← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 177

Sashe 27

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

asibitin ta dauki drop zuwa unguwarsu. Har ta isa gida haushin kanta take ji meyasa ta yi ma Matar nan magana gashi ta wulakantata. Chere m, a ga m ala n'ulo nweta ego gi ugbua" Ta fada masa da yaren Igbo cewar ya dan jira zata shiga gida ta dauko masa kudinsa. "Okay" Ya amsa mata ta nufi gate din ta buga, mai gadinta ya fara lekowa ya ga ganta madadin ya bude mata sai ya bude ya fito ya nufi motar da ta shigo ya leka mai motar, hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin be taba yi mata haka ba. Me ya faru? Babu komai ranki ya dade Ya amsa sannan ya bude mata ta shiga, kamar zata yi masa magana sai kuma wata zuciyar ta hanata, dan haka ta maida hankalinta gurin manyan bakaken karnukan da suka fara kuka saboda shigowarta, ba karamin tsorata ta yi ba ganin manyan karnukan har biyar daure da sarka a harabar gidanta. Tsayawa ta yi cak tana kallonsu daya bayan daya kamin ta kalli Vito da ya fito daga cikin gidan. Baka na son kare ka sani Na sani ba saboda ke na kawo ba Saboda wa? Ya saka hannu aljihunsa ya ciro kudin da shi kansa be san nawa ba ne ya mika mata. Je ki sallami mai mota, me yasa kika dawo yanzu? Ina London? Ta kalli kudin kawai ta dauke kai sannan ta kalli karnukan. A daure suke ba za su taba ki ba Tana matukar tsoron kare, amman a haka ta jure ta shiga cikin falonta, Fatima ta zo da gudu ta tarbeta tana sanye da uniform din makaranta. Momy good morning Ta rage tsawo tana shafa kan London Morning My love Ta amsa da murmushi kadan a fuskarta sannan ta daga kai ta kalli Chidimma dake jera cups a dinning. Me yake faruwa a gidan nan Kamar na me ranki ya dade? Me yasa Vito ya kawo karnuka a gidan nan? Kuma mai gadina ya leki motar da ta sauke ni yanzu, be saba min haka ba, kuma a yanayin yadda na ga Vito da alama gidan nan ya kwana Haka ne, Sir Vito ya kwana a nan a falon nan ma, sauran amsoshinki kuma sai dai ki bincike shi, ban san amsar ko daya ba Emily ta kalleta daga sama har kasa tana kallon yadda ta saka riga da wando da suka dame mata jiki sosai suka fitar mata da halittar jiki, bata sake furta komai ba ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta, babu jimawa ta sauko rike da kudi a hannunta ta fice daga falon. Har lokacin Vito na tsaye Balcony din yana kallon gate din gidan kamar mai jiran shigowar wani, shi ma kallonsa ta yi daga sama zuwa kasa ta dauke kai ta nufi gate din. Ta bude da kanta, ga mamaki sai ta samu direban ya tafi sai wata farar sabuwar mota ce fake a baya kadan da inda mai taxi din ya faka. Ganin yadda ta tsaya kallon motar ya saka Aliyu ya bude motar ya fito ba tare da ya rufe ba ya doso inda take tsaye tana kallon motarsa, da sauri ta sauke idonta kasa wani irin fargaba da faduwar gaba suka tunkarota da bata san na miye ba, a ka'idar rayuwarta, tana iya kallon kowane kalar namiji ido cikin ido ba tare da tsoro ko jin wani abu ba, sai dai a yau ta samu kanta da kasa motsa ta balle kuma har ta ido da mutumen da yake cikin jerin mutanen da ta tsana. "Ki yi hakuri na sallami mai taxi din da kika hau ba tare da izininki ba "Me ka zo yi nan? Ya daga kai yana kallon gidan. Na zo na bada hakurin abubuwa da suka faru ne, kamar hotunan da Fatima ta tura min ba tare da saninki ba, kokarin shiga rayuwarki son sani wasu abubuwan, aje aikin da kika yi saboda abun da Amal ta yi miki... Ka daina kokarin shiga rayuwata, karka janyowa kanka matsalar da ba zaka iya hadewa ba, sanin abubuwan da suka faru ba za su kara maka komai ba face su jefaka a ramen da ba zaka iya cire kanka ba, biya kudin taxi da ka yi kuma ban yafe ba Ta juya ta fara tafiya. Ban yi da gode ba, ba jarumi ba ne ni, balle a ba ni kambu ko ayi min jinjina, na zo nan saboda wani dalili, idan ba haka ba ba zaki gan ni kofar gidanki Ta juyo ta tana son ta kalleshi sai kwarjininsa a yau ba zai bar ta ta aikata hakan ba. Taya aka yi ka san gidan nan Yayi shiru kamar mai tunanin irin amsar da zai bata. Baka yi kama da mai boye gaskiya ba, magana biyu bata dace da namiji irinka ba, kuma addininku ya hana karya ko ba haka ba? "Kokarin sanin gaskiya ko gyara kuskura bai isa ya saka na dora tubalin ginin da karya ba, saboda na faranta miki ko na burge ki ba zai saka na sabawa Ubangiji na ba Ta yi wani murmushin shedanci tana kallon wani