Sashe 121
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba ne" "Danki na daga cikin mutanen da suka sauya ni, ko dai na sake maimaita miki labarin ne?" "Wannan rashin kunyar duk na minene Aisha?" "Na neman rabuwa da mutumen da ya fifita son zuciyarsa ne akan ra'ayin mahaifiyarsa, na yi zaton kin sa ya rubuta takardar ai, kawai zan karba ne ko kuma ki kawo min domin tabbatar da furucinki" "Saki ko? Yanzu nan zai sake ki" Ammy ta nufi stairs, Turhan ya bita da kallo gabansa na faduwa wani hadarin tashin hankali yana haduwa a cikin kansa. Kasaita sarauta da isa duk ciresu yayi ya jingine ya nufi Emily ya sake tsayawa a gabanta, tana daga kai ta watsa masa wani kallo sai da gabansa ya sake bugawa da karfi, ta cika shi da kwarjini. "Dan Allah ki fahimta, na san na bata miki na kuntata na munana miki, abubuwa da yawa sun faru, na rashin jindadi da cutarwa, amman ki yi hakuri, ina son ki fahimci cewar ni dan adam ne, dole mukan yi kuskure... Ko... Ko ganganci, amman mafi girman kuskure shi ne kasa gane cewar kuskure ne, ki yi hak'uri Emily ki yafe min" Emily ta dauke kai zata matsa daga gabansa sai ya kai hannu ya rikota. Hannunsa da gurin da ya rike ta kawai ta kalla ta dago ta watsa masa wani mugun kallo, ba shiri ya dauke hannunsa a jikinta a tsorace. "Please... Kar mu dawo muna nadamar abun nan, ki duba rayuwar ki da ta Fatima, ba zata ji dadi ba bayan tsawon lokacin nan ta tashi ba tare da mu ba, abu ne mai wahala ki iya jure ziyararta a koda yaushe, idan ke baki bukatata a rayuwarki ni ina bukatarki" Emily bata ce masa uffan ba, hankalinsa be kara tashi ba sai da ya hango Ammy na saukowa rike da takardar da biro. "No no nooo Ammy ni fa ba zan sake ta ba, ke kika sa na aureta, na ji na yi kuskure to ku ba ni damar gyarawa mana, duk wata wuta da zata kunna zan iya tarar ta, amman ban da rabuwa, wannan be dace ba, na shirya fuskantar ko wanw kalubale a yanzu, And Emily na shirya gabatar da ke har a gurin mahaifina da kuma ar mu Fatima, zan mu na komai a yadda ya dace" Ammy ta karaso gurin ta mika masa da biro. "Rubuta mata saki" Ya matsa baya ya girgiza ma Ammy kai. "Ammy please... Karki cilasta ni wannan, ki kan ba ni umarni na bi dan Allah kar mu samu tsabani a nan, ko sakinta na yi makiya ma dariya za su mana" "Ka dubuta mata saki Turhan" Ammy ta furta cikin kakkausan halshen. Yaja kujerar dinning ya zauna ya rufe ido yana murtuke fuska kamar mai shan wani abu marar dadi. Ya sake bude idon ya mike tsaye. "Bari na yi magana da ita" Ya karasa gaban Emily ya kama hannunta ya rike cikin yanayin dake bayyana tsakanin damuwarsa. "Dan Allah Emily ki yi hakuri ki yafe min, ki ba ni dama na gyara kuskuren da na aikata, ki yi hakuri Emily zan canja, na ma manja ba yadda kike tunani ba ne, zan baki duk wata kulawa da kike bukata" Ko kallonsa bata yi balle ta yi wani reaction da zai nuna ta fahimci kalamansa. "Ka sake ta na ce" Ya kalli Ammy kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah karki cilasta ni aikata abun da ban yi niya ba, ba daidai ba ne... I... I... I love her... Ina son... Matata, rabuwarmu zata kara bata abubuwa ne kawai, ya kamata mu fahimce ta zafin zuciya ne yake debanta take kalamai marasa dad..." "Zaka sake ta, ko sai na barranta ka daga gani ni" Ya kalli Ammy babu shiri sai ta sake nanata masa. "Ka sake ta yanzu nan" Kamar wanda aka yi ma shocking haka ya rumgume Emily da sauri ya matse ta a jikinsa ya runtse ido, ya dauki dakiku a haka Emily bata motsa ba sai ya sake ta koma ya zauna ya Ammy ya dora masa takardar a dinning da pen. "Idan baka sake ta ba, ban yafe haihuwar da na yi maka ba Turhan...!!!" Ya kalleta cikin tashin hankali da rashin madafa. "Ammy...." Ya masa cewa komai hannu na rawa ya dauka ya dora a takardar ya kama biron baya ko iya rubutawa har sai da ya saka dayan hannunsa ya rikw hannunsa na dama, ya sake dagowa ya kalli Emily. "Ba zaki ce komai ba Aisha? I'm sorry i Love you, idan ba zaki yi dan ni ba ko dan Fatima" Emily ta ki ta kalle shi. Sai ya kalli Ammy idona na zubar da hawaye ya ce. "A koda yaushe ni mai biyayya ne a gareki, da