← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 113

Sashe 110

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Furucin wata tsohuwa ne doki kunnen Mummy dake zaune tana kuka tana jiran azo daukar gawar Goggo,

Wani sabon kukan ne yazo mata tanata adduar nemawa mahaifiyarta sassaucin ubangiji,

*(Allah ghafuru raheem*)....

Mutuwar Goggo ta taba makusantanta,
domin ko babu komai rai daraja gareshi duk ko irin bakin halin wannan ran..

A ranar da akayi sadakar uku Baffa yasa aka kwashe kayan Goggo aka kaiwa tsofaffin mabaratan bakin titi,
kayan kudinta ne kadai ya bawa Goggo domin itace magajiyarta shi kuwa a bangarenshi yace baya bukatar komai nata domin ta fita a sahun matarshi kafin rai yayi halinsa...

***********

Har gurin mota Daddy ya raka su Anty Saude domin hirar da ta jashi da shi ba wacce zasu katseta bace,
Cike da damuwa  ita ta katse hirar bayan ta ajiye jakarta a bayan mota,

"Ya jikin Musaddiq?
Hope da sauki,
Hafeez ke faďa mana jiya ashe bai ji dadi ba kwana biyu,

Cike da basarwa Daddy yace "Alhamdulillah, jiki kam da sauki sosai,
dan har ya fita ma yau..

"To mashaa Allah Anty Saude tace cike da farin ciki,
jikanka dai yana neman haddasa min fitina, daga yaga zamu fita zai fara kuka saidai a barshi a gida,
yanzu dai na barsu da Taheer zasu zo zuwa anjima suyi muku gaisuwa sai yayi dabara ya barshi can gurin Nadeeyah,

"Murmushin dattaku Daddy yayi wanda ya tuno mata da samartakarshi yace
"Babu komai,
nasan rashin sabo ne,
wata rana ba zaiso ya bar gidana ba,

"In shaa Allah Anty Saude ta faďi tana dariya,
motar ta shiga tana faďin
"Kyan alkawari dai Kyari, ina nan ina jiranka,,

Baki da matsala, in shaa Allahu gobe zanzo ai ni na faďa.. ya faďi cike da jaddadawa...

"To saika zo bari mu wuce Allah ya kara hakuri,

Ameen Daddy ya faďi haďe da rufe kofar motar...

A tare motar su shigo cikin katafaren gidan,
sai da kowacce tayi parking a mazauninta sannan suka fito rike da kaya niki niki..

Cike da ladabi Kamal ya gaisheta bayan ta sakko daga cikin motar,

Amsawa tayi hannunta nakan kayan tace
"Har kun dawo?
Allah yasa dai bakuyi shirme a list dinnan ba,

Girgiza kai Taheer yayi cike da gajiya yace
"komai muyi momma,
muje ciki ki gani,
My dear kawo ledar nan ya karashe yana duban Junior dake rike da leda yana ja,

"Noo Daddy,
muje kaima naka akwai nauyi,

daya daga cikin mai musu aiki ne ya karaso ya karbi dukkan kayan harda na hannun junior,

sai a lokacin suka saki ajiyar zuciya suka wuce ciki ko wanne na dauke da gajiyar kasuwa data zaban kaya..

Buďe kayayyakin Shareefah takeyi tana duban Anty Saude dake cire warwarayen hannunta tana kallon kanta a mudubi,

"Kaya Machaa Allah Saude, yanzu abu kadan ya rage a gama, sai kuma su *plaķiù'oòl..*

Nasa Raahilar masu gari ta siyo ta taho dasu,
naso ayi bikin nan a can Agadez saboda a nuna su ga dangi kuma ayi biki kashi biyu,
na Yareemah mai jiran gado da kuma daurin auren tunda abun duk phàmèè ne,
to Taheer ya hana yace dole ayi shi anan,
amma ki faďa mishi daga an daura zamu wuce can sai ayi biki domin bazai yiwu bikin yazo min a yar karo ba alhali dukkansu nawa ne,
dole a buga tambura agadez ta dauki bikin jinina,
shakikai na wadanda zan bugi kirji ince su din nawa ne... 

