← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 113

Sashe 97

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri ya katse maganar ya amshi junior yace
"Sorry.. uncle dina na kirana, inaga zamu wuce ne,
thanks alot,
bin bayansu Musaddiq yayi dan keyn motarshi ya makale jikin showel din,
tsayawa Aman yayi cike da mamaki yace

"Any problem?

Nuna mishi keyn yayi lokacin ya cireshi haďe da jan kumatun junior,
"Bye Daddy,
ka daina rigima kaji ko?

yadda ya kaďa mishi keyn yasanya yaron sake yin dariyar da ta tsaya a ran Musaddiq,
saida suka kurewa ganinshi sannan ne yayi ajiyar zuciya haďe da kokarin cire tunanin yaron a cikin zuciyarshi...

Faďuwar da gabanshi yayi ne ya sanyashi faďin

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun...
kamar an sake hura faďuwar gaban domin kuwa da sauri da sauri take harbawa kamar ana lugude,
runtse idonshi yayi haďe da dafe kirjinshi,
tunanin da yake kwana yi shi ya dawo mishi sabo fil kamar yau aka halitta shi a cikin zuciyarshi,

Karar wucewar takalma ta bayanshi ya sanyashi buďe idon a hankali,
kafin ya juyar da fuskarshi duk sun bi ta kofar sun shige sai Aman da shima ya bi bayansu,
kamshin turarukansu da ya biye gurin shi ya sanya Musaddiq sake jingina da kujerar yana mai tsintar kanshi cikin shaukin da ya daďe bai shiga irinshi ba....

Saida jirgin yakai 45mins sannan ya sauka a wani kebabben guri saboda dama private ne,

A gajiye likiss suka sauko kowa yana mika saboda zaman guri daya,

Anty Reemah Musaddiq ya fara gani yayi saurin karasawa kusa da ita yana mata sannu da zuwa,

Sakkowar Sheik ba karamin gigita Musaddiq tayi ba,
bai dawo daga wannan shock din ba ya shiga wacce ta fishi,

Maleekah ya hango kanta dauke da hular Hilal wacce ta cire suna gab da fitowa,

"Kaga Nadeeyarka ko?
Kunci ya kare,
Papa ya faďi yana murmushi...

Hmmm ya faďi cike da mamaki,

"Mai kama da ita dai,
Nadeeyah ba haka take ba,
amma a ina kuka samo mai kama da ita,
in ma kunyi haka ne dan hankalina ya kwanta in sake wani auren to ku sani ni da aure sai dai a lahira,
yadda Nadeeyah ta gama aure ta tafi ta barni nima hakan zan je in sameta yadda ta barni..

Hannun Papa Anty Reemah ta kama haďe da girgiza mishi kai suka tsaya a gefe,

cike da murna Hilal ya sauko ya rungume Musaddiq haďe da tambayarshi bayan rabuwa,

Murmushin da dole uwar naki ta koya mishi shi ya sakar mishi haďe da tambayarshi su waye wadannan masu kama da su Mamma?

"Hello broo,
Ayyam Atika Ateek, a.k.a Maleekah,
tsaki Hilal yayi haďe da cire hular kanta yayi gaba,

"Salamu alaikum,
nyc meeting u Atika,
i am Musaddiq Kyari,

Maida hannunta baya tayi dan yadda ya amsa mata sallamar ya burgeta,

har kasa ya tsuguna ya gaida su Sheik,
dagoshi Sheik yayi ya rungumeshi haďe da amsa gaisuwar,
saida suka gaisa sosai sannan suka fita suka isa motar Musaddiq da wata da aka basu a airport din dan zurga zurga,
har suka isa gida Musaddiq bai bar tambayarsu daga ina suka nemo dangin Mama suwaiba ba....

Cike da al'ajabi Daddy ya ke duban Sheik,

"Ikon Allah kenan,
to meyasa babu wanda ya nemeta?

Murmushi sheik yayi yace

"Kaddarar Zuri'a,
a lokacin da labarin yazo mana ina da shekara shida a duniya, amma nakan tuna wasu abubuwan,

Lokacin da labarin mutuwarta ya riski ummul bata tsaya tayi binciken komai ba,
kamar jira takeyi ta tattara 'yayanta suka fita daga gidan da niyyar in ta koma tace harda ni aka kashe,
wani yaron da muke wasa dashi *Husaimin*
shi ya shigo ya tasheni yace
"inyi sauri gashi can za'a gudu a barni,
a lokacin ne yake faďa min cewa an kashe Habeebullah da yayata,
da gudu nabi bayansu lokacin har sun hau amalanke sun fara tafiya,
takalmina da ya cire na waiga zan dauko Husaimin yajani da tayar hannunshi mukayi gudu muka kamo su,
dakyar na iya hawa saboda tsayin abun,
ina hawa ummul ta fara yi min masifar borin kunya tana tambayata inda naje,
ban bata amsa ba na tsugunar da kaina inata kukan rashin gatan da zan tarar,
har muka isa inda zamu tsallaka ruwa ban daina kuka ba,

muna zuwa muka samu wadanda zasu tsallaka zuwa Egypt,
nan aka loda mu ciki muka fara tafiyar da ta kaimu washe gari cikin ruwa...

