Sashe 104
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
duk ya faru, but i divorced her today" "Guba kuma..... Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..." Ummi na rufe baki ta ji Aliyu ya amsa yana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un da karfi sai maimaitawa yake wayar ta fadi yana nishi da karfi sai karar abu take ji kamar ana dukansa. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un.... Aliyu.... Aliyu.... Lafiya? Kana ina?" Baya ina magana sai karar take ji kamin ta soma jiyo hayaniyar mutane sai kuma kiran ya yanke. "Sun kashe min a sun kashe min a, ko dai Turhan ko ita yarinyar ko Kameela sun kashe min a, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..." Ta fada da karfi tana fitowa dakinta da gudu har tana zubewa kasa ta tashi tana kuka. TURHAN POV. Bayan Aliyu ya wuce ya ji ba zai iya natsuwa ba ya haura sama ya dauko keys din mota ya sauko keys din a hannunsa. "Ina zaka je?" "Gidan shi zan tafi ba mamaki Aisha tana can, ina bukatar ganinta kuma ba zan sake bari ya keba da ita ba" Ya fice da sauri ya shiga motar da ya dauko key dinta mai gadin gidan ya bude masa ya fice, Ammy fitarsa da mintuna kadan Ammy ta kasa natsuwa da hakan ta dauki wayarta ta kira direban ta ya shirya mota ta saka hijabinta ta bi bayansa. @360 Turhan ya isa kofar gidan Aliyu, yayi horn da karfi babu daga kafa mai gadin ya fito a tsorace ya leka motar. "Me gidan baya nan" "Bude min Malam" Turhan ya fada da karfi mai gadin ya kuma ciki yana fadin "Allah yasa lafiya wannan lamari dake faruwa" Ya bude masa gate din Turhan ya shiga habarta gidan ko fakin din kirki be yi ba ya fita motar ya doshi kofar falon Aliyu ya tura kofar ya shiga Emily na zaune kan kujera ya duba ko'ina a gaggauce ya nufi sama ba dan be ganta ba sai dan tunaninsa da idonsa ba su zayyana masa matar da ya gani zaune a falon a matsayi Emily ba, sai da yayi rabin stairs din idanuwansa suka dawo masa da kamanin jan gashin da ya gani a gurin mace da ya tarar a falon sai ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, yana kokarin kamanta Emily da wannan matar da ya gani a yanzu. Ya juyo ya kalli Emily da ko kadan bata kalli inda yake ba, sun yi kama ta gashi da hasken fata har ma a fuska amman wannan ta fi Aisha da yake nema kyau da tsari sau miliyan ma, to amman idan ba Aisha bace to wacece? Ya sauko yana kallonta har ya karasa inda take zaune ya tsaya gabanta zuciyarsa kamar zata fado, tsabar kwarjinin da ta cika shi da shi. Sai a lokacin Emily ta mike tsaye ta kalleshi. Cikin tsakanin mamaki da kokarin tantance Emilyn din ce ko mai kama da ita ya furta sunanta a zuciyarsa. "Aisha.... Emily..." Be sani ba ashe tsabar mamakin be iya rike kanshi ba, daga kasa ya kafara kallonta turawa suka ce from toe to head yana kaiwa saitin fuskarta ya ji sauka abu mai sanyi a tsadaddiyar fuskarsa. Touf... Ta watsa masa yawu a fuska. Ya runtse ido da karfi ya jimke hannunsa da mugun karfin numfashinsa na fita da karfi, babban wulakanci a gurin balarabe shi ne ka jefe shi da talkami ko ka tofar masa da yawu. Sai dai a yanzu be isa ya nuna komai ba a hankali ya bude idon, ya sake kallon idanuwanta da be taba ganin tsarinsu da kyau ba sai a yau, tassaa ta wanke masa fuska da mari sannan ta kauce gaba gabansa ta nufi kofar fita falon kamin ta karasa Ammy ta shigo falon da saurinta jikin na rawa na son arba da Emilyn da take ta nema tsawon lokaci. __________________ ABOKIN RAYUWA.... [7/6, 9:18 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA