Sashe 38
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Yadda ta tafi a kafa haka ta dawo a haka feeling so lonely and hopeless. Ta kwankwasa gate din aka bude mata ta shiga, ganin bakuwar mota ya saka ta juyo ta kalli mai gadinta kamar zata tambaya waye sai kuma ta fasa, ta nufi main door din da sauri zuciyarta na raya mata wata kila Aliyu ne ya rigata iso gidan, sai dai hango direban Vito da ta yi a gaban motar ya sauya tunani, ta tura kofar falon ta shiga, sai ta samu babu kowa a falon sai wata bakuwar fuska da ta yi arba da ita a zahiri, a badini kuma mace ce da ta sha ganin hotonta a wayar Vito da kuma gidansa. "Da alama ke ce Emily" Matar dake tsaye a dinning din falon ta fada tana kallon Emily da murmushi a fuskarta. "Barka da sauka Mrs Gloria" Cewar Emily tana kallomta fuska babu yabo ba fallasa. "Vito ya fada miki wacece ni a gurinsa kenan" "Na sha ganin hotunanki a wayarsa da gidansa" "Kamar yadda ya cika ni da labarinki" Tana maganar tana nufo gurin da Emily take tsaye, ta kama hannunta suka zauna. "Fatan na same ki lafiya, ya yaranki" "Duk muna lafiya" Ta kai hannu ta rike fuskar Emily. "Ke kyakkyawa ce, kina da aji amman ba irin kyaun da za'a ce babu wata macen bayan ke ba, ana yana kaunarki sosai kin jama lu'u-lu'u a zuciyarsa, a duniyarsa kuma kin zama numfashinsa wanda yake jin kamar idan ya rasa ki ya rasa rayuwarsa gaba daya" Ta shafa fuskar Emily. "Kin canja rayuwar ana, a da babu ruwansa da mace ko wace kala ce, be taba min zancen budurwa ba, ban taba ganinsa da wata ba, idan ma na yi masa ransa baci yake, be taba soyayya sai akanki, ada baya tsoron aikata kowane kalar aiki ko jefe kansa a hatsari, amman sanadin ki a yanzu yana tsoron shiga matsala, ya kan ce min idan wani abu ya faru da shi ya zaki yi? Wa zai kula da ke da yayanki?" Emily ta sauke kanta kasa tana hade yawu. "Amman kin san danki yana siyar da kwayoyi? Drugs" Mrs Gloria ta yi murmushi. "Na sani, wannan sana'ace da ya gada tun daga gurin mahaifinsa, kamin a kashe shi, kar hakan ya dame ki, amman ki yi taka tsantsan da zuciyarsa, ba saboda ke ba saboda wadanda suke tare da ke" Ta mike tsaye. "Be san na zo nan ba, karki sanar masa. Na barki lafiya" Emily ta bita da kallo har ta fice, ta sauke ajiyar zuciya ta jingina da kujerar, ta daga hannunta tana kallon agogon dake hannunta ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin Jakarta da wayarta dake ciki ke sanar da ita isowar sako. Ta ciro wayar ta duba sakon da shigo daga number Aliyu even though bata yi saving number ba, amman ta gane number shi ce domin sakon yana a saman wacan sakon da ya turo mata a ranar da suka hadu asibiti. "Mahaifina dan siyasa ne, sau hudu yana tsaya takarar dan sanata amman be taba yin nasarar ba sai bana" Ta karanta sakon ta sake karanta sai ta aika masa da quation marks, like why are you telling me this? Ta tashi ta nufi dakin da danta yake tana ta mamakin dalikinsa na bata tarihim mahaifinsa ba ma nata ba, tana tura kofar dakin sai ta same shi tare da Fatima da Chidimma suna ta wasan doki cikin far'a da sakewa, sai da ta fara kawata fuskarta da murmushi sannan ta karasa cikin dakin ta shafa kan London a take ya hade rai ya matsa gefe, bata damu ba ta shafa na Fatima sannan ta karasa kusa da shi ta zauna a kasa. "My handsome Man" Kamar jira yake ta rufe baki sai ya saka mata ihu da sauri ta tashi daga gurin ta matsa. "Baya bukatar ganinki ne a yanzu, da dai zaki yi hakuri ki fita saboda muna wasa a yanzu kar a bata masa rai, mu wuni a damuwa" Ta daga ma Chidimma kai cikin rashin jindadi ta fice daga dakin, ta shiga nata dakin ta aje jakarta da duk wani abu da yake hannunta ban da wayarta da yake karanta sakon Aliyu da ya shigo mata yanzu. "Wata rana a Kaduna ranar 20 ga watan march 2020 aka ina tare da friends dina a inda muka saba haduwa mu yi shawara ko wani abu mai amfani, a ranar muna kallon tv ne a lokacin ake sanar da sakamakon zabe wanda mahaifina ya tsaya a karo na hudun kuma karo na karshe a rashin nasararsa, aka sanar cewar ya fadi kamar kowace shekara abokin hamayyarsa yayi nasara a karo na hudu, daman shi ya saba yi nasara a duk zabe" "Miye alakata da zaben mahaifinka?" Ta aika masa da tambayar domin har yanzu bata fahimci inda ya dosa ba, ya aiko mata da murmushi sai kuma wani sakon. "Na ji babu dadi sosai, abokaina suka karfafa min guiwa, muna haka sai ga mahaifiyata ta kira ni cewar mahaifina yana ciki wani hali