Sashe 7
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a ranar saida yayi kukan murna dan ko a mafarki bai taba tunanin rike dubu hamsin tashi ta kanshi ba, bare dubu dari har guda biyar,
Allah kenan in yace "ku fa ya kun" shikenan, (Allah ka datar damu)..
Zama yayi da Mai gidanshi sukayi shawarar abunda zaiyi da kudin,
d'aura shi yayi akan harkar sosai saboda yanada jarin shi na kanshi, babu inda basa Zuwa saro Kaya basu onitcha, enugu Lagos da sauran guraren sarin kayan fruits,,
Cikin ikon Allah da taimakon Papa aka bawa Nadiya admission a fgc malali,
Hafiz yayi kokari wajen yi mata komai na tafiya makaranta,
haka babanta da Mamma suwaiba duk sunyi mata kokari,
Sam bata San tafiya saboda tausayin mahaifanta,
wani bangare na zuciyarta kuma ya bata shawarar, Ilimi shine gishirin zaman duniya,
kuma ko ba komai zata kauracewa ganin Badariyya,
da wannan tunanin ta samu karfin gwiwar tafiya makarantar kwana....
*****
Frederick University..
Gudu yake shararawa cikin motarshi kirar KIA karama ruwan goro,
wakar "Rockabye" ta "Anne-marie ya Kure volume yake saurare yana bi a hankali,
hon ya latsa da karfi yana sauke glass din motar hade da kallo inda take..
mikewa tayi ta isa gurinshi ta bude kofar gaba zata shiga yayi saurin dakatar da ita,
"baya zaki zauna ko kin manta bani kadai bane,
rufewa tayi bata ce kala ba ta bude baya ta shiga,
ko kallonta baiyi ba ya tada motar ya wuce "faculty of engineering"
a kofar dept din ya hango shi zaune yana duba wasu littafai,
kashe motar yayi ya fito ya karaso gurinshi yace
"heyyy guru" shall we,
musaddiq ya mike yana kakkabe jikinshi yace eh mu tafi,
waya Hilal ya mik'a mishi yace "call ur mama ta kirani Wai wayarka a kashe,
Musaddiq ya dan ja tsaki yace "barta zan kira in naje gida na gaji Sosai,
mayar da wayar aljihu yayi ya bude kofar motar ya shiga,,
gaisawa musaddiq sukayi da meerah dake baya tana shafa hoda a fuska,.
kallonta Hilal yayi ta mudubi yace "madam makeup" an fara, banza tayi mishi ta cigaba da kwalliyarta,
jan motar yayi yana murmushin ko a jikina yarinya...
Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:46] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣1⃣
Shekaru sun dan jaaa,
cikin farin ciki da akasin shi saboda halin rayuwa na yau zuma gobe madaci,
"Nadiya Adam"
muje mu rage Miki hanya mana,
yamutsa fuska Nadiya tayi cikin damuwa tace bari kawai Rukky, zan samu napep in tafi,
Kallonta rukky tayi cike da mamaki dan dai tasan bata da ko Naira biyar a jikinta,
hannu tasa ta fara daukar kayanta tace zan kai miki kayan, ki taho a mashin ma wannan ke ta dama,
bin ta Nadiya tayi da kallo tace
"Haske dan Allah ki barshi kar in matsa muku Kinga hanyar mu ba daya bace,
"ke kika rokeni? Rukayya ta fadi fuska a hade,,
Girgiza kai Nadiya tayi tace "a'a amma--- amma me Haske tayi saurin katse ta, tace "zo mu tafi dan Allah,
kwashe sauran kayan tayi ta bi bayan Rukayya Haske ranta duk a jagule,
A gatance ta fara makaranta,
tun daga shigarta har Zuwa ss1 third term,
tunda ta dawo first term din nan ko sau daya babu wanda ya ziyarce ta,
zuciyarta cike take da fargabar abin da yake faruwa da Yan gidansu,
number yaya Hafiz Sam bata shiga haka ta mamma,
tunda ta shiga motar take addu'ar Allah yasa kowa na nan lafiya,
dai dai kofar gida suka sauketa suka wuce cike da kewar makaranta,
Jakarta ta dauka ta fara tafiya domin karasawa cikin gidan,
A can bakin murhu ta hangi mahaifiyarta idonta yayi jawur hanci duk ruwa saboda wahalar hura wuta,
ajiye Jakarta tayi ta karasa kusa da ita,
idonta cike da kwalla take kallon mahaifiyarta dake mata murmushi,
hannunta Nadiya ta kama zata fara magana suka jiyo tari me karfi babu kakkauci daga cikin dakin,
da gudu mamma ta nufi dakin tana fadin subhanallah!! sannu,
bin bayanta Nadiya tayi da sauri, ta tarar da abin da ya daga hankalinta matuka,
mahaifinta ne kwance cikin bargo kamar jaririn goye,
ya rame ainun, idanuwanshi sun zurma sai tari yakeyi hade da kakin jini,
kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin meya sameka Baba?,
mamma me ya sameshi,?
