← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 177

Sashe 165

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsadadden lace na al'adar yarbawa, Tana sanye da sakarta ta zinari da aka saka mata a lefe, wuyanta da murjani da ya sauko mata har gaban kirjinta, haka ma hannayenta, kafafuwanta da suka sha bakin lallen suna sanye da iborun, tana ta kamshin turare sai gu a ake masu, suka ta saka mata albarka da yaren na yarbanci. Aka fada mata idan zata shiga gidan ta shiga da kafar dama kuma ta yi addu'a da Bismillah. Tana zaune falon mahaifiyarta Fatima ta shigo ta ratsa mutane ta zauna kusa da ita tana ta kallon mutane, Emily ta miko hannunta a hankali ta kama hannun Fatima ta rike, idan suka yi magana da yarbanci tana jin duk abun da suke fada saboda tana jin yaren yarbanci da igbo tun a zamansu na can. Can kuma ta juya ta daga mayafin mahaifiyarta ta leka fuskarta. "Momy kin yi kyau" Ta fada tana shafa fuskarta tana murmushi, hawayen dake makale a idon Emily ya zubo mata. "Kin fi kowace rana kyau, har da lalle fa da sarka har biyu, da makeup" Emily ta lumshe ido tana murmushi, ko kadan bata yi tsammanin jin haka daga bakin yarta ba, ko da yake tun da Turhan ya saka kafa ya bar garin Fatima ta dawo gurinta daker da sudin goshi sai ta waye cikin mutane, musamman da kannen Emily suke janta a jiki. Da kuma aka fara hidimar auren sai ya zama abun ya burgeta, domin bata taba gani irin wannan auren ba, komai a gurinta sabo ne, duk abun da za'ayi ana yi da ita yana gaba gaba. Aliyu idan ya zo gidan zai zo mata da kayan dadi, ko be zo ba zai aiko a kawo mata, wani lokacin idan ya zo ita yake sakawa a sallamo yayi hira da ita ya bata tsaraba ya tafi. Yana iya kar kokarinsa wajen ganin Fatima ta sake jiki da shi kuma ta kwantar da hankalinta dan kar damuwarta ta jefa Emily a damuwa. Kusan kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya samu fiye da rabin abun da yake nema a gurin Fatima. Wadanda suka kasance iyaye ga Emily ne suka bukaci kanen su daukewa Fatima hankali ta yadda za a fita da Emily ba tare da ta sani ba. Domin suna jin lokacin da take tambayar Emily yau sabon gida za su tafi ko? Da wayo aka fitar da ita, sannan aka fita da Emily, a nan ma ta ga wata al'ada da a bata kyauta a karbi Amarya. Emily ta shiga motar tana hawayen da a yau ta tabbatar na farinciki ne. Tana zaune shiru tana saurari tafiyar har suka isa gidan masoyinta kuma Abokin Rayuwarta. An riko hannunta ta sauko motar kanta a kasa aka shiga da ita gidan da duk wanda ya ga tsarinsa da kayan da aka zuba a ciki sai ya yaba da kokari mijinta da kuma iyayenta. Bayan iyaye sun fita aka barta da kanenta da wasu daga familyn Mama Baraka da suka zama kawayenta na short period of time. Abokan Aliyu suka rako shi ya shigo falon da manyan tufafi babbar riga har da hula. Kowane yana rike da babbar leda suka cikin big center table din da kayan taba ka lashe da suka shigo da su. A nan ta san wani abu siyen bakin amarya, abokan Aliyu suka siye bakinta da kudi mai kauri da siyayya da, sun yi farinciki sosai domin ba su bar gurin ba sai da kowa ya ji saukar alert. Sai da kowa ya watse Aliyu ya rufe kofar sannan ya yarda ya bude fuskar matarsa, sannan a hankali ya yaye duk wani abu dake jikinta ya rage daga dankwalinta sai lace ne kadai, har sarkar cire mata yayi saboda yana ganin kamar sun mata nauyi, ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta sannan ya cire abun hannun ya aje, ya sauko kasa ta zauna ya daga kafarta abun adon dake kafarta ya cire bayan ya sumbanci kafar sannan ya aje ta a hankali, ya dago dayar ya cire ya sumbance ta ya aje kasa. Ita kanta ta ji a jikinta jumma'ar da zata yi kyau, tun daga laraba ake ganewa, Aliyu ne kadai Jarumin dake tsoron tana jikinta saboda gujewa tsallake iyakokin da musulunci ya gindaya musu. Har bayan aurensu, be taba kokarin taba jikinta ko wuce gona da iri saboda ta zama mallakinsa ba, kamin ranar yau idan ya rumgume ta ko ya sumbance to ya fahimci tana cikin damuwa ne sai yayi mata haka saboda ya kwantar mata da hankali, shi ma yana kokarin ganin be tsallake iyakoki ba duk kuwa da ya san halalinsa ce