Warwaron karshe Anty Saude ta zare ta dawo kusa da Shareefah,

"Karki damu yar uwa,
yin bikin a nan ya zama dole, bayan an daura sai kiyi yadda kike so babu wanda zai hana, kwana nawa ya rage,
kedai kisa a fara shirye shirye a can kafin isowarmu..

Wannan ba matsala bane,
biki kam za'ayi shi wanda ba'a taba yin irinshi ba a tarihi.. Shareefah ta faďi zuciyarta cike fal da murna...

**********

Tsakurar indomien dake gabanta takeyi a hankali tana kaita baki,
tunanin abubuwa da dama sun cika zuciyarta,
ga tausayin halin da Musaddiq yake ciki ga kuma tausayin Taheer  wanda ya sallamar da dukkan hope dinshi a kanta,
tsaki tayi a hankali ta ture indomien gefe dan dama cinta takeyi badan daďi ba sai dan yunwar dake neman yi mata illah...

"Nadeeyah in kin gama Daddy yace kizo..

kafin ta juyo ta ba Husnah amsa har ta bacewa ganinta,
ruwa kaďan ta kurba ta gyara gyalen dake daure a kanta ta nufi parlon kamar wacce kwai ya fashewa a ciki...

Cikin dariyar karfin hali Daddy yace

"Amarya taho nan ki zauna mana,

Cike da karyewar zuciya ta tsuguna can nesa dashi tace

"Ina kwana Daddy,

" Lafiya kalau Nadeeyah,
ke kuma haka akeyi,
kullum ina son muyi magana sai kiyi bacci baki jirana in dawo,
baki kyauta min ba,
gashi yau saura kwana huďu kadai ki tafi,
yanzu dai kije ki shirya kizo muje ki zabi abinda kike so..

Hawayen dake kwance cikin fararen idonta ne suka sauko kan kumatunta,

"Daddy bana bukatar komai ta faďi cikin rawar murya..

Cike da zolaya yace
"Nasani Nadeeyah,
amma ai a matsayina na uba duk da ban kai matsayin kuďin su Taheer ba ai bana kai ki haka ba, sai a goranta mana,
tashi maza ki shirya..

"Sautin kukanta ne ya fara karaďe cikin falon wanda ya dauki hankalin Hilal dake saukowa kasa..

"A'a Kuka kuma Nadeeyah,
ki daina kuka dan Allah kar ki karya min zuciya,
wasa nake miki,
tashi kije ciki zamuje da Reemah..

"Dan Allah Daddy kuyi hakuri, wallahi na rasa yadda zanyi,
ina cikin tsaka mai wuya.....
ta karashe cikin tsananin kuka..

Tasowa Daddy yayi ya isa gareta, a hankali ya dagota ya shiga share mata hawaye,

"Allah shi zai fidda ki,
nasani baki da laifi dan baki isa ki ketare kaddararki ba,
duk abinda Allah ya rubuta akanki babu wanda ya isa ya gogeshi,

Musaddiq ko baki aureshi ba yana nan dai a matsayin jininki babu wanda ya isa ya raba,
rabuwa da Taheer kuma samm babu adalci domin bazan fifita son ďana akan na wani ba,
shima ďa ne,
kuma yana da zuciya a kirjinshi,
ki kwantar da hankalinki ki barwa Allah lamuranki shi ne mai saukakawa...

Ajiyar zuciya tayi mai karfi zatayi magana muryar Junior ya katseta..

A tare suka waigo suka kalleshi Daddy ya saki murmushi haďe da cewa
"Aboki, kaine a gidan da safe?
Ina Daddynka?

Jin ya ambaci sunan Daddy yasa shi waigawa dan tare suka tako har kofar parlon,

"Daddy,
Daddy..
ya fara kwala kiran sunan Taheer wanda ya riga yayi nisa,
"Dama kawoshi yayi ya zauna a gidan dan ya saba dasu,
sai kuma abinda kunnuwanshi suka jiye mishi abin da ya sanyashi cikin tsananin tausayi da kuma sake ganin girma da kimar Daddy..

Kuka sosai Junior ya farayi dan ya fito baiga motar Taheer ba,

Hilal da ya gama sauraron su Daddy shi ya fito wajen yana lallabashi haďe da yi mishi alkawarin maidashi in yayi wanka,
da kyar ya yarda amma har lokacin bai bar kuka ba...

Cike da kuluwa Nadeeyah ta kama hannunshi ta nufi ďaki dashi tayi mishi tsawar da ya sake sanyashi cikin wani gigitaccen kuka,

"Tsanar da kikayi wa ubanshi ce ke neman shafarshi,
Husna ta faďi tana janyoshi jikinta,
ga mamakinta sai ya turata baya ya koma jikin Nadeeyah ya kankameta yana cigaba da kukan,

Kukanshi da kalaman Husnah su suka sake dugunzuma zuciyarta, nan take ta turashi gefe ta faďa bayi tana kuka mai sosa zuciya, tana jiyo ihun kukanshi yana faďin "bazai sake yin kuka ba Dan Allah ta buďe mishi kofa,
duk yadda Husna taso kamashi kasawa tayi haka Anty Reemah da Maleekah,
duk wanda ya tabashi sai ya turasu ya cigaba da ihun sunanta,

Hilal ne kaďai ya iya calming dinshi ya daukeshi suka fita daga dakin,

Sama suka nufa yana rarrashinshi haďe da yi mishi alkawura kala kala...

Gaban mudubin da babu glass suka samu Musaddiq zaune da towel a jikinshi alamun yanzu ya fito wanka..

a kunne Hilal ya raďawa Junior cewa
"Go nd say sorry to ur Twinny, kasan bashi da lafiya,
he will feel better in dai yaji sorry daga bakinka..

Da sauri ya sauka ya isa kusa dashi yace
"Sorry Twinny,
hw is body? Hope u are feeln better?

A hankali ya maida dubanshi gareshi ya tallabo fuskarshi yace "Yes twinny,
hw are u?

"Nt fine, Mamma shoutd at me nd she is crying..
ya faďi kamar zai sake yin wani kukan,, 

Raunanniyar zuciyarshi wacce ake lallabawa ta fara mishi zugi, nan take idanuwanshi saka kawo ruwa,
burinshi bai wuce ace in ya rufe idonshi ya farka ya ganshi a kabari ba,
ya tsani rayuwar gaba ďayanta,

Tunda ya taso a duniyar nan baisan mecece rayuwar duniya ba,
shiyasa ya ke kiran Nadeeyah da rayuwarshi baki ďaya,
itace duniyarshi,
Daddy ya kasa fahimtarshi,
kowa ya zuba ido yana ganin za'a rabashi da rayuwarshi..
hannun Hilal yaji a kafadarshi wanda ya sanya hawayen karasa saukowa kamar an ingizo su,

"Hilal babu wanda zai iya taimaka min a cikinku,
haka zaku zuba ido---
toshe mishi baki Hilal yayi yace

"Bamu isa mu shiga hurumin ubangiji ba Kyari,
ka fahimci hakan,
dan Allah kayi tawakkali,
kaddara babu yadda bata zuwarma bawa,

Rungume junior yayi saboda jin hannunshi yana share mishi hawaye,

"Please Hilal take care of my son bayan raina,
wallahi bazan rayu ba,

Dogon tsaki Hilal yaja haďe da raba junior da jikinshi yace
"Sai ka kashe kanka tunda rayuwarka a hannunka take..

Muje kasa kaji takwara,
ur twinny is crazy ya karashe haďe da jan hannun junior sukayi waje...

Maida kai Musaddiq yayi ya kwanta yana rusa kukan da tunda aka haifeshi bai tunanin ya taba yinshi,
duk yadda yaso yin karfi da zuciyarshi kamar yadda Daddy ya bukata ya kasa saboda zuciyar ta raunana matuka da kaunar Nadeeyah,

Ya Allah Ka sàssauta min,
haka ya dinga faďi yana juyi akan gadonshi....

*******
Alkawari dai Kyari,
gashi har karfe biyar baka ba labarinka,

Yadda take maganar ya sanya Shareefah kureta da ido domin ta dade bata ga yar uwarta cikin wannan yanayin ba,

"Kiyi hakuri Saudatu,
in shaa Allahu zanzo zuwa anjima,
ina nan sane ban manta ba,
Daddy ya bata amsa yana mai duban agogon hannunshi domin ganin lokaci...
Chapter 110 · 0% Book details