Sashe 169
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Kamin na dauke ta na yi magana ke, kuma alamunki be nuna min kin yarda ba, sannan na fada miki ba zan taba bari a taba ta ba, na zo da ita saboda ina sonta akusa da ni, kuma nan din ma gida ne, ya kamata ta san kowa kowa ya santa, idan tana bukatar zama a can ko nan zata zauna, amman gurin Ammy ba gurinki, Ammy ma da kanta ba zata bar ni na zauna da ita a nan ba, kuma ba zan so karatunta ya kasu guda biyu ba" "Zaka dawo da ita kenan?" "Zan dawo da ita, na yi nufin ta zauna na dan lokaci, amman yanzu tun da hankalinki ya tashi zan dawo da ita satin nan" "Na gode, tana kusa da kai" Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ta ji muryar Fatima cikin haki tana fadin "Momy?" Emily ta kara matse wayar a kunnenta. "Fatima, kina lafiya" "Lafiya kalau, Momy i miss you" "I miss you too baby, kina lafiya babu wani damuwa?" "Babu, ina yin wasan doki yanzu, Momy na iya hawan doki, Momy Zaki zo?" "Aa" "I miss you" "I know, babanki ya ce zai dawo da ke gurin Ammy za mu ga juna a can" "Okay Momy i love you, ki rika kirana kinji Momy?" "Tohm, idan wani yayi miki wani abun da baki ji dadi ba ki fadawa Babanki kinji" "Tohm momy gidanki yana da kyau" "Eh" "Mu ma nan yana da kyau" "I know, zan aje waya sai an jima" "Okay bye i love you" "I love you too" Ta kashe kiran sannan ta kalli Aliyu. "Na gode" "Anything for you" Ta kashe wayar. A ranar ta kwana da salama babu tunanin Fatima ko son sanin halin da take ciki. A kokarinsa na faranta mata kuma washe gari ya saka ta shirya da wuri ya sauke ta gidan Mama Baraka shi kuma ya wuce aiki bayan ya gaisa da ita cikin mutunci da girmamawa. After ya fice falon ne Mama Baraka ta kalli Emily tana murmushi ta ce. "Kin yi dace mijin, Aliyu ya dade yana burge ni, wani lokacin har cewa nake be dace da Kameela ba, ashe an kaddara zai rabu da ita ya aure yata ne, ya zama sirikina, ina jindadin yadda yake nuna kulawa da damuwa akanki" Emily ta yi murmushi. "Yana da kirki, ga addini" "Kusan fa duk wasu dabi'u da hallaya da ake so a gurin namiji Aliyu ya hada su, Allah yasa mutuwa ce zata taba, ga Ummi ma tana kaunarki baki da matsala ta ko'ina" "Alhamdulillah" "Allah ya datar da yan'uwanki su ma, su samu mazajen na kaurai" "Ameen, har da ke ai Mama, ko Babansu Kameela zaki komawa?" "Kai anya, ai aurena tsakanina da shi ya kare, kuma ni yanzu ba wani auren zan sake ba, kula da ku ya wadatar, sai idan na ga na aurar da duka yayana" "Allah ya nuna mana" "Ameen Ya Rabbi, kina da labarin Fatima?" "Eh..." Emily ta bata labarin abun da ya faru jiya.. "Daman Aliyu ya fada min yana ganin kamar bata nan" "Ya zo nan ne?" "Eh ya kan biyo, har alheri yake kawo min, da nake tambayarsa ya kike kuna da labarin Fatima yake fada min yana ganin kamar Turhan ya tafi da Fatima" "Be taba min zancen ba" "Ni da har na yi zaton wata kila yana jin tsoron ko kar Rito yake ki bitto? Ya cutar da ita ne da shi shiyasa Turhan din ya dauke ta suka koma can, sai yace aa ba wannan matsalar ba ce, ai Vito ya dade da mutuwa" Wani rudududun Emily ta ji kamar saukar cida, ko a mafarki bata taba mafarkin Vito ya mutu ba, bata ma taba mafarkinsa tun da ta bar gidan? "Ya mutu yaushe? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un" Ta kai tsaye numfashinta na rawa, jikinta ma haka nan da nan hawaye suka taru a idonta sai kuka. "Miye abun innalillahi a mutuwar kafiri kuma mutumen da ya addabeki? Yake neman rayuwarki data yarki da ta mijinki? Daman baki san ya mutu ba?" "Wallahi ban sani ba, Aliyu be fada min ba, babu wanda ya fada min, yaushe ne?" "Zuwansa na karshe da yayi muke wannan maganar da shi" "Miyasa suka kashe shi? Why not su kama shi su hukunta shi, be cancanci kisa ba" "Mutumen dake kashe mutane? Kuma idan yana raye ke kanki ai rayuwarki na cikin hatsari" "Kawai ya fada ne, amman ba zai iya komai ba, ba mamaki lokacin da ya turo min sakon baya cikin hayyacinsa ma, Vito ne mutumen da ya fara taimakon rayuwata, ya maida ni mutum na zama yadda nake a yau, miyasa za su saka masa ta wannan hayyar? Ban kyauta masa ba, ni ce sanadi be kamata ba" Kuka take sosai kai kace Aliyun ne ya mutu ma, daker ta iya janyo wayarta ta kira Aliyu. Jin muryarta da kuka yayi mugun daga masa hankali. