← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 177

Sashe 21

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da tunani biyu, mutumen da ya gani dazun da kuma kukan da Emily take, kokarin hada biyun yake yaga yadda za su zame masa daya ko zai samu amsar kukanta, sai dai zuciyarsa bata natsu da hakan ba. Yadda ya bukata haka maganer hotel din ya aiwatar aka daukar masa shatar jirgi private jet shi kadai daga Lagos to Port harcourt, tun kamin ya bar Lagos ya turawa direbansa dake port Harcourt sakon lokacin da zai sauka, so that ya zama cikin shiri. In less then awa biyu ya sauka Lagos daman daga Lagos to Port Harcourt 1hr 10m ne to nonstop flight. Yana sauka direbansa ya dauke shi a cikin 2022 -BMW X3 baka mai bakin gilashi. Be sauka ko'ina ba sai gidan Emily, yana fitowa motar be tsaya rufewa ba ya nufi kofar shiga falonta da saurinsa irin saurin dake ake hadawa da guda, a falo ya fara cin karo da Fatima tana zaune a dinning tana shan cornflakes, kallonta kawai yayi ya dauke kai ya kalli wayar Emily dake aje kan kujera da jakarta, be taba komai ba ya haura sama ya tura kofar dakinta a hankali ya shiga. Talkaminsa ya fara cirewa sannan ya taka ya karasa bakin gadon yana kallon fuskarta a take zuciyarsa ta fara rawa ganin yadda fuskarta ta yi ja ta kumbura saboda kukan da ta yi, idanuwanta a lumshe tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take irin na yaran da suka gaji da kuka suka yi bachi. Zaunawa ya fara yi a hankali sannan ya kai hannunsa ya dagota ya kwanto da ita a jikinsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, jira kawai yake ta farka ta fada masa wanda ya saka kyakkyawar sarauniyarsa kuka. Jin ana shafa fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali ta sauke su akan fuskar mutunen da murmushi ba shi da muhalli a gurin. Ta tashi zaune tana kallonsa sai na juya ta kalli gadon ta kalli agogo ta ga karfe biyar na yamma ta sake kallonsa. Yaushe ka zo? Ya ki ya amsa sai kallonta yake. Kace min zaka tafi Lagos? I thought kana can Nan ma be ce mata komai ba sai kallonta yake. Why are you here? Ya saka yatsansa ya shafe mata gefen bakinta. Waya taba ki? Kallon fuskarsa take zuwa kirjinsa da boturan rigar suke bude, sannan ta sake kallon fuskarsa sai ta fashe da wani sabon kuka. Kowa baya so na, babu mai bukatata a kusa da shi, Fatima tana bata min rai yau sauran kadan mota ta bugeta saboda ta bata min rai, na tafi asibiti London yace baya so na ya tsane ni Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta tare da dora chin dinsa saman kanta. Sai kuma wa? So yake ta ambata masa sunan wani dabam ba yayanta ba tace su suka bata mata rai, domin ya san ba zai iya taba yayanta ba, amman zai iya taba kowa bayan jininta. Ita kuma bata yarda sunan kowa ya fito daga bakinta domin ta san waye Vito ta san abun da zai iya, kuma ta san yadda yake sonta. Ya dago ta daga jikinsa ya rike fuskarta da hannunsa biyu yana kallon kyakkyawan idanuwanta. Akwai wanda ya taba ki bayan Fatima da London? Akwai wanda ya fada miki wata magana? Ta girgiza kai alamar aa, ya mutsa bakinsa kamar zai yi magana sai kuma ya saketa ya mike tsaye, kasa ya sauka ya shiga kitchen ya dauko mata ruwa ya fito har ya nufi stairs ya fara takawa sai kuma ya juyo ya dawo gurin da fatima take zaune a dinning ya kalleta. Idan kika sake batawa mahaifiyarki rai har ta yi kuka idonta ya kumbura kamar yau, sai na miki danyen hukunci Ya fada fuskarsa babu alamar wasa sai ma kara hade mata rai da yayi. I hate you, kuma Momy ba zata aureka ba Ta fada masa cikin tsiwa tana murguda baki. Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya dauke kai ya haura sama. Tana ganin haka ta mike tsaye ta nufi wayar mahaifiyarta ta dauka ta haura sama da gudu ta shiga dakinta, jakar makarantarta ta bude ta dauko kati da Aliyu ya bata ta zauna bakin gado tana cire password din wayar. ALIYU POV. Misalin karfe 3pm ya faka motarsa harabar gidan ya bude ya fito yana kallon bakuwar motar dake fake kusa da balcony. Bayan ya rufe motarsa ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Matarsa ya tarar a tsaye tare da wata bakuwar fuska dake rataye rike da karamin mayafi a hannu dayan hannunta kuma rike da jaka. Aisha na ganin shigowarsa sai hankalinta ya tashi, ta juya ta gefen da bakuwar take tana tarewa dan kar Aliyu ya kalleta da kyau, domin atamfar dake jikinta da matse ta sai dai ba sosai ba, amman ta karbe ta yi mata kyau. Ta inda ta yi sa'a mijinta baya daga cikin irin mazan nan da suke son kallon mata balle kuma ya san halin matarsa da kishi ko a tv ya kurawa mace ido sai ta yi masifa balle kuma a zahiri, tun kallon farko da yayi ma bakuwar a farkon shigowarsa be sake kallonta ba. Sannu da zuwa Sannu Babyna ya gidan? Lafiya Kalau Yayi kamar be san da bakuwar ba ya shafa fuskar matarsa zai wuce sai ta gabatar masa da kawarta tana dan kareta. Tasmia ce ta zo mana Maa Shaa Allah, ina mata barka da zuwa Ganin alamar be gane ta ba ya saka ta ce. Tare muka yi Secondary School Nice Ya fada ba tare da ya kalleta sannan ya wuce zuwa dakinsa, tun da ya bada baya Aisha take kallon Tasmia ta ga ko ta kalli mijinta and yes ta kalleshi da kyau har ya shige ciki, Aisha ta dan canja mata fuska tare da jefa mata zagi cikin wasa sai dai har a zuciyarta ta ji zafin kallon da ta yi ma Aliyu. Yar iska me kike kallo? Da wani billenki a nan Tasmia ta kalleta ta yi murmushi. Masu ciki fa zuciyarsu a kusa take, daman gaki ba tsaye kin san ance short people suna da saurin fushi, wai su da fushi 5&6, ni kin ga tafiyata Ta nufi kofa, Aisha ta tsaya a gurin bakinciki ya hanata raka kawar da suka shafe shekaru ba su ga juna ba, sai ma binta da ta yi da harara. Aliyu na shiga dakinsa wayarsa ya fara cirowa ya aikawa Turhan da sako bayan ya gama karanta wanda ya turo masa. Yau gidan marayu hudu muka je ba mu dace ba, ko'ina cewa suke ba su santa ba Baka amsa ni ba, Turhan me ya rabaka da yarinyar nan? Me yasa ka sake ta? Ya aika masa sannan ya aje wayar ya fara cire tufafinsa. [4/20, 9:59 AM] : https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w ABOKIN RAYUWA
Chapter 21 · 0% Book details