na damuwa saboda faduwa zaben da yayi, na yi hanzarin barin abokaina na shiga motata domin tafiya karfafawa mahaifina guiwa kasancewata namiji daya tilo da ya haifa a cikin yayansa mata, a hanyata ya tafiya aka fara ruwa daman hadari ya gama rufe garin kaduna a wacan lokacin... A hanyata ta tafiya na hango wata mata tare da danta sun fake a wata kazantaciyar tumfa, yana daya daga cikin halina taimakon mai rauni a duk lokacin da na samu hali, and it does not matter if musulmi ne ko ahalul kibat, a nan na gagara wucewa na matsa kusa da inda matar take na faka motata na fita sai na same ta tana ihu da dukannin karfinta, ashe nakuda take a gurin tana dauke da tsohon ciki ne, ga kuma danta da ya kasance marar lafiya, "Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?" Haka na jera mata tambaya ina leken fuskarta, sai ta kalleni amman bata iya magana ba sai dai ta kalleni a lokacin ta mika hannayenta ta riko hannuna. "Subhanallahi... Christen ce ke?" Na tambaya domin na lura da sarkar cross din dake wuyanta, sai na yi cire hannuna hannayenta, a kokarin yin haka agogon hannuna silver color ya zame ya tsaya a hannunta, sai ta jimke agogon tana cizon baki tana nishi mai karfi alamar tana jin zafin ciwo, hakan ya saka ban yi yunkurin karbarsa ba. "Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?" Na sake tambayarta sai ta girgiza min kai alamar aa, "Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan..." Na tambaye ta, kamin na dagata na sakata a motata ina istigifari. "Allah ka yafe min wannan ba da niya na aikata ba" Na saka danta na tuka motar ina tafe ina mata sannu har muka isa asibiti, na bada damar ayi mata komai a cikin aljihun familynsu domin asibitin da na kaita kamar ta gidanmu ce, a nan na barta na tafi gurin mahaifina, bayan na dawo sai a aka samu bata dakin da aka aje ta ta gudu ita da yar da ta haifa da danta kamar yadda suka fada min, tun daga ranar ban sake ganinta ba, abun da kawai zan iya tunawa a game da ita ita wacan tana da jiki fara ce sol kamar baturiya, tana jan gashin kai da blue eyes. Fatan kin isa gida lafiya... Ta lumshe ido hawaye na cika fuskarta, jikinta kuma yana ta bari mazari, abun da ya rubuto mata a yanzu shi ne abun da ya faru a wacan lokacin da ta rike a zuciyarta saboda taimakon da yayi mata har ta rayu ta kawo labari yanzu... ALIYU POV. Ya dago daga jikin karfen dage gabansa yana slipped tea dake hannunsa. Mamaki yake yadda time yake gudu kamar jiya komai ya faru amman gashi yanzu lokaci yaja. Yayi murmushi at least ya ceci rayuwa har biyu, ta Emily da kuma Fatima, sai a yanzu yake mamakin kansa na rashin ganeta da be yi ba tun farkon ganinta, ko da yake kamaninta sun sauya yanzu, a baya tana da jiki yanzu kuma babu yanzu ta zama yar kwalliya ba kamar so acan karon da ya ganta ba. Sai dai ko a lokacin da yake ganinta a gurin aikinsa yana ji a jikinsa kamar ya santa ko ya taba ganin wata mai kama da ita, ashe ma matar abokinsa ce ya taimaka a wacan karon kuma yar abokinsa ce ta ceto... "Subhanallahi" Ya fitar tare da iskar bakinsa, amman taya Turhan ya bar har ta fada a wannan halin dauke da cikinsa? Lallai akwai alamar ta tayu da kalubale a zamansu, shiyasa ta yi ma yarta karyar cewa bata da mahaifin, kuma take gudun ya dawo rayuwarta a yanzu. Ya dago wayarsa ya fita daga sashen sakon ya shiga sashen kiran waya ya kira matarsa yana jin cewar shi kam sam ba zai taba iya wulakanta matarsa ba kamar yadda Turhan yayi. Wayar na daf da tsinkewa ta amsa cikin wata murya dake bayyana damuwarta. "Salam..." "Hello Dear, yanzu nake son na kiraka na san ranka ya bace dan Allah ka yi hakuri da abun da ya faru" Yayi jimmm domin be san da faruwar komai ba. "Me ya faru?" "Kayan da aka kawo ne Hajiya ta sa aka maida wai yayi kadan" A take fuskarsa da zuciyarsa suka rikedewa zuwa bacin rai. "Kameela ya kamata ace muna lurar da iyayenmu inda ya kamata su kyautata ko su daga kafa, Ina sonki kin sani amman duk wani abu da zai munanawa iyayena ko ya zama cin mutunci a garesu ba zan jure ba, ban san Ummi ta aika miki da kaya ba sai da kika kirani dazun kika fada min, na kira na yi mata godiya, ban san komai akan al'adar haihuwar mace idan a ya zo ba rai ba, duk abun da kika gani kokarin Ummi ne, ina son wannan abun ya zama na karshe" "Yadda kake son iyayenka kake gudun bacin ransu haka nake gudun nawa, ai kasan dai ba zan taba bada go ahead akan amai da kayan da har kiranka na yi