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, me ya faru Qalbina?" "Me... Me... Me... Yasa kuka kashe Vi.. Vito?" "Kun yi magana da Mama ne?" "Mutumen da ya taimaki rayuwata ya so ni shi zaku kashe, ya zama kamar na ci amanar sa kuma sanadina ya rasa ransa, bayan ka yi min alkawarin ba zaka kashe shi ba" Tana kuka tana maganar. Kashe wayar yayi sai ta kara fashewa da kuka sosai tana jin silarta komai ya faru, bata kyautawa Vito ba, be cancanci irin wannan sakamakon daga bangarenta ba. Babu jimawa Aliyu ya faka harabar gidan domin yana jin kamar ba zai iya jure rarrashinta ta waya ba, ba lallai ta fahimce shi ba. Ya shigo falon babu ko sallama a lokacin Emily ta ci kuka sosai har idonta ya kumbura, Aliyu ya zauna kan kujera ita kuma tana zaune kasa rike da dankwali a hannu sai sharbar kuka take. "Na yi rarrashinta har na gaji ta ki ta yi shiru" Mama Baraka ta fada cikin yanayin damuwa. Aliyu ya kai hannu ya karbi dankwali ya rike kanta ya shafe mata hawayen. "Wallahi Wallahi ba mu muka kashe shi ba, ba ta sanadinmu aka kashe shi ba, ko da aka aje an samu police har sun dauke garwarsa da ta matar da yake tare da ita, Chidimma sun kaita gurin aje gawa, lokacin da na nunawa Daddy sakon da ya turo miki, sai Daddy yace na sanar da Turhan saboda kar wani abu ya faru tun da har ya dauka Turhan kika aura ba ni ba, kuma Fatima tana gurinsu saboda kar ayi sake ya cutar da ita, na san Turhan ba zai saurare ni ba, ko ya dauki abun da muhimmanci shiyasa na aikawa Ammy da sakon, kuma na tabbatar mata ana kan nemansa, da sakon da ya turo miki aka yi amfani da Location din sim din aka gano inda yake a Lagos, amman ko da aka tafi sai aka samu gidan a rufe da shairdar police saboda an yi musayar wuta a gidan makota suka kira police amman ko da suka zo aikin gama ya gama sai gawa suka dauka, sun turo mana komai sun mana bayani, kuma da suka zurfafa binciken sai aka gano abokan sana'arsa ne suka masa wannan aikin, ba daga mu ba ne, Ki yarda da ni Aisha Wallahi tallahi a haka muka samu shi, sun turo mana hotuna, ban fada miki ba ne saboda ina jin tsoron kar hankalinki ya tashi" Yana maganar yana share mata hawayenta da dankwalin. Mama Baraka ta ce. "Daman su irin wadannan mutane ai basa tsawon rai, saboda sana'arsu ta shadari ce suna neman rayuwar wasu ana neman ta su" "Haka ne, amman Wallahi ba daga mu ba ne" Ta kwantar da kanta jikin Aliyun da ya sauko kasa yana kokarin fahimtar da ita. Mutuwar Vito wani abu da ya tsaya a zuciyar Emily kuma ya zauna zaman da ba zai taba yiyuwa ta manta ba, daga lokacin da ta ji labarin mutuwarsa sai ya zama bata da walwala saboda tana ganin shi ma ya cancanci farinciki, ta bangaren da take jin sanyi da ya kasance ba Aliyu ne ko ita ba ce siyar mutuwarsa, da ba zata iya yafewa kanta ba. Haka Aliyu yayi ta fama da ita yana nuna mata amfanin mutuwarsa, da kuma tausaya mata har ta fara kwantar da hankalinta. Ba ma kamar ranar da Mama Baraka ta kirata ta sanar mata Ammy ta aiko da Fatima gidan Mama Baraka saboda bata san gidan Emily ba. Ammy ta yi hakan ne saboda bata son aika direbanta kai tsaye gidan Emily din ne, kuma daman bata san gidan ba saboda sanin gidan da Emily take rayuwa da Aliyu baya cikin lissafinta a yanzu. Mama Baraka ta aiko Misira ta kawo mata Fatima a ranar farinciki da far'a kamar su kashe Emily da Fatima. Sosai Emily ta jidadi da yarta bata rame ba, kuma bata labarta mata wani abu marar dadi da aka mata ba, sai ma jindadi da take fada mata da wasu abubuwa da ta iya a zuwanta garin, tana ta bata labarin yadda masarautar take da mutanen cikinta. [9/5, 12:32 AM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t ABOKIN RAYUWA