Karya da gaskiya Ummul ta fadawa mahaifina har ta ce mishi an sallaceta a gabanta domin tasan bazai yarda da ita ba sai yasa an je an dubo ta,
saboda tsabar bakin cikin rashin Atika mahaifina ya kamu da mummunan ciwon stroke wanda ya daukeshi shekara biyu yana yi kafin Allah ya dauki ranshi,
gaba daya dukiyarshi ummul ta tattareta ita da yayanta ta maidani dan aikinsu,
son zuciya yasa ta manta matsayina a gurinta,
ta mance cewa inda mahaifiyarmu ta tafi itama zata je komi daren dadewa,
gidan Sheik Al' Mannar abokin babana nan nake zuwa daukar karatu,
ganin hazakata yasashi ya sanya ni a makarantar boko,
daga can sai in wuce gurin da suke aikin gini in dinga koya ina samun na abinci,
gaba daya kwanan gidanmu ya gagareni domin kwana nakeyi aiki bani da wani hutu,
abinci ma ummul sai taga dama take bani a cewarta itama ba kudi gareta ba,
duk wasu kadarori na mahaifinmu ta haďe ta siyar sun cinye kudin da 'yayanta...

Muna da shekara sha takwass 'yaranta biyu sukayi wa wata yarinya fyaďe wanda hakan yayi sanadiyyar yi musu hukuncin da yayi ajalinsu,
a lokacin ummul hauka ne kawai batayi ba domin saida tayi wata biyu a asibiti,
ni nayi jinyarta saboda dayan yaronta an nemeshi an rasa ya gudu da ragowar kudin da ta ajiye,
ashe shima smuggling din kwaya yakeyi,
ranar da dubunshi ta cika aka kamashi ita ma a ranar rayuwarta tazo karshe saboda shock din fille mishi kai da akayi...

Gaba daya ummul ta manta cewa akwai mutuwa a bayan rayuwa,
damar da Allah ya bata ta butulce mishi tayi wasa da ita,
lokacin aji na biyu a jami'a,
da taimakon Allah da taimakon Sheik na samu na kammala makaranta,

Dan kudin da gwamnati ke bamu na scholarship da kudin aikin ginin da nakeyi yasa ni na fara dan karamin business dina,
cikin ikon Allah kafin shekara abun ya bunkasa dan har na sai fili nawa na kaina,
a lokacin ne kuma Allah ya azurtani da samun mace ta gari Zeenat yar gidan Sheik,

Shekararmu biyu da aure muka samu Irfan,
daga nan ne kuma duk shekara sai ta haihu wasu suzo babu rai, wasu kuma suyi watanni su mutu,
daga kan Maleekah ne kuma haihuwar ta tsaya mana duk da ba haka naso ba,
amma zabin Allah shine zabin komai.....
ya karashe yana share hawaye haďe da yin murmushin takaicin fitar da irin kunar ukubar da yasha yana yaro.....

Babu wanda bai zubda kwalla ba a dakin,
lallai mutanen zamanin yanzu banda rikon sakainar kashi da sukayi wa zumunci,
harda illata rayuwar juna ma sun kware akanta....

Babu wanda yake da kwarin gwiwar faďin mutuwar Atika domin basu san katse mishi shaukin da yake ciki...

Wayar Papy Daddy ya kira domin jin ko sun kusa isowa,
kashe wayar yayi yace wa Musaddiq "har sun iso bakaje ka daukosu ba,

"Zubair zai dauko su, Musaddiq ya faďi cikin girmamawa..

"Okk to, Allah ya kawosu lafiya, Daddy ya faďi haďe da sake jan sheik da hira....

Motar da Zubair ya sai mata farar matrix sabuwa dall ita ta tuko tazo gidan tare da kayan abincin da ta hadawa bakin,
koda ta isa gidan kiran Musaddiq tayi a waya dan ya fito ya tayata shiga da kayan,

Fitowa sukayi shi da Hilal suka kwaso kayan abincin,
tsokanar Musaddiq Faidah takeyi wanda ya sanyashi yin murmushi haďe da matsowa amsan tray din hannunta,

Garammmmm....
sukaji an saki kofar gidan da karfin gaske......

Mrs Tijjani Shatimah.....
[11/06 8:34 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Anty....

Nadeeyah ta faďi cikin dashewar murya,
juyowa Raliya tayi ta sake kankame junior a kirjinta,

"Na'am Nadeeyah,

wayar dake hannunta da take kokarin kira Nadeeyah ta karba ta ajiye a gefe,

"Dan Allah kiyi min alfarma ďaya!

Dan Allah karki sanar da kowa dawowata,
inada dalilai masu karfi da in na faďa miki zaki fahimceni,
dan Allah Anty ki dubi maraicina kiyi min wannan taimakon!

Cikin sanyin jiki Raliya tace
"Nadeeyah nayi miki alkawarin in har dalilanki masu karfi ne zan taimakeki har sai kin cika burinki, faďa min kanwata....

Anty bani da gatan da wuce Allah,
bamu da asali ni da yan uwana kamar yadda ake faďi..
na taba ji a bakin wani malamin mu cewar Allah da ilimi sune gatan maraya,
babu wanda zai zama maraya sai rago,
sannan wannan ilimin shi zai sa ka samu yancinka a cikin al'umma,
a yanzu in na zauna tare daku, Mummy da su Anty Raudha bazasu taba barina in yi rayuwar yanci ba,
sannan bazan iya jurar ganin yaya Musaddiq da wa------

Shhhhhh...
Anty Raliya ta katseta saboda ganin junior na kokarin yin bacci,
sabashi tayi a kafaďa tace
"ina jinki?

Na dade da burin yin ilimi mai zurfi,
dan Allah ki goyamin baya in samu abinda zan tsaya da kafafuwa na,
banason mu kare a haka ni da zuri'ata,
kinfi kowa sanin rayuwar rashin gatan da mukayi mu da iyayenmu,
bana fatan mu kasance a cikinta ni da ďan da na haifa,
nayi miki alkawarin zan kare mutuncin kaina,
zan nemi kuďin halal inyi sponsoring kaina,
su uncle Taheer sunyi min duk abinda ya kamata dan uwa yayi maka,
yanzu zan fita in nema da kafata har Allah yasa na dace....
Chapter 97 · 0% Book details