← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 177

Sashe 49

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 2 Da gari ya waye sai na yi ta raba ido a cikin tashar ina kallon mutane, daman na kwana a kusa da massalaci ne a wani guri da ake aje sako tare da wasu matafiya da dare yayi musu. Na zauna a gurin har zuwa karfe daya na rana saboda ban san a inda zan je ba, ba zan iya komawa lagos ba idan ma nace zan koma ba ni da kudin motar idan kuma na koma ba ni da tabbacin a karbe ni. Jama'ar gurin da suka lura ina zaune a gurin har ana daf da ayin la'asar sai suka same ni suna tambayar na san a inda nake kuma wana sani a garin Kaduna? Nace musu na sani kuma bani da kowa a garin kaduna. Sai suka tambaye ni ni matar aurece? Nace musu aa domin a halin da nake ciki babu aure a tare da ni, idan ma akwai vana bukata domin na gama kakkabe Khaleefa a rayuwata yanzu, sai kuma suka sake min wata tambayar da na rasa amsar da zan ba su. "Toh cikin dake jikinki fa?" Na shafa cikin ina hade wani abu mai daci, dole kowa zai yi zaton cikin shege ne, wata kila su yi tunanin ko na gudo daga gidanmu ne. "Dan Allah inda ake bada taimaka idan mutum yana cikin matsala?" "Kamar wani irin taimako?" Dayan ya tambaya. "Kamar wata kungiya ta musulmai da take bada taimako haka ko masallaci" "Toh sai zakka da wakafi" Dayan kuma yace na tafi massallaci, wani kuma ya tambaya wani irin taimako nake nema, na ce na wanda zai rike ni har na haihu. "Wannan cikin ba shi da uba ne?" "Yana da uba, ni ba ni kowa marainiyace ni, kuma mijina ya sake ni, kuma musulunta na yi ban san kowa a nan ba" Ina rufe baki daya daga cikin dattijan dake tsaye a gurin ya rufe da fada kamar zai dake ni. Wai na tashi na bar gurin haka muke muna zuwa muna cikin shege mu zo tasha mu tare muna haifa musu yara yan iska muna bata musu tasha. "Idan baki da kowa ki koma garinku mana, karya ce suke saboda kawai a tausaya musu, cikin shege suke yi" Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, daman wai waye zai yarda da ni, suna da gaskiya suna bukatar tabtace tashar su. Haka na tattara na bar tashar na fito na kama hanya ina tafiya ban san inda zan je ba, can na samu guri kusa da wata mai wara na zauna na siya wara na ci saboda ban saka komai a cikina ba tun safe. "Dan Allah ina ne? Zakka da wakafi?" Ba tambaye ta, sai ta kwatantamin na bata kudin wararta na siye ruwan leda na sha, na tari mai achaba na hau na fada masa inda zai kaini ban tambaya nawa ba sai da muka isa yace min 500 zan bashi a lokacin 2300 ne suka rage min, na ba shi 500 na doshi gurin gabana na faduwa, domin maraicina be taba saka ni rokon kowa ba. Mai gadin gurin ya fara tambayar ina zanje na fada masa taimako nake nema a take na bayyana masa abun da ke tafe da ni da kuma taimako da nake bukata. "Kin tabbatar cikin nan baki ba na shege ba ne? Domin suna yin bincike idan za a bada taimako" "Wallahi gaskiya ne, ba karya nake ba" Sai yace na jira a nan ya shiga ciki ya fito da wani mutum mutumen yayi min tambayoyi ya yi rubutu akai sannan yace min yanzu kowa ya tashi aiki saboda yamma ta yi, amman na tafi zai saka sunana a cikin mabukata na dawo wani sati, sannan ya tabbatar min kamin su bada taimako suna yin bincike saboda akwai bata gari da suke zuwa suna karya nace masa na yarda su yi duk abun da ya kamata. "Amman yanzu idan na tafi ba ni da gurin zama ban san a inda zan zauna ba" "Ki yi hakuri dai wani satin ki dawo da wuri kamin rana ta yi" "tohm" Na amsa ina kuka, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi naira budu daya ya ba ni wai na hau abun hawa. Na karba na juya na kama hanya daman kam wa zai karbe ni a haka dole kowa zai yi zaton karya nake saboda cikin dake tare da ni ga shi kuma ina fadar ba ni da kowa kuma nace ban san kowa a garin Kaduna ba, ga ina cewa musulunta na yi wasu ma sai su dauka karyar ma ta yi yawa. Daga gurin na kama hanya ina ta tafiya a kafa ba dan na san inda zanje ba, har dare ya fara yi na siye ruwan leda na yi alwala na raba gefen wani icce dake kan hanya na yi sallah, ina addu'a ina kuka ina rokon Allah ya kawo min mafita. A gurin na yi ta zama har aka yi isha'i a nan ma na yi sallah. Da yake akwai mai shayi nesa da inda nake zaune