mamma dake tare jinin da wata tsumma tayi kokarin boye idonta da ya ciko tace "bashi da lafiya ne amma da sauki,
wani irin sauki mamma, Ina saukin yake anan?,
dan Allah ki kira yaya Hafiz mu kaishi asibiti,
nan kukan da mamma ke boyewa ya bayyana,
Take Nadiya ta rikice, dan ita dai tun tasowarta bata taba ganin bacin ran mahaifiyarta ba bare har takai ga zubar ruwan hawaye,
Durkushewa Nadiya tayi tace "mamma me nayi,? Dan Allah kiyi hakuri,
Wai me yake faruwa ne?
kuka mamma takeyi iya karfinta gunin ban tausayi,
kallonta Malam Adamu keyi hawaye na zuba ta gefen idonshi a ranshi yana mai Jin dadin kukanta domin ko ba komai zata samu saukin nauyin dake cikin ranta,
sai da tayi mai isarta ta share hawayenta, ta kalli Nadiya dake kuka tana share hawayen idon mahaifinta tace
"tashi maza kije kiyi wanka kiyi sallah,
bari in nemo miki abin da zaki ci,
Nadiya ta share hawayenta tace "ki barshi kawai, bari nayi wanka in daura mana, zauna ki kula da baba,
Gyada kai mamma tayi kawai, dan bata son tasan abinda ke faruwa,
Nadiya na shiga bayi mamma ta fita shagon Tasi da ya kara cika ba kamar da ba,
Indomie da Kwai ta ce ya bata,
dakyar ya bata dan yana bin ta bashin kusan dubu daya da dari hudu,
da sauri tayi cikin gidan, ta hado yayi, ta sauke ruwan dumin da ta daura ma mijinta, ta iza wutar ta daura Indomien cikin karamar tukunya..
Wanka da sallah Nadiya tayi,
ta saka doguwar rigar deep blue material mai gajeren hannu ta shan iska,,
ko mai bata shafa ba ta daura jar hula a kanta,
kyawu mai sirri da cikar budurci suka bayyana a tare da ita,
wani irin kyau Nadiya ke dashi marar hayaniya, wanda ya kara fitowa saboda dan hutu da kuma rufin asirin da suka samu,,
kusa da Mamma ta tsaya tace "sannu da aiki mamma,
ina Zainab?
"Tana islamiyya,, mamma ta bata amsa tana tura leda cikin murhun,
Tambayoyi ne cure cikin zuciyar Nadiya,
ta rasa wanda zata tambaya ya bata amsarsu,
ko zata mutu tana tambayar mamma bazata amsa koda tambaya daya cikin tambayoyin da take dasu ba,,
Daki ta shige gurin mahaifinta da ya fara bacci numfashin shi na fita dakyar,
Kure shi tayi da ido tana addu'a tana tofa mishi,
Mamma na kwashe Indomien zainab ta shigo gida da gudu jikinta yayi futu futu,
"mamma yunwa nake ji, zainab ta fadi murya a sarke saboda tsabar gajiya..
kallon Indomien mamma tayi tace to bari kiyi wanka ko? ,
noke wuya tayi kamar zatayi kuka tace cikina na murda min,
je ki wanke hannu kizo muci, Nadiya ta fadi tana fitowa daga daki,
rungumeta zainab tayi tace "yaushe kika dawo anty?