gafe. Ku dai musulman nan idan kuna magana kamar ace zuciyarku ma haka take, aikinku dabam addininku dabam Kar ki yi la'akari da aikinmu ko kalamai, ke dai ki maida hankalinki gurin addini kawai, Williams ne ya bani addreshinki Ya amsa mata tambayarta bayan ya shimfida mata matashiya akan addininsa. Ta juyo da kyau ta fuskance shi, sai dai har lokacin ta kasa kallon wayar idonta, tana dan mamaki waye ma Williams. Aliyu ya saka hannunsa aljihu ya dauko wayarsa ta kamo hoton Williams ya nuna mata. Idan ma ya taba fadin sunansa tohm na manta, amman dai shi Williams din be san gidana ba, be san komai a kaina ba Wani tunanin ne ya zo mata. Ka yi hanzarin barin gidan nan wata kila saboda kai Vito ya kawo dog's yau, kuma saboda kai ya kwana a nan Rufe bakinta yayi daidai ta daga kan da Aliyun yayi ya kalli kofar gate din da aka bude gaba daya, Emily ta juya da sauri ta kalli gate din, a take hankalinta ya tashi ganin gogan ne a tsaye fuskarta kamar kullum babu annuri. Ka yi hanzari bari gurin nan Ta fada ba tare da ta juyo ba, kana ta saka kai ta nufi gate din da nufin shiga cikin gidan, tana isa a daidai gurin da Vito yake tsaye zata wuce shi, sai ya fisgota da karfi ya dawo da ita. Kamin ta yi wani yunkuri ya dauke fuskarta da mari mai zafi, har sai da dafe kunci hawaye ya cika idonta, sanin karamin aikinsa ne dukanta ya saka ta auna da gudu cikin gidan tana ihu, binta yayi a baya kamin ta haura entrance din ya janyota ta fadi kasa ya fara shurinta yana kai mata duka ta ko'ina. Kan kace me ta cika gidan da ihu tana kuka shi ko dukanta yake kamar an aiko shi. Chidimma da Fatima suka fito da gudu saboda ihun da take, sai dai babu wanda ya iya kawo mata agajiya har sai da ya duketa iya son ransa, sannan Fatima ta zo gurinta ta fada jikinta tana kuka, Chidimma kuma ta juya ta koma cikin gidan ba tare da rika Emily ko bata hakuri ba. Duk abun da ya faru Aliyu yana tsaye yana kallo hannayensa biyu rumgume a baya, sai a lokacin Fatima ta lura da shi, da sauri ta dawo daga jikin Emily tana kuka ta nufi gurin da Aliyun yake tsaye, sai dai kamin ta karasa mai gadin ya hada gate din ya rufe. Aliyu ya sauke numfashi a hankali ya juya ya shiga motarsa dake bude har lokacin, ya dan jima a motar zaune kamar mai tunanin abun yi, kamin ya ja motar ya juya ta hanyar da ya fito. Har ya isa gidansa ransa a jagule yake, damuwar da bata tasa ba na neman mamaye masa zuciya. Be san ya dade a cikin motar zaune ba har sai da Kameela (AISHA) ta fito daga falon ta kwankwasa motarsa sai ya sauke gilashin motar yana kallonta da murmushin da ya fi kama da damuwa a fuskarsa. Mai ciki? Lafiya ka shigo cikin gidan ka zauna a mota, kuma ga damuwa a tare da kai Ya san daman zata ga damuwar kam domin be iya sauya kansa a duk lokacin da wani abun na damuwa ya same shi, iyakar abun da yake shi ne boye sirrin damuwar tasa har sai ya samu mafita. Sanin halinta na zafin kishi da kuma saurin juyar da abu ya saka be fada mata daga inda yake ba, da kuma dalilin damuwar tasa, haka kuma ba zai iya mata karya ba, domin karya ba dabi'arsa ba ce. Kiran wayarsa ya yanke masa tunanin da yake na yadda zai kawar da maganar a gurin matarsa Kameela, kusan kamar an yi sara akan gaba ne, domin kiran da Turhan yayi masa yayi daidai a yanzu da yake neman amsoshin wadansu tambayoyi. Sanin ba zai iya amsa wayar a gaban matarsa ya saka shi daga gilashin motar ya rufe ruf sannan ya amsa wayar. Assalamu Alaikum Wa'alaikumussalam, Aliyu ya gida "Alhamdulillah, har yanzu babu wani labari ne?" Aliyu ya shiga shi tambayar ne a kokarinsa na gujewa tasa tambayar. "Babu, na yi yawo duk inda ake saka ran za a samu yarinyar nan ba a same ta, da har nace yau zan dawo gida, sai kuma mutumen da ka hada ni da shi yace na yi hakuri mu sake bincikawa daga yau zuwa gobe, idan ban same ta ba, sai na hakura "Toh ya zaka yi da Ammy? Ba dan Ammy ba, taya zan bata lokacina ina nemanta, kawai dai ina hakuri ne saboda Ammy mahaifiyata ce ba yadda zan yi, amman su ma iyayen suna shiga hakki yaya wani lokacin Wallahi Wata kila Ammy ta ji ko ta gani ko tana tunanin ka munana mata a zamanku ne, shiyasa ta gagara shiryawa da kai Kaddara ma ace hakan ta faru, amman ai ni danta ne, be kamata ta juya min baya ba a kowane condition, taya zaka fifita wani fiye da naka? Kuma tun farko ita ta cilasta min auren yarinyar nan ni gaba daya bana
Chapter 27 · 0% Book details