← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 177

Sashe 46

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na karba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace. "An daura aurena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kawo amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce" Ina daga zaune na daga kai na kalleshi. "Ba zaki ce komai ba" Bance masa komai ba bayan kallonsa da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu. "To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data rike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba" Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe... Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Kuma karku manta ku yi sharing [5/4, 6:26 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA
Chapter 46 · 0% Book details