kadan da na yi yunwa ta matsa min sai na tafi na siya birede da ruwan lipton na koma gefe daya na sha, sai wani azababben ciwo ya taso min, da na kawo masa kofin kowa kallon wulakantacciya yake min domin mace mai daraja ba zata saya tea ta raba gefe ta sha ba, gashi na zama kamar mahaukaciya duk na firgice ga rama cikin ma yayi min nauyi haka dai nake ta fama. Da na bashi kayan sai na raba ta wata hanya dake kusa da shagon na bi na lulla da wasu kananan gidaje, a gurin na samu inda na raba. Na wahala a gurin domin ciwon ba kadan nake jinsa ba, sai da na bari sawu ya dauke na tabbatar da dare yayi sosai sannan na tashi na koma inda na fito yadda na ayyana haka na samu. Mai shayin nan ya tashi ya kwashe kayansa a gurin na kwana, washe gari tun da asuba na yi sauri na tashi na koma gurin hanyar na zauna, da haske ya fito sai na shiga wani gida dake kusa na roki ruwa dattijiwar ta ba ni na yi alwala na fito nan na yi sallah. Rayuwa ta zama min haka, da dare sai na kwana a shagon mai shayi da rana kuma na shiga gari Bara da neman taimako. Ta inda Allah ya taimake ni babu wanda ya taba cewa me nake a gurin ko ya kure ni, ko da yake bana dawowa gurin sai dare yayi, idan kuma sawu ya dauke sai na kwana a shagon mai shayin da be san ina yi ba. Ranar da na kwana uku a gurin ciwon ya matsa min sosai har na tafi yawon bara na dawo na shiga gidan matar dake bani sadakar ruwa ina ta gumi na roki ta ara min wayarta na kira wata nu mber. Har tace min bata da waya na juya sai kuma ta kira ni ta ba ni amman tace na zauna a kusa da ita na yi wayar bata yarda na fita ba kuma ta saka wayar a speaker saboda bata yarda da ni ba. Na warware zanena na dauko number Maman Luratu na saka a number na kirata, babu jimawa tana ringing ta daga wayar da sallama Maman Luratu nice Aisha ce" "Aisha Allahu akbar sannu Aisha ya kike ina kike yanzu" "Ina wani guri, maman luratu dan Allah ko kin san abun da zan yi na daina jin ciwon cikin da baya? Wallahi ciwon nan ya tsananta min yanzu sosai yau ma kamar bana iya tafiya" Ina fada ina kuka. "Toh ko haihuwarce? Amman cikin ai be isa haihuwa ba ko?" "Eh wata bakwai ne, amman ina jin wahala sosai" "Ko nakuda kike yi? Oh Allah gashi bana kusa, amman dai ki daina yawo nesa" "Idan haihuwar ce me zan yi?" "Kina tare da wa ne?" "Babu kowa ni kadai ce" "Ki nemi reza ki aje kusa saboda yanke ciki, kuma idan da hali ki tafi asibiti Aisha kin san baki da lafiya tun a nan ma" "Tohm" Na amsa sannan na kashe wayar na mikawa matar ina godiya, sai matar ta tambaye daga ina nake. "Labarin mai tsayi ne ko na fada miki ba zaki yarda ba, na gode" Na fice daga gidan ina ta sharar kwallah. A rabar ne zuciyata ta debeni na yanke shawarar ziyartar coci ba dan komai ba sai dan na samu kudin da zan tafi asibiti kuma na samu kulawa. Dan canjin da ya rage min na hau abun hawa bayan na tambaye shi wace coci ce a kusa na fada min, da muka isa na bashi kudinsa na doshi gurin gabana na faduwa a zuciyata ina jin kamar hakan ba daidai ba ne amman ya zan yi? Dole ce ta saka. Na isa gurin na yi magana da mai gadin coci na fada masa damuwata da abun da ke tafe da ni, sai yace na jira a gurin ya shigo ciki ya fito da wata Sister tace ba shigo ciki na shiga nayi mata bayanin damuwata sai ta kira wani pastor shi ma ya kira wani muka shiga wani office na sake karanta musu damuwata, da na yi hakan ne saboda kawai su taimaka min. Sai dayan yace za su taimaka min da gurin zama da abinci amman sai idan zan yarda na koma gidan jiya, ma'ana na zama christen kamar baya, har ita macen take ce min ko da ace ban taba yin addinin a baya ba zan shiga a yanzu su kuma za su bani duk abun da nake bukata kuma za su shirya ni da mai rikona ma dake Lagos." ***. ****. *****. Ta daga kanta sama, Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zaro tissue ya mika mata, ta karba ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Ta kalleshi da fuskarta da ta yi ja tsabar kukan da take. "Ni na sani a yanzu ba akan shiriya nake ba, na sani ba akan daidai nake ba, na san addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, a wacan lokacin ban yarda da tayinsu ba duk kuwa da kasancewar ina cikin tsananin bukatar taimako
Chapter 49 · 0% Book details