Sashe 136
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 Dr A-B ya bi bayan Momy ya shiga bedroom dinta, ya zauna cikin rashin natsuwa da kuma bacin rai. "Ya aka yi suka san nan? Kuma suka san Emily tana nan?" Momy ta dube shi. "Samu sakon neman yarinyar nan ta email, waya daga wannan yaron Aliyu, kullum da kalar magiyar da yake min da rokon na ba shi dama ya zo yayi magana da ita, ya fada min Madam Barakat ce mahaifiyarta, ita kanta ta same ni da maganar kuma na fahimce ta na karanci damuwa a tare da ita sosai saboda ni ma uwa ce, and kai kanka mafita kake nemawa yarinyar ai kuma yanzu yan'uwanta sun bayyana me zai saka mu cigaba da boyeta?" "You just don't like her Momy haka ne?" "Me zai saka na tsane ta? Me ta min? Labarinta abun tausayi kamar rayuwarta, amman ba mu da wata hujja na cigaba da rike ta, kasan mahaifiyarta tana da damar ta saka kara ma akan boye mata yarinya? Balle kuma Madam Barakat ta yi min komai? Ba zai yiyu na gagara cireta daga matsala ba" Dr A-B ya mike tsaye ya taka ya juyo. "Amman baki shawarce ni ba, ni na kawo ta gidan nan akalla ta kamata ace ina da labarin abubuwan da suke tafiya akanta" "Ba lallai ita ko kai ku aminta ba, shiyasa ban fada maka ba, kuma ai ba tafiya suka ce za su yi da ita ba, magana kawai za su yi, ni kaina na dauki tsawon lokaci kamin na amince da yaron ma, daga baya Mahaifin yaron ya tuntubi mjjina akan yarinya and i can't said NO" Ya sauke ajiyar zuciya mahaifiyarsa ce ba zai iya daga mata murya ba, sai dai sam abun da ta yi masa be masa dadu ba ko kadan. Ya fito daga dakin yana kokarin boye bacin ransa ya kalli Madam Barakat da bakuwarsa ba. "Barka da zuwa Madam ya hanya?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana kallonsa kamin ta kalli Aliyu dake kofar shigowa falon tana takowa a nutse. Dr A-B ya kalleshi shi ma ya kalli Dr A-B kamar ba za su yi magana da juna ba, sai kuma Aliyu ya mika masa hannu. Dr A-B ma ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya nunawa Aliyu kujera shi ma ya zauna. "Yaya Emily take a yanzu?" Aliyu ya tambaya, Dr A-B ya fada masu yanayinta da kuma abunuwan da yake kokarin ganin ya cin ma a game da lafiyarta. "Maa Shaa Allah haka ake so, ka yi kokari mun gode sosai" Mama Barakat ta fada. Dr A-B be ce komai ba ya kalli agogon hannunsa. "Momy tace kun zo nan ku ganta ne, bari na yi magana da ita sai ku shiga ku ganta" "Already na yi magana da ita, kuma mun zo nan ba dan magana da ita kawai ba, maganar gaskiya mun zo nan ne saboda mu tafi da ita gida" Aliyu ya amsa masa, Dr A-B ya kalli Aliyu. "Bana tunanin tana bukatar tafiya wani guri yanzu, domin abun da Emily take bukata a yanzu shi ne kulawa da kwanciyar hankali" "Zamu bata fiye da abun da kake tunani Dr already mun yi booking flight in the next 40 to 1h zamu juya In Shaa Allahu" Dr A-B yayi kokarin mikewa tsaye sai ga Momy ta fito dakin ta dawo falon tana zaunawa Emily ma ta shigo falon tana tafiya a hankali. EMILY POV Mikewa yayi tsaye. "Jirgin da za mu bi zai tashi nan da awa daya, ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci na dawo gareki, wata kila kuma sa'a ce zata rabe ni ta saki ki bi ni, duk wannan ba ni da ilimi akai, sai abun da zuciyarki ta gamsu da shi" Ya juya ya fice daga dakin. Emily ta bishi da kallo har ya fita yaja mata kofar, sai ta lumshe ido murmushi kadan ya bayyana a fuskarta dake dauke da hawaye. Nemanta kawai da ya bata lokaci yayi abun farinciki ne a gurinta, gashi kuma a yanzu ya daureta da kalaman da wani be taba mata ba, ko da karya Aliyu yayi mata a yau ta jidadi domin ya nuna mata tana da muhimmanci, da ace zata iya da ta zauna Aliyu yayi ta zuwa yana dawowa ba dan komai ba sai dan waken da daya rare mata mai dadi a yau ya karanta mata shi a kullum ya zo neman Alfarma. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta nufi kofar dakin ta bude ta fita tana tana takawa a hankali kamar mai tsoron bayyana sautin takun kafarta haka ta haura sama ta shiga falon Momy, sai kuma ta yi tsaye bata karasa kusa da kowa ba. "Emily kin yi magana da wannan" Dr A-B ya nuna mata Aliyu ta kalli Aliyu da be kalli inda take ba tun da ta shigo, ta daga kai. "Ya fada miki sun zo man ne saboda su tafi da ke?" Ta daga kai. "Za ki bisu?" Ta dubi Aliyu har lokacin be kalleta ba idonsa yana kan wayarsa. Ta daga kai "Kin tabbatar kin shirya komawa?" Ta yi shiru na lokaci kamin ta daga kai. Dr A-B ya mike tsaye daman tun dazun yake da shirin tashi ya nufi kofar fita ya raba gefen Emily ya fice ba tare da yace komai ba. Aliyu na ganin haka ya san Emily ta amincewa bukatar da ya zo da ita sai ya hade yawun farinciki ya gyara zamansa ya daga ido kadan ya kalli Emily. Emily ta ji babu dadi ficewar da Dr A-B yayi domin haka ya nuna be yi maraba da tafiyar tata ba. Ta juya ta bi bayansa ko da ta shiga dakinsa Already ya zauna akan kujera and to her wannan ne karo na farko data taba shigowa dakinsa. Ta karasa inda yake zaune ta risina kasa ta dafa hannun kujera. "Ka yi fushi da ni?" Ta tambaya da wata murya gwanin tausayi. "No bani da hujjar yin fushi dake akan abun da ke kika yanka da kanki, kawai dai abun da nake tsoro ya zamana cilasta miki yayi ko kuma yayi miki barazana" "Ba ko daya, kawai ya yi rubutu a kwakwalwata ne, ya karanta min da halshen da da zan fahimta" "Kuma bana fatar ki koma ki sake fuskantar wata matsala" "Ni ma bana fatan haka" "Ko ma dai miya faru ki sani you're always welcome here" Ya mike tsaye ya nufi gurin da yake aje kayansa ya dauko card din ya nufota ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye ya danka mata. "In case of.., kuma ba lallai sai kina cikin matsala ba ya kamata ace ko da yaushe ina jin duriyarki domin sanin halin da kike ciki" "Na gode na jidadin haduwa da kai, ka taimaka min gashi ba ni da wani abu da zan biyaka" "Zaki biya idan lokacin biya yayi" Ta yi murmushi tana hawaye sai ya rumgumeta yana jin babu dadi domin zaman da ta yi a gidan ya saba da ita. "Idan kin tafi karki fasa shan maganinki, kuma ki guje duk wani abu da zai saka miki bacin rai ko damuwa" Ta amsa masa da kai tana kallon katon hoton dake tsaye gefen mirror sa kamar na cikin hoton zai yi magana. Ta dago daga jikinsa tana cigaba da kallon hoton. "Mahaifina ne" Ya amsa mata tun gabanin ta yi masa tambayar. Sai ta juyo ta kalleshi da mamaki ta sake kallon hoton amman bata ce komai ba. "Kina mamaki ne? Ni ma haka nake mamakin jin cewar Madam Barakat ita ce mahaifiyarki" Ta share hawayenta ta yi "Shiyasa nake son tafiya, akwai tambayoyin da ita kadai zata iya amsa min su. "Fatan alheri" Yayi fada da murmushi sai ta saki hannunsa tana jin kewarsa tun kamin ma ta bar gidan. Ta fito dakin sai ta sake dawowa falon Momy ta samu mai aikin gidan ta hado mata kayanta a akwaiti har hudu domin Dr A-B ya wadata da tufafi a gidan daidai gwargwado. A sanyaye ta karasa kusa da Momy ta risina kasa "Na gode da karbata da ka yi, na gode da masauki da hidima da kika yi da ni, na gode Sosai" "You're Welcome, kina jin kina son tafiya Emily?" Ta daga kai. "Okay, ga kayanki an hado, ki shiga ki duba idan baki manta komai ba" Emily ta girgiza kai domin bata son komawa dakin, ji take kamar ta yi kuka ita ma ta saba da su musamman ma DR AB dake shiga mata gaba a komai na gidan. Duk abun da ake Emily bata kalli gefen da Mama Barakat take ba ita ma kuma bata yi saka bakinta ba sai bin Emilyn take da kallo cikin yanayi marar dadi. Mai aikince ta saukar da kayan kasa aka saka a motar da suka zo da ita Aliyu yayi ma Momy godiya sannan ya mike tsaye yana kallon Emily. "Zamu iya tafiya?" Ta kalleshi sannan ta fara takawa ta wuce ya bi bayanta, da suka zo gurin sauka stairs sai ya cira kafa ya rigata sauka just to watching her steps kar ta fadi domin benen mai hawa biyu ne ba daya ba gashi hawaye take ba lallai tana gani da kyau ba. Da suka sauka kasa gaba daya sai ya bude mata kofar falon ta fita Mama Barakat ma ta fita sannan ya fita, sai da Emily ta sauka entrance din sannan ta juyo ta kalli kofar falo, bata sani ba ko zata dawo ko kuma tafiya ce ta har abada, domin kaddara tana hadata da mutane kala kala kuma ta rayu a gida mabanbanta, sai dai a wannan gidan ta hadu da mutane masu karamci da girmamawa. Aliyu ya bude mata back Seat yana tsaye yana kallonta sai ga kira ya shigo wayarsa ya dayan wayarsa, yana ganin haka ya san Fatima ce domin har yanzu wayarsa dayar tana hannun Fatima, kusan kullum sai ta kira shi tace ya bata Momy zata yi magana da ita ko ta ce ya fadawa Momy ta zo, wani lokacin zai ce Momy ta yi bachi, ko kuma yace ta yi tafiya, ta ce ya turo number ya tura mata idan ta kira ta ji kashe. Shi kanshi fargabar kiranta yake domin kuka take masa sosai idan