Sashe 163
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sannan ya tura masa da sako da wayarsa. "Ba Balarabe ne ya aureta ba, ni ne na aureta mutumen da ya janyo ta daga PH zuwa Kd, mutumen da suka yi aiki tare, wawa ka zo ka tare ni mana, miyasa kake tsoro?" Ya kalleta. "Daman na yi tunanin zai samu number duk da yake sabuwar number ce, amman mai son abun ka ya fika dabara, kuma zuciyata ta raya min yana bibiyar rayuwarki, amman yanzu an zo karshe da yardar Allah, tun da har giyar hauka ta dauke shi ya turo wannan sakon za a gano inda yake" Emily ta mike tsaye. "Kashe shi za'ayi?" A kokarin Aliyu na kwantar mata da hankali ya ce. "Aa za a dai kama shi, sai a gabatar da shi gaban kuliya saboda kar ya cutar da kowa, haka yayi miki?" Ta daga kai. "Zauna kin ji yan matana, bari na nunawa Daddy wannan sakon, kuma zan sanar da Ammy halin da ake ciki, ba lallai idan na yi magana da Turhan ya saurare ni ba, amman na san Ammy zata dauki abun serious" Ta koma ta zauna ya nufi hanyar da zata sadashi da bangaren Daddy, sai kuma ya juyo ba shi da nutsuwar barinta a falon jin yake kamar wani abu zai same ta. "Shiga dakin Nafeesa ki zauna, kuma kar kowa ya sake sallama miki ki fito ko ni ne, mai son ganinki ya zo ya same a nan" Ta sake tashi, zuciyarsa bata bar shi ba sai da ya rakata har bakin kofar dakin Nafeesa ya bude mata ta shiga. "Karki bar yarinyar nan ta fito, idan ta bata ke na sani" Ya bugawa Nafeesa warning, sannan yaja kofar ya rufe ya nufi bangaren Mahaifinsa. TURHAN POV. Ammy bata yi mamakin ganin ya dawo da Fatima ba, daman ta lura tun kamin su tafi bata son tafiyar, tun jiya tana jikin ubanta tana taya shi jimami ko abinci sai da ta ga yana ci sannan ta ci. "Shiga ciki ki yi kallo" "Dady ba zai tafi ba?" Ta tambayi Ammy dake bata umarnin. "Eh" Tohm" Ta amsa sannan ta nufi hanyar dakinta. "Fatima" Turhan ya kirata sai ta juyo, ya tafi inda take ya rumgumeta sosai yayi kissing dinta ita ma ta yi masa kiss. "I love you" "I love you Too Dady" Ya sake ta yana murmushi, ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo kusa da Ammy. "Bata yarda ta zauna can, ko magana bata yi da Emily ba" "Daman na ga alamar ba zata zauna ba" "Ni zan tafi Ammy, anjima kadan jirgimu zai ta shi" "Ba zaka bari sai next week ba" "Garin ne baya min dadi gara dai na tafi kawai, ko zan samu salama" Ammy ta mike tsaye ta bude masa hannayenta sai ta matsa kusa da ita ta rumgume uwarsa. "Jikinka da zafi sosai Turhan, baka da lafiya ne?" "Zazzabi ne kadan na ke ji" Ta sake shi tana taba fuskarsa da jikinsa. "Ba kadan ba ne, ko'ina ya maka zafi fa, gaskiya ba zaka yi tafiyar nan a yau ba" Turhan ya zube kasa ya rike kafafuwan Ammy yana kuka kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah ki yafe min, bijirewa umarninki ne ya jefani a halin da nake a yau, da ace na bi yadda kika tsara, da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da yanzu ban shiga wannan bakincikin ba" "Na yafe maka duniya da lahira, kuma damuwa Allah zai maka maganinta, Emily ba ita kadai ce mace a duniya ba" Ta daga shi ya zauna kan kujera ya rike kansa dake tsarawa. "Ba zaka tafi yau ba" Ya sauka kasa ya zauna ya dora kansa akan cinyar Ammy. Sun dade a haka kamin ya ciro wayarsa yayi canceling flight din, ko kadan a yanzu baya son ya sabawa Ammy domin ya ga illar hakan. "Zan bari sai next week" "Allah ya maka albarka, bari na dauko waya na kira Likitana" Ammy ta tashi ta fice daga falon ta shiga dakinta, tana daukar wayarta ta ci karo da sakon Aliyu daga numbersa da tuni ta goge ta a wayarta. [8/27, 11:03 PM] ABOKIN RAYUWA