Dazu kina islamiyya,
da fatan kina karatu a makaranta, Nadiya ta tambayeta tana shafa kanta,,
gyada kai zainab tayi tace Sosai ma,
kin kawo min chocolates,
Kumatunta Nadiya taja tace "eh yana jaka ta,
maza wanko hannu muje muci abinci..
Mamma kinci abincin ne?
Nadiya ta tambaya idonta kyar akan mahaifiyarta,
mamma dake kofar daki tace "eh munci sosai, bansan zaki dawo ba da na ajiye miki,
zainab da ta kai Loma kamar zata shake tace "mamma yaushe kika ci abinci?, bayan tafiya ta makaranta,
shine kika cinye baki ajiye min ba,
mamma ta saci kallon Nadiya,
tayi saurin maida kallonta gurin zainab tace ba gashi kina ci ba,
maza kici karki kware,
Nadiya dai hannu kawai take juyawa cikin abincin har zainab ta kai karshen shi harda sid'e kwanon,
meya ke faruwa mamma???
Tambayar ta fito a bakin Nadiya cikin rashin sanin fitowarta,
me kika gani?
Mamma ta amsa ta cike da fargaba,
rarrafowa Nadiya tayi ta dafa cinyarta tace "mamma boyemin abin da ke damunki bashi da amfani, nasan bani da maganin shi amma atleast zaki ji sauki in kin fada min.....
**********
Ohh ni!!!
"wacce iriyar rayuwa ce wannan? d'aki kaca kaca sai kace ba na mata ba, mummy ke mitar tana tafe tana tsintar kayayyaki a kasa da takalma,
Husna dake kwance tana duba littafi tace
"kema kin San ko aikin waye mummy,
"ni gaskiya na gaji wallhy, canza min daki za'ayi, bazan iya wannan rayuwar ba,
kwance take cikin matsatstsiyar jar riga da yellow mini skirt,
Gashinta Parke a tsakiya da yellow ribon,
kunnenta dauke da earpiece alamun bata ma San me sukeyi ba,
kada kanta kawai takeyi tana bin wakar hade mutstsuka santala santalan kyawawan kafafuwan ta,
kafarta mummy taja a hankali,
juyowa tayi tana cire earpiece din kunnenta cike da rashin da'a tace
"ya akayi ne mum"
mummy ta ajiye kayan makarantar ta a gefen gado tace "babu komai baby na, kinci abinci dai ko?
gyada kai Badar tayi alamar eh sannan ta juya ta mayar da kanta kan pilo tana cigaba da jin waka hade da chatting,,
"hmmmm" kawai Husna tace ta sakko daga kan gado tace
"mummy zanje gidan Anty Raudha,
"me akeyi??
mummy ta tambaya tana gyara ma Badar skirt dinta,
"birthday din Amal diyar Anty Laura, Husna ta bata amsa,
gyada kai mummy tayi tace "too jira Badar ta shirya ku tafi tare,
hanyar bayi husna ta nufa tace "bata San me muke fadi ba sai ki fada mata dan gaskiya ina shiryawa zan tafi,
Badar da ke saurarensu da kunne daya tace
"kifi ruwa gudu,
ke kika damu da local partys,
duk inda kika ji sha'ani jiki na rawa kin tafi,
'anyways baki yar a kasa ba,
maida earpiece dinta tayi ba tare da ta kalli mummy ba ta cigaba da danne dannen waya,
Husna kuwa bayi ta shige cike da bacin ran irin rainin da Badar ke ma mummy,
abin da ke kara bata ranta bai wuce yadda mummyn ko a jikinta ba,
duk rainin da badar ke mata sai dai tace "yarinta ke damun ta,
ita kuwa komin kankantar abu in tayi mummy ta dinga masifa kenan kamar zata ari baki,
watsa ruwa tayi cike da takaici da tunani iri iri....