyasa nake shirya komai na barin gidan domin na san ba lallai zaman yayi miki dadi ba, be zama lallai ki sake jiki a nan ba saboda Kameela ko Hajiya, amman za mu koma gidana da na siya ki saba da kanenki su ma su saba da ke, ki yi hakuri dan Allah ki fahimce ni" Emily ta daga mata kai sai ta mike tsaye a take. "Zan koma, daman na zo na ji ta bakinki ne" Mama Baraka ta kalleta cikin rashin jindadi sannan
Chapter 154 · 0% Book details