dadi ko ba dadi, zan saki Aisha, amman ba dan raina na so ba, sai dan ba zan iya jure tsinuwarki ba, amman dai ba haka raina ya so ba" Ya maida hannunsa yayi rubutun da larabci hannunsa na rawa, sannan ya dago takardar ya mikawa Emily, sai a lokacin ta kalle shi tana jin wani sanyi a ranta. "Ashe kana iya kuka Turhan, ko kuma na munafunci ne irin yadda ka yi a lokacin da za mu bar Kasar nan zuwa Sudan" Ta fisgi takardar daga hannunsa, sannan ta juya ta kalli Ammy. "Ina yata?" "An dai baki takardar da kika bukata, kuma na fada miki za a tabbatar miki an kuma yi haka, takardar ita ce wajibi" Emily ta daga kai ta kalli stairs da nufin kiran Fatima sai ta hangota tsaye tana kallonsu tana kuka, bata fahimci me kai da kawo ba ita dai kawai abin da ta gane mahaifinta na kuka Emily ta ki jin tausayinsa. Emily ta mata murmushi ta mika mata hannu. "Fatima zo mu tafi" Fatima ta sauko da gudu Ammy ta juya da nufin idan Emily ta yi yunkurin rikonta ta hana, Turhan kuma hankalinsa ya kara tashi ganin zai yi 2 - 0. Fatima na saukowa ya nufi Turhan ta rumgume shi. "I love you Daddy, stop crying" Emily ta kira sunanta da karfi. "Fatima wannan mutumen da kike gani, ba mutunen kirki ba ne, shi ya bar mu a tsawon shekarun nan, baya son ki ya cutar da ni" "Be cutar da ke ba, na ga yana kuka yana cewa yana sonki, me ya kika min karya Momy miyasa baki son na samu Baba? Kowa yana da baba amman ni ba ni da shi?" Turhan ya dauke ta ya dora a kafada ya rumgume yana jin sanyi a ransa. "Fatima wannan mutunen ya cutar da ni ya wofintar da ke" "Duk abun da ya faru ya faru ne saboda be san an haife ta, kin samu abun da kike so dan Allah ki tafi" Ammy ta fada. "Ba zan tafi ba sai da yata, daman mun saba rayuwarmu ba da ku ba, da Fatima zan tafi" Emily ta fada sai ta nufi Fatima ta riko hannunta zata rabata da jikin Turhan, a take Fatima ta fisge hannunta. "Bana son na tafi tare da ke, ina son babana i hate you" Emily ta fisgota da karfi, sai Fatima ta saka mata ihu tana kuka. "Bana son na tafi da ki, Babana nake so" Emily ta kalli Turhan. "Na rainin cikin yarinyar na haife na raine ta har ta kawo yanzu, ba tare da kai ba, a yau ka bayyana a rayuwarta ka cusa mata kiyayyata alhalin kai ne makiyinta, hakika kai azzalumi Turhan" Turhan ya girgiza mata kai alamar ba shi da laifi, Emily ta juya ta nufi kofar fita, zai yi magana Ammy ta rike hannunsa ta girgiza masa kai. Emily ta fita falon tana zubar da hawaye ta nufi motar da aka kawota ta shiga tana kuka, har direban ya isa gida kuka take, haka ta motar ta nufi entrance din taka ta isa bakin kofar falon, a kokarinta na saita kanta ya jingina da window falon tana maida numfashi. "Ki taimaka min dan Allah, ban san ta ina zan tunkareta ba, ba lallai ta fahimta ba, amman ina son Emily fiye da sauran yayana kuma tsawon lokacin nan Wallahi ban san inda take ba, ban ma san yadda abubuwan nan suka faru ba..." Ta ji muryar Mama Barakat tana maganar cikin kuka, Emily ta dago daga jikin window falon tana jin wani jiri yana debanta, kawai sai ta ji mafarki take ta girgiza kai ta juyo rike da takardar da kuma wayar, ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice, haka ta kama hanyar titi, ta taba fuskarta sai ta ji kamar ba tata ba, idonta har wani rufewa suke suna budewa hawaye suka fara mata kwarara. Tsayawa ta yi cak ta kalli gabas ta kalli yamma, ta kalli kudu ta kalli arewa, ta kalli sama ta kalli kasa sai ta rasa a ina take. Babu wanda ya fado mata a kwakwalwa sai Dr A-B, ta share hawayen ta dago wayarta ta kalli screen din ta bude ta shiga ciki, one by one ta rika bin number har ta isa gurin number Dr A-B ta danna masa kira. Ta yi ringing uku ya daga. "Hello..." "Emily ce i need your help, ina tunanin kwakwalwata ta samu matsala" "Daman na san zaki kira, a ina kike?" "A inda nake" "Zaune ko a tsaye?" "A tsaye nake" "Samu guri ki zauna ki bawa wani na kusa da ke wayar" Ta mika wayar a iska ta sake ta, sannan ta zauna a kasa, tana bin ko'ina da kallo kawai rayuwar mafarki take ganinta.... [7/19, 5:10 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA