← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 177

Sashe 77

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

yi be isa yace ki dawo gida sai ya neme ki ba? Me yake takama da shi?" Cewar Hajiya Asma'u Anty taba ya tsina fuska. " Wallahi kuwa nan kika watsa mana kasa a ido kika tsaya kai da fata babu mai son auren nan kika ce sai Aliyu, gashi nan tun ba aje da nisa ba ya koraki ya nuna wata banza ta fiki muhimmanci ina alkawarin da yayi miki toh?" "Alkawarin banza, dadin baki ne irin na maza kuma ni daman na san ba da zuciya daya ya aureta ba, ya aureta ne kawai saboda ubanaa ya karbi mukamin ubanki a yanzu, ke kuma ya aure ki ya wulakanta mu, kuma yayi nasara tun da kin ba shi hadin kai" Hajiya ta fada, sai Anty Shafa ta sake karba mata "Ai kara ma auren ya kare kowa ya huta, idan abun be tsaya iya nan ba gaba ba a san ya zai kasance ba, kuma dan Allah Hajiya ki hana D Alhaji kiransa dan jin ba'asi ko kiran iyayensa" Hajiya ta daga hannu. "Ai Alhaji ma ya fini daukar zafi shi da kansa yace tun da ya turo masa ya gida sai ya san yarsa tana da gata" Ganin ba za su barta da damuwar abun da ya isheta ba ya saka ta tashi ta bar musu bangaren gaba daya ta koma part din Mama Barakat ba dan ranta ya so ba, kan kujera ta zauna tana rushe da sabon kuka bayan wanda ta sha har ya kumbura mata ido ya hana ta cin abinci tun da ta dawo gida. Mama Barakat ta aje abincin dake hannunta ta taso da sauri ta dawo kusa da Kameela dake zaune kasa ta zauna kan kujera. "Subhanallahi Kameela lafiya? Yaushe kika zo?" "Aliyu ne yace na tafi gida sai ya neme ni" "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un Me kika masa?" "Ban masa komai ba, saboda wannan bakar kafirar ne, ba ma ita kadai ba har kawata yake bibiya" "Abun be yi dadi ba, amman kin yi bincike? Kar ya zama kin masa mumminar fahimta ne, ko kuma kim yanke hukunci cikin fushi" "Mama Baraka har test fa Emily ta turo min tana fada min magana son ranta" Mama Baraka ta yi shiru na mintuna tana shafa Kameela alamar rarrashi sannan tace. "Kina da hoton Emilyn ne Kameela?" "Ba ni da hotonta" Mama Baraka ta sauke ajiyar zuciya domin tun a fadansu na farko take son ganin hoton Emily saboda yadda Kameela ta siffanta ta. "Ki yi hakuri idan mahaifinki ya dawo zamu yi magana da shi" "Aa ni na hakura ba zan koma ba, kar ma ki masa magana ko Aliyu ne autan maza ni ba zan koma gidansa ba" "Ba'ayi ma aure haka, tun har kuna son junanku baki san abun da Allah ya tsaro a tsakaninku ba, hakuri zaki yi" Kameela ta kara fashewa da kuka tana fadar ita ba zata koma ba ta hakura da Aliyu. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [6/11, 11:51 AM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing ABOKIN RAYUWA
Chapter 77 · 0% Book details