Sashe 74
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daga nuna min soyayya Emily? Ba ki jin cewar lokaci yayi da ya kamata ace mun kasance karkashin inuwa daya?" Ta sauke idonta kasa tana shafa wuyanta. "Kina da wani buri ne da kike son cin ma kamin ki amince min ne?" "Vito bana son sana'arka" "Bayan shi fa" "Fatima-... La lall" Bata karasa ba ya katsi hanzarinta yayi gaba. "Oh Okay" Ta bi bayansa suka fito daga gurin ya nufi motarsa ya bude ya shiga har yayi mata key sai kuma ya fito ya dawo daidai inda take tsaye ya shafa fuskarta sannan ya koma motar, tana tsaye tana kallonsa har ya fice, abun da ba su sani ba duk abun da suke Chidimma na lekansu. Emily ta shigo falonta kenan wayar hannunta ta yi ringing data duba wayar sai ta ci karo da sunan Tasmia, babu bata lokaci ta amsa. "Hello" Tasmia ta fashe mata da kuka. "Emily dan Allah ki zo ina cikin damuwa ina cikin bakinciki, ki zo yanzu dan Allah ina da bukatar taimakonki" "Okay gani nan zuwa" Ta nufi staircase da sauri ta dauko key din motarta ta fito ta sauri ta nufi gurin da motar take, daga unguwar da take zuwa unguwar da Tasmia take tafiya ce ta mintuna Arbanin amman cikin minti ashirin da biyar ta isa gidan Tasmia hankali a tashe saboda ta ji muryarta tana kuka kuma gashi ta fada mata da bakinta cewar tana cikin tashin hankali. Tana faka motar ta bude ta fita ya fara kwankwasa kofar Tasmia kamin ta tura ta shiga, yanayin yadda ta ga falon a hargice ta san ba lafiya ba, ta zauna kusa da Tasmia dake rusar kuka tana tambayarta abun da ya faru. "Ni ma ban san miya faru ba, matar nan tana shigowa ta rufe ni da duka wai mijinta yana zuwa gidan nan nemanki, gaba daya Kameela bata da hankali, akan Aliyu zata iya komai Wallahi kara ma ki rabu da mijinta, ni din ta yi min haka ina ga ke kuma" "Ba soyayya nake da mijinta ba, kuma waya fada mata yana zuwa nan nemana? Yaushe rabon da na zo gidan nan ma" "Waya sani wata kila bincike tayi har ta gane ko kuma shi ya fada mata ai maza ba su da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba" "Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu" "Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti" "Okay tashi mu tafi" Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye "Ban san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki" Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan ta sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling. "Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiransa" Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta. "Okay mu tafi asibitin" "Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba" "Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya" "Okay" Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta. ALIYU POV. "Daman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta" Shi ne sakon da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce. Amman me zai saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibiti ta kwana. "Ahhh Ahhh" Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka. "Me ya faru?" "Baka ga sakona ba" "Na gani, garin ya ta miki duka?" "Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gidana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka" "Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na" "Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sai yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya" Bata jira abun da zai fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily. Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa. "Hello" "Emily" "Na'am" "Kina ina? Me kike yi a yanzu" Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne sai washe gari ta dawo. "Ina gidana" "Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?" "Aa" "Tasmia fa?" "Meyasa ka tambaya?" "Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?" A take ran Emily ya bace "Matarka bata da hankali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?" "Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani" "Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta" "Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni dan iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai" Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a hanyarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B yana cikin PH. "Ka je ka ganshi misalin karfe tara, na yi magana da Dr Osman zai hada ku sai ku yi magana ya baka ranar da ya kamata ku hadu, idan a Abuja zaka same shi sai kaje idan kuma a zai iya dubata idan ya shigo PH duk daya domin yana yawan shigowa nan aka ce" "Okay na gode Nura zan shirya zuwa 9 na tafi gurin ka turo min address da number Dr Osman din" "Okay" Daga haka suka yi sallama, Aliyu ya koma gidan sai ya samu Kameela ta yi masa gyara, wato ta hargitsa gidan gaba daya ta fashe abubuwan da zata iya fasawa ta watse wasu. Zaunawa yayi kan stairs din ya dafe kansa yana ta ambaton Allah, daya daga cikin dalilin daya saka yayi ma kansa kuma yayi ma Kameela alkawarin ba zai kara aure ba har da gudun tashin hankali da kannan maganganun ashe dai ko a yanzu bw tsira ba. EMILY POV. Cikin bacin rai ta fito Kitchen din, Vito dake zaune a dinning yana karyawa ya bita da kallo. "Jiya baki kwana a gida ba" Emily ta kalli Chidimma, domin ta san Vito baya kwana a gidan balle ya san ta kwana ko akasin haka. "Ni ba karamar yarinya bace, ina da damar na kwana a duk inda nake so" "You're just 25yrs old kuma