tun da an daura musu aure. "Abar kauna? Komai na ki yayi kyau" Ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta, kunyarsa da take ji a yanzu ta fi wanda ta ji a washe garin ranar da aka daura musu aure. Kafarta daya ya daga a hankali yayi mata chakulkuli, ta motsa kafarta murmushi ya cika fuskarta kunya ta saka ta rufe idonta. Yatsansa ya saka yana bin layin lallen da aka zana mata a kafa a hankali kamar mai zanen yana kallon kai kace be taba gani lalle a kafar mace ba. Har sai da ta kasa jurewa ta hanye kafarta. Sai yayi murmushi ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje ya zauna kusa da ita, ya juyo da fuskarta ta fuskance shi. "Qalbi, bude idonki ki kalli mijinki, masoyinki, mallakinki abokin rayuwarki na har abada, mijin da yake jin ya fi kowa sa'a da rabo saboda ya same ki" Ya kara matsawa kusa da ita sosai har jikinta yana taba na shi. "Kin san me, uwar a? Tun daga ranar da kika shigo rayuwata, komai ya canja. Na rasa yadda zan bayyana, amma ke ce farin cikin zuciyata. A duk Lokacin da na gaji, sai murmushinki ya bani arfi. A duk lokacin da na shiga damuwa, sai kalamanki su zama shauki da nutsuwa a raina." an janyo hannunta ya ri e, yana tana saman yatsunya, ya ci gaba da cewa "Kin fi zinari daraja a wurina, kin fi dukiya ima. Wallahi idan na dubi idanuwanki, ina jin kamar na mallaki duniya baki aya. Ke ce zuciyata, ke ce abokiyar tafiyata har arshen rayuwata." Emily ta bude ido tana jin da in maganganun a zuciya, kowane harafi yana tsarata ya isar mata da sako. Ya saka karamin yatsansa cikin nata irin yadda yara suke yi. "Na yi alkawari ba zan ta a barin ki, ki ji ka aici ba. Zan kasance tare da ke cikin farin ciki da bakin ciki. Domin soyayyarki ita ce hasken zuciyata, kuma ke ce sarauniyar gidana" Hawaye ya sauko mata ya saka yatsansa ya share mata, ya sakar mata murmushi mai taushi ya girgiza mata kai alamar no more tears, ya kwamto da ita kirjinsa yana shinshinar gashin kanta dake kamshi. Slowly and slowly ya dago kanta ta kalli saitin idonsa ya sauko da fuskarsa sai ta lumshe ido tana jin sanyin lips dinsa a saman nata lips din, kamin ya raba lips din gida biyu ya saka nasa a tsakiya. Wani sako mai nauyi da mai wuyar dauka ya aika mata mata ta tsakanin bakinsa da nata, a lokacin da ya cire bakinsa cikin nasa sai ta kalleshi a rikice tana maida numfashi, sai kuma ta lumshe ido ta yi murmushi ta maida kanta kirjinsa tana mai jin kunya. Sun samu lokaci a haka sannan ya tashi dauro alwala ita ma ta yi suka yi sallah, yayi musu addu'a, ya dauko abun tabawa ya ciyar da matarsa, sannan sauya tufafin jikinsa zuwa ma bachi, ita ma ta sauya nata bayan ya bata guri ya fita falo har sai da ta gama sannan ya dawo. Abubuwa da Emily bata saka ran Aliyu ya sani ba, ko ya iya ta gansu, bata yi zaton zai zo mata a haka ba, saboda yadda take ganinsa da kokarin kawarda kai. Kusan duk wani abu mai sunan damuwa sai da Aliyu ya matar da ita a daren, har take jin kamar ita ce ta kwashe kason jarumin namiji, ta rika jin kamar bayan Aliyu babu wani namiji mai halayya da dabi'un da ya rage irin nasa. A kirjinsa ta kwana har safe, ba kuma a daren kadai ba, a kowane dare bayan daren tarewarta tana kwana a kirjinsa ne, idan yana gidan da rana kuma tana sarkafe cikin hannayensa, duk wani abun da zai bada space a tsakaninsu be yarda da shi ba. A nan ta gane kalmar soyayya ba a cikin kalami kadai take ba har a cikin aiki da zamantakewa. Matukar hali da hallayar da Aliyu ya sauke ta da su a gidansa zai daure, to bata jin akwai wata macen da zata fita dace ko jindadin aure a halin yanzu. Idan ya fita har kewa take, shi kan shi kamin ya dawo gareta ya yi missing dinta kamar ba a gida daya suke rayuwa ba. Awa ashirin da hudu yana jin kamar a kara musu wasu awanin domin sun masa kadan. Kusan duk wanda ya shiga gidan sai ya yaba da yadda aka gyara ko'ina kuma aka zuba kaya, sosai Mama Baraka ta yi kokari wajen ganin ta fitar da yarta kunya, kuma ta faranta mata rai, kuma kwaliyya ta biya kudin sabulu domin ta siya komai a gurin Khadeeja Candy ne. [8/31, 11:54 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 165 · 0% Book details