Sashe 51
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
"Shikenan amman ki yi ma maigadinki magana domin yanzu da na zo hana ni shiga yayi wai babu kowa a gidan alhalin na san a nan na taba sauke ki" Emily ta daga mata kai domin shi ne kawai abun da take iya yi. Tasmia ta tashi ta fice har lokacin mamakin mijin kawarta take tana jinjina halin maza duk kuwa da kasancewar bata san me yake faruwa ba. Bayan Tasmia ta fice Emily ta rumgume kanta ta fashe da wani irin kuka mai karfi sosai daker ta iya rarrashi kanta ta mike tsaye ta haura staircase din ta doshi dakin da London yake a hankali ta tura ta shiga ciki, bashi a dakin ta nufi bandaki slowly ta bude nan ma be ciki, ta fito ta janyo kofar dakin ta shiga dakinta ta zauna kan tool tana kallon kanta. Ji tana bukatar ganin danta ya saka ta nufi gurin da dayar wayarta take ta dauka ta kira Chidimma a zatonta London yana tare da ita ne. "Kina ina" Ta tambaya bayan Chidimma ta dauka. "Ina gurin kawata" "Ina London?" "Ba da shi na fita ba, na bar shi a gurin Sir Vito kamin na fita" Emily ta kashe wayar ta kira wayar Vito ringing daya ya daga. "Ina London?" "Na bar shi a dakinsa yana bachi, Ina kika je?" Bata amsa tambayarsa ba ta kashe wayar ta fito ta sake komawa dakin London din ta duba ko'ina har kasan gado bata ganshi ba, ta fito falo tana dubawa nan ma baya nan, ta fara duba lungu da sako na falon wai ko ya boya domin dabi'arsa boya a wani gurin musamman idan yana fushi, a nan ma bata ganshi ba. [5/8, 8:18 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA